Ambaliyar Accra ta 2022
A ranar Lahadi 5 ga watan Yuni, shekarar 2022, an mamaye wasu sassa na Accra yayin da ake ruwan sama. [1] Ruwan saman da ya kwashe kusan sa'o'i huɗu ya bar baya da ƙura a yankuna kamar Kaneshie, wanda ya fi ƙamari bayan ruwan sama.
Ambaliyar Accra ta 2022 | ||||
---|---|---|---|---|
ambaliya | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Ghana | |||
Kwanan wata | 5 ga Yuni, 2022 | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | |||
Yankuna na Ghana | Yankin Greater Accra |
Wasu daga cikin yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Kwame Nkrumah Circle, Spintex Road, Tetteh Quarshe, Fiesta Royal da Nsawam Road.[2]
Sakamakon ambaliyar ruwa a birnin Accra, shugaba Akufo-Addo ya umurci hukumomin birnin da majalisun gundumomi (MMDAs) na yankin Greater Accra da su rusa dukkan gine-ginen da ke kan hanyar kogin da ke haddasa ambaliya a cikin birnin.[3]
Duba kuma
gyara sashe- 2015 Ambaliyar Accra
- 2016 Ambaliyar Accra
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Parts of Accra flooded again after downpour". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2022-06-05. Retrieved 2022-07-25.
- ↑ "Parts of Accra flooded again, social media users react". GhanaWeb (in Turanci). 2022-07-05. Archived from the original on 2022-07-25. Retrieved 2022-07-25.
- ↑ "Parts of Accra flooded again after downpour". Citinewsroom - Comprehensive News in Ghana (in Turanci). 2022-06-05. Retrieved 2022-07-25.