Alliance Française de Port Harcourt
Alliance Francaise of Port Harcourt ( Faransanci: l'Alliance Française de Port Harcourt) wata cibiya ce ta Najeriya da ke Fatakwal, Jihar Ribas mai himma wajen horarwa da ilmantar da mutanen da ke zaune a cikin birni ko kewaye cikin harshen Faransanci da al'adun gargajiya. Ta fara aiki a cikin shekarar 1983, kuma ta koyawa ɗalibai fiye 18,000 tun lokacin da aka kafa ta. Gwamnatin Jihar Ribas ta tallafa wa cibiyar, tana da alaƙa da haɗin gwiwar kungiyoyi sama da 800 a fadin duniya.[1][2]
Alliance Française de Port Harcourt | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1983 |
Fage
gyara sasheSaboda ƙaruwar masu yawan shiga cibiyar, inda tayi ƙaura daga ofisoshinta zuwa wurin da ake yanzu akan titin Herbert Macaulay. Wuraren ya ƙunshi ɗakin karatu, azuzuwa tara, gami da huɗu tare da alluna, gidan cin abinci na gida, filin wasa da babban ɗakin taro, wanda ke iya ɗaukar jimillar baƙi sama da 200 alokaci ɗaya. Darekta, mataimakin darekta ɗaya (darektan karatu) sune ke tafiyar da harkokin gudanarwa na cibiyar, tana da kimanin malaman Faransanci ashirin da fiye da ma'aikatan gudanarwa 10.[3]
Duba kuma
gyara sashe- Faransa Alliance
- Old GRA, Port Harcourt
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Rivers govt. restates support for French language". Vanguard. 12 September 2013. Retrieved 26 November 2014.
- ↑ "RSG Trains French Teachers". The Tide. Port Harcourt: Rivers State Newspaper Corporation. 18 September 2013. Retrieved 26 November 2014.
- ↑ "New premises for the Alliance Française of Port Harcourt". Ambafrance-ng.org. 1 February 2014. Archived from the original on 25 April 2016. Retrieved 26 November 2014.