Alimata Salembéré (an haife ta a shekara ta 1942) shugabar fina-finan Burkina ce, ma'aikaciyar gwamnati kuma 'yar siyasa. Ta kasance memba ce ta kafa bikin fim na FESPACO, kuma ta kasance Babban Sakatariya a shekarun 1982 zuwa 1984. Ta kasance ministar al'adu a Burkina Faso daga shekarun 1987 zuwa 1991.

Alimata Saleméré
Rayuwa
Haihuwa Bobo-Dioulasso Department (en) Fassara, 9 Nuwamba, 1942 (82 shekaru)
ƙasa Burkina Faso
Sana'a
Sana'a darakta, ɗan jarida, civil servant (en) Fassara da filmmaker (en) Fassara

An haifi Alimata Salembéré ranar 9 ga watan Nuwamba, 1942, a Bobo-Dioulasso. Bayan ta sami digiri na BA a fannin adabi na zamani da kuma digiri na ƙwararru a fannin shirye-shiryen talabijin, ta fara aiki da gidan rediyon Television du Burkina. [1] Ita ce wacce ta kafa FESPACO a shekarar 1969, kuma shugabar kwamiti na farko. [2]

Daga shekarun 1976 zuwa 1980 Salembéré jami'iyyar yaɗa labarai ce a kungiyar haɗin gwiwar Afirka da Malagasy (OCAM). Daga shekarun 1982 zuwa 1984 ta kasance babbar Sakatariya na FESPACO, kuma daga shekarun 1983 zuwa 1986 ta kasance sakatariyar yaɗa labarai a ofishin jakadancin Burkina Faso a Paris. An naɗa ta babbar sakatariya a ma’aikatar yaɗa labarai daga shekarun 1986 zuwa 1987, sai kuma ministar al’adu daga shekarun 1987 zuwa 1991. Daga shekarun 1992 zuwa 1999 ta kasance Darakta Janar na Hukumar Haɗin Kan Al'adu da Fasaha (ACCT). [1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 FESPACO 2013 : Alimata Salambéré, une pionnière à l’honneur, lefaso.net, 25 February 2013.
  2. Chamseddine Bouzghaia, Le Fespaco, festival vitrine pour le cinéma africain, célèbre ses 50 ans, France 24, 24 February 2019.