Alhaji Umaru Danjuma Katsina wanda aka fi sani da Kasagi Na Halima (An haife shi a watan Afrilu, shekarar 1950 zuwa Octoba, shekarar 2021). Ya kasance Marubuci ne kuma memba ne a Ƙungiyar marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Katsina. An haife shi a Jihar Katsina, Nijeriya. Sunan Mahaifinsa Muhammadu Danjuma, sunan Mahaifiyarsa kuma Hajara Lonso.[1] Marigayi kasagi ya rubuta wasannin kwaikwayo ba iyaka, daga ciki an wallafa guda biyu a matsayin littafi, 'Kulba Na Ɓarna' da kuma 'Ai Ga Irin Ta Nan'.

Marigayi Alhaji Umaru Danjuma ya yi firamare ta 'central elementary' daga shekarar 1960 zuwa 1965.[2]

A shekarar 1965 ya shiga 'provincial Secondary School Katsina' ya gama a shekarar 1972, bayan wani tsaiko da ya samu sakamakon rashin lafiya.

A shekarar 1975 ya je Ingila karatun aikin Sinema da Talabijin. Ya yi Difloma da babbar Difloma a harkar shirya wasan kwaikwayo.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://hausa.legit.ng/news/1441047-abubuwa-x-da-ya-kamata-a-sani-game-da-marubucin-kulba-na-barna-da-ya-rasu/
  2. https://fimmagazine.com/an-gina-kabarin-umaru-kasagi-kwana-biyu-kafin-rasuwar-sa-ya-na-da-shekara-71/