Alexander Dovzhenko
Alexander Petrovich Dovzhenko, wanda kuma aka kira da Oleksandr Petrovych Dovzhenko[1] (Russian: Александр Петрович Довженко,10 Agusta 1894 - Nuwamba 25, 1956), ya kasance marubuci wasanni dan Yukren ta Soviey,[2] furodusan fina-finai kuma mai darekta. Ana hakayo shi a matsayin masu shirya fina-finai mafi muhimmancin na lokacin Soviet, tare da Sergei Eisenstein, Dziga Vertov, da kuma Vsevolod Pudovkin, gami da zama majagaban tsarin Soviet montage theory.
Tarihin rayuwa
gyara sasheAn haifi Oleksandr Dovzhenko a ƙauyen Viunyshche wanda ke karkashin Sosnitsky Uyezd na Gwamnatin Chernihiv na Daular Rasha (yanzu wani ɓangare ne na Sosnytsia a Chernihiv Oblast, Yukren), a cikin yayan Petro Semenovych Dovzhenko da Odarka Yermolayivna Dovzhenko . Kakanninsa na uba sune Chumaks waɗanda suka zauna a Sosnytsia a ƙarni na sha takwas, daga lardin Poltava makwabta. Oleksandr shi ne na bakwai cikin yara goma sha huɗu da aka haifa wa ma'auratan, amma saboda mutuwar 'yan uwansa shi ne mafi girma a lokacin da ya cika goma sha ɗaya. Daga ƙarshe, Oleksandr da 'yar'uwarsa Polina ne kawai, wanda daga baya ya zama likita, suka tsira har zuwa balaga.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Oleksander Dovzhenko at the Encyclopedia of Ukraine
- ↑ Е. Я. Марголит, ДОВЖЕНКО//Great Russian Encyclopedia [1] Archived 2020-07-25 at the Wayback Machine