Alain-Guillaume Bunyoni (an haife shi 23 da watan Afrilu 1972) ɗan siyasan Burundi ne wanda ya kasance Firayim Minista na Burundi daga 23 ga Yuni 2020 zuwa 7 ga Satumba 2022. Kafin haka, daga shekarar 2015 zuwa 2020, ya zama ministan tsaron cikin gida a majalisar ministocin kasar Burundi .

Alain-Guillaume Bunyoni
Prime Minister of Burundi (en) Fassara

23 ga Yuni, 2020 - 7 Satumba 2022
Pascal-Firmin Ndimira (en) Fassara - Gervais Ndirakobuca (en) Fassara
Minister of Internal Security (en) Fassara

24 ga Augusta, 2015 - ga Yuni, 2020
Minister of Internal Security (en) Fassara

7 Nuwamba, 2007 - 11 Nuwamba, 2011
babban mai gudanarwa

2005 - 2007
Rayuwa
Haihuwa Commune of Kanyosha (Bujumbura Mairie) (en) Fassara, 23 ga Afirilu, 1972 (51 shekaru)
ƙasa Burundi
Karatu
Makaranta Université du Burundi (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Council for the Defense of Democracy–Forces for the Defense of Democracy (en) Fassara

Tarihi da ilimi gyara sashe

An haifi Bunyoni a ranar 23 ga Afrilu 1972 a cikin gundumar Kanyosha, a lardin Bujumbura Mairie .Ya yi karatu a Jami'ar Burundi .Ya kammala karatunsa kuma ya fito cikin jerin wadanda suka kammala karatu a shekarar 1994, amma bai halarci bikin ba. Maimakon haka, ya shiga fadan da ya barke, bayan kashe shugaba Melchior Ndadaye . Ya kasance memba ne a rundunar sojojin da ke,yaki da Demokradiyya .

Sana'ar siyasa gyara sashe

A shekara ta 2003, Majalisar Tsaron Demokraɗiyya ta ƙasa - Forces for Defence of Democracy kawancen siyasa sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tare da sauran mayaka a yakin basasar Burundi . Daga 2004 zuwa 2005, Bunyoni yayi aiki a matsayin kwatankwacin Sufeto Janar na sabuwar rundunar 'yan sanda. Daga 2005 zuwa 2007, ya rike mukamin shugaban 'yan sandan Burundi.

Daga tsakanin 2007 zuwa 2011, Bunyoni ya rike mukamin ministan tsaron cikin gida, rawar da ya koma tsakanin 2015 zuwa 2020. Daga shekarar 2011 zuwa 2014, an nada Alain-Guillaume Bunyoni shugaban ofishin ministan harkokin jama'a a ofishin shugaban kasa.

A ranar 23 ga Yuni, 2020, Majalisar Dokokin Burundi ta kada kuri'ar amincewa da nadin Alain-Guillaume Bunyoni, da Evariste Ndayishimiye, sabon zababben shugaban kasa, ya yi a matsayin Firayim Minista na 8 na Burundi. Shugaban kasar Burundi ya rantsar da shi a wannan rana.

A watan Afrilun 2023, 'yan sandan Burundi na neman Bunyoni amma, sun yi gargadin kama shi, ya gudu. Ba a san abubuwan da ake zargi ba. A karshe an kama shi a ranar 23 ga Afrilu, ranar haihuwarsa.

Sauran la'akari gyara sashe

Baya ga wannan nauyin da ke sama, Bunyoni ya kasance mai kula da harkokin tsaro daban-daban na kasa da kasa kuma a shekara ta 2007 ya kasance daya daga cikin wakilan Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da samar da zaman lafiya da tsaro. Ya kuma jagoranci kwamitin 'yan sandan gabashin Afirka (OCCPAE) kan Interpol .

Duba kuma gyara sashe

  • Majalisar Burundi
  • Majalisar ministocin Burundi
  • Lardunan Burundi

Manazarta gyara sashe


Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

Political offices
Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}

Template:BurundiPMs