Alƙali Abubakar Salihu Zaria
Abubakar Salihu Zariya wanda aka fi sani da Alƙali Zariya babban Malamin Addinin Musulunci ne, (An haife shi ranar 1 ga watan Janairu shekara ta 1980) a unguwar Tudun Wada cikin birnin Zariya a Jihar Kaduna.[1]
Tarihin Rayuwa
gyara sasheAn haifi Alƙali Abubakar Salihu Zariya a unguwar Tudun Wada cikin birnin Zariya a Jihar Kaduna.
Ya fara karatu a makarantar Isah Abdulkarim Nursery and Primary School, kafin ya samu shaidar digirin sa ta farko a Jami'ar Ahmadu Bello inda ya karanta fannin Addinin Musulunci (Islamic Studies).
Cikin Malaman da ya yi karatu a hannusu, akwai mahaifinsa da Mallam Umar a Tudun Wadan Zariya da Mallam Aminu Adam Nepu, masanin Fikihu da Nahawu, akwai Mallam Mai Bala'i Gyallesu da Mallam Shu'aibu Salihu Zariya.