Ajibola Ponnle (An haife ta a ranar 9 ga Satumba, 1973)[1] ita ce kwamishiniya ta yanzu a Ma’aikatar Kafa, Horo da fansho ta Jihar Legas[2][3] wanda Gwamnan Jihar Legas ya naɗa.[4]

Ajibola Ponnle
Rayuwa
Haihuwa 1973 (50/51 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan Digiri a kimiyya : ikonomi
University of London (en) Fassara Master of Science (en) Fassara : organizational psychology (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifeta a 9 september, 1973. Tana da B.Sc. karatun Tattalin Arziki (Economics) daga Jami'ar Ibadan da kuma M.Sc a Organisational Psychology daga Jami'ar London.[1]

Ta fara aikinta ne a shekarar 1994 tare da kamfanin Arthur Andersen, wanda yanzu akafi sani da (KPMG). Daga baya, ta fara aiki da kamfanin British American Tobacco, a matsayin wanda suka samar da kamfanin, ta bar ƙungiyar a matsayin Ma'aikaciyar Kula da Kudade da Kasuwanci. A shekarar 2004 ta yanke shawarar tsunduma kanta a kasuwanci kamfanonin gine-gine wadanda suka hada da TeamBuilding Africa Consultancy, wakiliyar yanki na Team BuiUSA. Ta kuma ziyarci Shirin Executive Management Programme a Makarantar Kasuwanci na Legas.[1][1]

Mrs Ajibola Ponnle ta bayyana wa gwamnatin Legas ta jawo hankalin duniya ta hanyar shirya likitan hakora na farko a duk Afirka ta Yamma.[5][6] A karkashin jagorancin ta ne gwamnatin jihar Legas ta biya Naira biliyan 1.63 ga masu ritaya 321.[7][8][9]

Auren ta ya kare a gaban Mai Shari’a Lateefah Okunnu na Babban Kotun Legas,[10] Igbosere, Legas. bayan sun kashe shekaru 22 da Abiodun Michael Ponnle a matsayin ma'aurata.[11] Suna da yara uku.[10]

Haɗin waje

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 "Mrs. AJIBOLA YEWANDE OLUFUNKE PONNLE —HONOURABLE COMMISSIONER". Ministry of Establishments,Training and Pensions. Retrieved 2020-11-15.
  2. "Lagos Unveils New Head Of Service, Sherifat Folashade Jaji". The Gazelle News. 2015-02-17. Retrieved 2020-11-15.
  3. "Lagos approves payment of 3-yrs arrears pensioners". Vanguard News. 2014-12-10. Retrieved 2020-11-15.
  4. https://metp.lagosstate.gov.ng/2019/08/20/mrs-ajibola-yewande-olufunke-ponnle-honourable-commissioner/
  5. "Lagos to produce first forensic dentist in West Africa". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2020-06-03. Retrieved 2020-11-15.
  6. "Lagos to produce first Forensic Dentist in West Africa — Commissioner -". The Eagle Online. 2020-06-03. Retrieved 2020-11-15.
  7. "Lagos govt. pays N1.63 billion to 321 retirees | Premium Times Nigeria". 2019-12-13. Retrieved 2020-11-15.
  8. "Ajibola Ponnle Archives". The Eagle Online. Retrieved 2020-11-15.
  9. "Lagos pays N1.63b to 321 retirees in December -". The Eagle Online. 2019-12-13. Retrieved 2020-11-15.
  10. 10.0 10.1 "Ajibola Ponnle, Husband in Bitter Divorce Saga, Web of Lies". THISDAYLIVE. 2020-02-23. Retrieved 2020-11-15.
  11. newsbreak (2020-02-08). "Lagos Commissioner, Ajibola Ponnle Files For Divorce From Husband". NewsBreak. Retrieved 2020-11-15.