Ahmed Saleh (an haife shi ranar 14 ga watan Nuwamba 1979) ɗan wasan table tennis ne na Masar. Ya yi takara a gasar Olympics ta bazara a shekarun 2008 da 2012. A wasannin na shekarar 2008 ya halarci gasar ta maza, inda ya sha kashi a zagaye na biyu a hannun Damien Éloi na Faransa. [1] A gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2012 ya fafata a gasar rukunin maza.[2]

Ahmed Saleh
Rayuwa
Haihuwa Giza, 14 Nuwamba, 1979 (44 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a table tennis player (en) Fassara

2019 Wasannin Afirka

Ahmed Saleh ya fafata a gasar cin kofin Afirka na 2019 a cikin men's singles, da na men's doubles, da kuma na mixed doubles.

A Gasar Cin Kofin Men's singles, Saleh ya doke Kurt Lingeveldt da ci 4-1 a zagaye na 16 inda ya tsallake zuwa zagayen Quarterfinals. Daga nan ne Olajide Omotayo wanda ya ci nasara ya kawar da shi a wasan kusa da na karshe, inda aka yi rashin nasara da ci 6-11 a wasa na bakwai.

A Gasar Cin Kofin Men's singles, Tawagar Masar ta Ahmed Saleh & El-Beialy ta zo ta biyu.

A cikin Mixed Doubles, Saleh ya sake haɗa kai tare da wani ɗan ƙasar Masar a Farah Abel-Aziz. Sun samu lambobin azurfa.[3]

WTT Macao 2020

A ranar 29 ga watan Nuwamba, 2020, Saleh ya fafata a gasar gayyata ta wasan commercial table tennis a Macau, kasar Sin da aka fi sani da WTT Macao. Ya shiga gasar ba tare da ya shirya ba kuma a sakamakon haka dole ne ya buga wasan share fage a ranar daya da Wong Chun Ting. Wong ta doke Saleh a wasa mai ban sha'awa (2-3). Domin halartar gasar, an baiwa Saleh kyautar dalar Amurka 15,000.

Manazarta

gyara sashe
  1. Evans, Hilary; Gjerde, Arild; Heijmans, Jeroen; Mallon, Bill; et al. "Ahmed Saleh". Olympics at Sports-Reference.com. Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 26 November 2014.
  2. "Ahmed Saleh" . London2012.com . London Organising Committee of the Olympic and Paralympic Games . Archived from the original on 25 May 2013. Retrieved 1 August 2012.
  3. https://www.ittf.com/tournament/5075/2019/all-africa- games/ https://www.ittf.com/wp-content/ uploads/2020/11/WTT_MAC_DRAW_SHEET_MS-12.pdf