Ahmadiyya a Guinea-Bissau
Ahmadiyya. Al'ummar musulmi ce a kasar Guinea-Bissau a karkashin jagorancin khalifa a birnin Landan. Da farko an kafa ta a kasar a shekarar 1995, a zamanin khalifanci na hudu, Al'ummar tana wakiltar kusan kashi 2% na al'ummar musulmin kasar, wanda ta kai kusan mutane 13,000. [1]
Ahmadiyya a Guinea-Bissau | |
---|---|
Ahmadiyya of an area (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Ahmadiyya da Musulunci a Guinea-Bissau |
Facet of (en) | Guinea-Bissau |
Ƙasa | Guinea-Bissau |
Tarihi
gyara sasheAn kafa kungiyar musulmin Ahmadiyya ta kasar Guinea-Bissau a shekarar 1995. Duk da haka, ba ta sami farkon farawa ba tun lokacin da aka kafa ta. Shekaru shida kacal bayan haka, a ranar 20 ga watan Agusta, 2001, shugaban Guinea-Bissau na lokacin, Kumba Ialá, ya ba da umarnin rufe masallatai da gidajen mishan na Ahmadi, kuma ya yi kira da a kori Ahmadi musulmi mishan na kasashen waje dan asalin Pakistan, su bar kasar. a cikin lokaci na "48 hours". A wata ganawa da ya yi da shugabannin musulmi 500 a kasar, shugaban ya zargi musulmi Ahmadi da tsoma baki a harkokin siyasar kasar da haifar da rashin fahimta da rashin zaman lafiya a tsakanin al'ummar musulmi. Dangane da matakin, Sory Djalo ya yi murabus daga mukaminsa na mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin addini. [2] [3] [4] [5]
A martanin da shugaban ya yanke, al'ummar sun daukaka kara a kotun yankin Bissau, daya daga cikin kotunan yanki tara na kasar. Kotun ta gano cewa matakin da shugaban kasar ya dauka na saba wa kundin tsarin mulkin kasar da ya ba da yancin addini da ya haramta rusa kungiyoyin addini ba tare da izinin kotu ba. Sakamakon haka, an bayyana hukuncin a matsayin mara amfani kuma ya saba wa kundin tsarin mulki. Duk da wannan, har yanzu an dakatar da Al'ummar.
A watan Janairun 2005 ne aka ba wa al’ummar Musulmin Ahmadiyya izinin ci gaba da gudanar da ayyukansu na addini, amma sai aka sake dakatar da su bayan wata biyu, a watan Maris. Dalilin da ya sa aka danganta wannan hukunci shi ne rikicin da ya barke a garin Gabú tsakanin Ahmadiyyawa da wadanda ba musulmi ba wanda ya yi sanadin raunata wasu Musulman Ahmadi hudu. Shekara guda bayan haka, a shekara ta 2006, Al’ummar ta sake ɗaukaka ƙarar matakin da gwamnati ta ɗauka na hana ayyukanta na addini. Har ila yau, gwamnati ta ba wa Al'umma 'yancin gudanar da addininsu a fili. Tun daga shekara ta 2006, ba a sami rahotannin nuna wariya ga Musulman Ahmadi ba, na gwamnati ko kuma na daban. [6] [7]
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "The World's Muslims: Unity and Diversity" (PDF). Pew Forum on Religious & Public life. August 9, 2012. Archived from the original (PDF) on 2012-10-24. Retrieved December 31, 2015.Empty citation (help)
- ↑ "Guinea-Bissau: Attack on the independence of the judiciary". Amnesty International. Empty citation (help)
- ↑ "Guinea-Bissau: Government expels Ahmadiyya Islamic group". IRIN News. August 21, 2015. Retrieved December 31, 2015."Guinea-Bissau: Government expels Ahmadiyya Islamic group" . IRIN News. August 21, 2015. Retrieved December 31, 2015.
- ↑ "Guinea-Bissau in 2001" . Encyclopædia Britannica .Empty citation (help)
- ↑ "Guinea-Bissau" . Freedom House. Retrieved December 31, 2015.Empty citation (help)
- ↑ "RELATÓRIO INTERNACIONAL DE 2006 RELATIVO À LIBERDADE RELIGIOSA" (PDF) (in French). U.S. Department of State. Retrieved December 31, 2015.Empty citation (help)
- ↑ "Institute on Religion and Public Policy Report: Religious Freedom in Guinea- Bissau" (PDF). United Nations Human Rights Office of the High Commissioner.Empty citation (help)