Agbassa sunan ɗayan masarautun Urhobo guda biyu ne a Warri, jihar Delta, Najeriya, ɗayan kuma shine Okere-Urhobo.[1] Sunan 'Agbassa' asalinsa yazo daga Birtaniyya ne daga asalin sunansa AGBARHA, wanda har yanzu ake amfani da shi. Sarki na yanzu shine ; Mai Martaba Sarki, Orhifi, Ememoh II (JP) (Ovie Of Agbarha - Masarauta, Warri ) .[2]

Agbassa

Wuri

Abinda ke ciki gyara sashe

Akwai kusan al'ummomi bakwai waɗanda suka haɗu da masarautar Agbarha Warri (Agbassa):

  1. Otovwodo (Hedikwatar gargajiya)
  2. Igbudu
  3. Edjeba
  4. Ogunu
  5. Okurode (Okurode Urhobo)
  6. Oteghele
  7. Ukpokiti

A cikin Agbassa, ana yin bikin Iyerin kowace shekara, haka kuma ana yin bikin Esemor da Iniemor. Wani biki, wanda aka fi sani da Idju, ana kuma yin shi ne duk bayan shekaru biyu a duk cikin al'ummomin Agbassa, da Okere-Urhobo. Ana kiran wannan bikin da suna Agbassa Juju, kuma tana tsakiyar bautar Owurhie, wani allahntakar mutanen Warri.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. Akenzua, Nosa (2021-04-03). "Delta : Agbarha Warri set to celebrate 'Agbassa Juju Festival'". Platinum Post News. Retrieved 2022-01-18.
  2. 2.0 2.1 "Akenzua, Nosa (2021-04-03). "Delta : Agbarha Warri set to celebrate 'Agbassa Juju Festival'". Platinum Post News. Retrieved 2022-01-18.