Afia Asantewaa Asare-Kyei
Afia Asantewaa Asare-Kyei lauya ce ta kare haƙƙin ɗan adam kuma memba ce ta Kwamitin Kulawa da Meta. Tana aiki a matsayin manajan shirin na Open Society Initiative for West Africa (OSIWA).[1] Yankunan kwarewarta sun haɗa da haƙƙin ɗan adam, haƙƙin mata, shari'ar aikata laifuka, samun dama ga bayanai da batutuwan 'yancin kafofin watsa labarai a Nahiyar Afirka.[2] Ita 'yar asalin Ghana ce da Afirka ta Kudu.[3]
Afia Asantewaa Asare-Kyei | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | Lauya |
Ta yi karatun shari'a a Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam a Jami'ar Pretoria a Afirka ta Kudu . [4] Kafin ta shiga OSIWA, a baya ta yi aiki don Save the Children da USAID.[5] A watan Maris na 2020, ta kasance ɗaya daga cikin 'yan Afirka uku da aka nada su zauna a Kwamitin Kula da Facebook.[6] A watan Yulin 2023, biyo bayan shawarar da kwamitin kula ya bayar don kawar da shugaban kasar Kambodiya Hun Sen, gwamnatin Kambodiya ta lissafa Asare-Kyei a matsayin daya daga cikin mutane 22 da ke da alaƙa da Meta waɗanda aka dakatar da su shiga kasar.[7]
Bayanan da aka ambata
gyara sashe- ↑ Rahman, Khaleda (4 May 2021). "Donald Trump's Facebook Future Will Be Decided by These People". Newsweek (in Turanci).
- ↑ "Ghanaian Joins Board Members For New Global Independent 'Oversight Board' For Facebook And Instagram Content". Modern Ghana.
- ↑ Culliford, Elizabeth (6 May 2020). "Factbox: Who are the first members of Facebook's oversight board?". Reuters (in Turanci). Retrieved 10 February 2023.
- ↑ "Ghanaian Afia Asantewaa Asare-Kyei appointed to Facebook and Instagram Content 'Oversight Board'". Graphic Online (in Turanci).
- ↑ Ashiadey, Bernard Yaw (7 May 2020). "Meet Afia Asantewaa Asare-Kyei, a Ghanaian, who sits on Facebook's new Oversight Board". The Business & Financial Times.
- ↑ "Ghanaian Afia Asantewaa Asare-Kyei on Facebook board to decide Trump's fate". GhanaWeb (in Turanci). 25 February 2021.
- ↑ "Cambodia bans 22 members of the Board of Directors of Meta Platforms. Inc from entering country - Khmer Times". July 4, 2023.