Abu Muslim al-Khurasani
Abu Mūslīm Abd ar-Rāhman ibn Mūslim al-Khūrasani (Larabci: أبُو مُسلِم عَبدُ الرَّحمَن بنُ مُسلِم الخُرَاسَانِي; Farisawa: ابومسلم عبدالرحمان بن مسلم خراسانی) (718 - 754) shi ne shugaban Farisa wanda ya jagoranci juyin juya halin Abbasiyya wanda ya kifar da daular Umayyawa, wanda ya kai ga kafa daular Abbasiyyawa. Mutum ne mai kishi kuma an bayyana shi a matsayin ginshiƙin daular a farkon shekarunta, Har ila yau, wani lokaci ana bayyana shi a matsayin ainihin wanda ya assasa daular Abbasiyawa.[1]
Abu Muslim al-Khurasani Sahib ad-Da'wa | |
---|---|
Haihuwa |
Behzadan, ko Ibrahim 100 AH/ 718 AD Isfahan, Daular Umayyawa |
Mutuwa |
24 Sha'aban 137 AH/ 15 Fabrairu 754 AD Iraƙi, Daular Abbasiyyah |
Sababin mutuwa | Kisan kai |
Burial place | Kogin Tigris, Iraƙi |
Aiki | Sarki, mai juyi, jagora |
Organization | Motsin Abbasiyya |
Shahara akan | Jagorancin juyin juya halin Abbasiyawa |
Office | Sarkin Khurasan |
Karaga | 750 – 754 |
Magaji | Khaled al-Dhahli |
Uwar gida(s) | Bint Imran at-Ta'i |