Abu Bakar Abdul Jamal
Abu Bakar bin Abdul Jamal shi ne Cif na goma 10 kuma Admiral na farko na taurari huɗu na Royal Malaysian Navy (RMN). [1]
Abu Bakar Abdul Jamal | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Johor (en) , 13 Nuwamba, 1946 (78 shekaru) |
ƙasa | Maleziya |
Karatu | |
Makaranta | Naval Postgraduate School (en) |
Sana'a | |
Kyaututtuka | |
Digiri | admiral (en) |
Abu Bakar ya yi aiki kusan shekaru 40 a cikin RMN kuma ya rike mukamai daban-daban. Ya kasance kwamandan jami'in jiragen ruwa da yawa na RMN ciki har da jirgin sintiri, masu hallaka (makami mai linzami) da corvettes. Tsakanin shekara ta 1981 da kuma shekara ta 1984, bu Bakar ya zama babban jami'in kungiyar Corvette Project Team a Kiel, Jamus. Daga baya ya rike mukamin Mataimakin Shugaban Sojan Ruwa (Human Resource) da Mataimakin Babban Jami'in Ruwa a shekara ta 1996. Admiral Abu Bakar ya zama Shugaban Sojan Ruwa a ranar 15 ga watan Oktoba a shekara fa 1998 kuma an ɗaukaka shi zuwa matsayin admiral a ranar 1 ga watan Yuni shekara ta alif dubu biyu 2000. Ya yi ritaya a shekara ta alif dubu biyu da biyu dai dai 2002.
Baya ga kyaututtuka da lambobin yabo daban-daban na Kasar Malaysia, da ya samu Abu Bakar ya kuma sami lambar yabo ta Bintang Jalasena Utama daga Kasar Indonesia da Legion of Merit (digiri na kwamandan) daga Kasar Amurka.
Rayuwa ta farko
gyara sasheAn haife shi a ranar 13 ga watan Nuwamba shekara ta 1946 a Johor, Malaysia kuma yayi karatu an farko a Kwalejin Soja ta Royal a Sungai Besi, Kuala Lumpur . Abu Bakar ya shiga aikin sojan ruwa a shekarar 1965 kuma ya fara horo a matsayin ɗan wasa a Kwalejin Sojan Ruwa ta Kasar Britannia da kasar Ingila. Abu Bakar ya sami horo a fannin Injiniyan makamai a makarantar HMS Excellent School of Weapons Engineering, a Kasar Ingila. An kuma horar da shi a fannin Fasahar Horarwa ta Royal Australian Navy . Abu Bakar ya kuma kammala karatu a Kwalejin Naval ta Royal, Greenwich, United Kingdom da kuma Makarantar Naval Postgraduate, Monterey, California, inda ya yi karatun Gudanar da Tsaro. Ya ci gaba da yin rajista a cikin shirin zumunci a Kwalejin Wolfson, Cambridge kuma daga baya ya yi karatu a Kwaleji ta Royal ta Nazarin Tsaro, a kasar Ingila.
Iyali
gyara sasheAbu Bakar ya auri Kamariyah binti Buang kuma suna da 'ya'ya uku. [ana buƙatar hujja][<span title="This claim needs references to reliable sources. (November 2019)">citation needed</span>]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Abu Bakar bin Abdul Jamal, Memoir Seorang Laksamana, published by the Ministry of Defence, Malaysia (library.mod.gov.my/AccessionFullDisplayRetriever.jsp?H0008295)