Abu Abdallah Mohammed II, Al-Mutawakkil,sau da yawa kawai Abdallah Mohammed (ya mutune a ranar 4 ga watan Agustan shekarar 1578) kuma ya kasance Sarkin Maroko daga shekarar 1574 zuwa shekara ta 1576. Shi ne babban ɗan Abdallah al-Ghalib kuma ya zama Sarkin Musulmi bayan mutuwar mahaifinsa.[ana buƙatar hujja]

Abu Abdallah Mohammed II Saadi
sultan of Morocco (en) Fassara

1574 (Gregorian) - 1576 (Gregorian)
Abdallah al-Ghalib (en) Fassara - Abu Marwan Abd al-Malik I Saadi (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 16 century
ƙasa Moroko
Harshen uwa Larabci
Mutuwa Ksar el-Kebir (en) Fassara, 4 ga Augusta, 1578
Ƴan uwa
Mahaifi Abdallah al-Ghalib
Yara
Yare Saadi dynasty (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a sultan (en) Fassara
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Nan da nan bayan ya hau kan gadon sarauta,ya sa aka ƙashe wani ɗan'uwansa kuma aka tsare wani (Mulay en-Naser, gwamnan Tadla).

Kawun Abu Abdallah, Abd al-Malik, wanda,kamar Abdallah al-Ghalib, dan Mohammed ash-Sheikh ne,ya riga ya gudu zuwa Constantinople a daular Usmaniyya a shekarar 1574.[1] Bayan dawowar Ottoman Algeria,Abd al-Malik yayi nasarar shirya rundunarsa, wacce ta kunshi sojojin Ottoman, kuma a shekarar 1576 ya kutsa cikin Maroko ya cinye Fez daga ɗan ɗan'uwansa, a Kame Fez . Yakin farko ya kasance a al-Rukn a cikin ƙasashen Banu waritin, kusa da Fez. A yakin na biyu kusa da Salé (Rabat) a Jandaq al-Rayhan, Abd al-Malik shi ma ya kayar da ɗan ɗan'uwansa. Yaƙi na uku, wanda shi ma Abd al-Malik ya ci nasara, ya gudana a Taroudannt.

Dukansu Abd al-Malik da Abu Abdallah sun mutu bayan shekaru biyu a Yaƙin Alcácer Quibir, a cikin shekarar 1578.A wannan yakin, Abu Abdallah ya yi yakinsa na ƙarshe da kawunsa Abd al-Malik tare da taimakon abokansa na Portugal .

Duba kuma gyara sashe

Manazarta gyara sashe

Magabata
{{{before}}}
{{{title}}} Magaji
{{{after}}}