Abia, Jihar Enugu

Ƙaramar hukuma da gari a Jihar Enugu, Nijeriya

Abia gari ne, da ke a jihar Enugu, a ƙasar Najeriya.[1]

Abia, Jihar Enugu
Bayanai
Iri administrative territorial entity (en) Fassara
Ƙasa Najeriya da Jihar Enugu

Tarihi gyara sashe

Abia gari ne da ke a kudancin ƙaramar hukumar Udi a jihar Enugu a Najeriya.[1][2] Abia tana cikin dangin Umu-Neke, sauran garuruwan da suka haɗa da Udi, Amokwe, Agbudu, Obinagu, Umuabi, Umuaga, da Nachi. [2]

Tsarin aure gyara sashe

Gabaɗaya ɗaurin auren a Abia iri ɗaya ne da sauran al’ummar Igbo da ke Gabashin Najeriya. Ana ɗaura auren ne tare da yarda da halartar manyan dangi da aka sani da Umunna. Bikin auren na gargajiya ya ƙunshi matakai da dama inda na farko shi ne Iku-aka (buga kofa) zuwa mataki na karshe da aka fi sani da Igba nkwu (Auren Gargajiya). A al'adance masoyan kan zama ma'aurata da zaran an kammalan bikin karshe.[3][4]

Geography gyara sashe

Abia na a dai-dai Latitude: 6° 19' 48" N Longitude: 7° 24' 28" E.[5] Lambar gidan waya ita ce 401104.[6]

Yankunan da ke kusa gyara sashe

Abia ta yi iyakoki, a Arewa ta Obioma, a Kudu ta yi iyaka da Udi, a Gabas ta yi iyaka da Ozalla da Akegbe Ugwu, a yamma kuma tana iyaka da Amokwe.[2]

Yanayi gyara sashe

Kamar yadda yake a mafi yawan sassan Gabashin Najeriya, Abia na da yanayi na wurare masu zafi tare da yanayi daban-daban: lokacin damina da rani wanda ke da bambancin yanayin zafi a cikin shekara.[7]

Cibiyar gargajiya gyara sashe

Akwai tsarin mulki guda biyu a yankin Abia. Na farko ya samu wakilcin basaraken gargajiya, Mai Martaba Sarki, Igwe na al’umma da majalisar ministocinsa mai mulki wanda ya ƙunshi wakilan dukkanin sassan hukumomin ƙauyen da masu ba da shawara.[8] Tsarin na biyu shi ne ƙungiyar gama gari da zaɓaɓɓen shugaba - wanda ake kira The President General da membobin zartarwarsa.[9][10]

Addini gyara sashe

Mutanen Abia galibi Kiristoci ne. Akwai majami'u da yawa a Abia da suka haɗa da; St. Luke's Anglican Church, St. Mark's Catholic Church, Grace of God Mission Incorporated, Assemblies of God, Methodist Church, Winners Chapel, Holy Ghost Church, Deeper Life Bible Church, Church of Advent, da kuma All Saints Church.[1]

Tattalin Arziki da ababen more rayuwa gyara sashe

A zamanin mulkin mallaka, mutanen Abia galibi manoma ne, amman a yau yawancin al'ummar Abia ma’aikatan gwamnati ne ko ƴan kasuwa. Garin yana da wadataccen ruwan sha da wutar lantarki da kuma hanyoyin da suka haɗe da sauran yankunan da ke makwabtaka da garin.[9][10]

Ilimi gyara sashe

Akwai makarantun firamare guda biyu a Abia sai kuma sakandare guda ɗaya mallakin Abia da Udi.[1]

Fitattun mutane gyara sashe

  • HRM Igwe Apostle KS Chime[11]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 "Abia Town Udi – LGA of Enugu Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2022-06-22.
  2. 2.0 2.1 2.2 "Abia · 401104, Nigeria". Abia · 401104, Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-06-22.
  3. "Our Marriage System – Abia Town Udi" (in Turanci). Archived from the original on 2022-06-22. Retrieved 2022-06-22.
  4. Widjaja, Michael. "Igbo Family Ceremonies and Traditions". igboguide.org (in Turanci). Retrieved 2022-06-22.
  5. "Mindat.org". www.mindat.org. Retrieved 2022-06-22.
  6. "Udi ment L.G.A Zip Codes" (in Turanci). 2017-09-22. Retrieved 2022-06-22.
  7. "Nigeria climate: average weather, temperature, precipitation, when to go". www.climatestotravel.com. Retrieved 2022-06-22.
  8. "Ministry of Chieftaincy Matters Enugu Abia". Ministry of Chieftaincy Matters Enugu Abia (in Turanci). Archived from the original on 2023-04-24. Retrieved 2022-06-22.
  9. 9.0 9.1 Ogbu, Sunday (2022-03-10). "Abia Community Cries Out Over Abandoned Road" (in Turanci). Retrieved 2022-06-22.
  10. 10.0 10.1 "Abandoned road: Abia community seeks contractors' return to site". Punch Newspapers (in Turanci). 2017-09-28. Retrieved 2022-06-22.
  11. "Buhari greets Igwe Kingsley Chime on 80th birthday | Encomium Magazine" (in Turanci). Retrieved 2022-06-22.