Abdulrahman bin Abdulaziz Al Kelya

Abdulrahman bin Abdulaziz Al Kelya Babban alƙali ne a bangaren shari'a a kasar Saudi Arabia . Shi ne Babban Alkalin Kotun Koli na kasar Saudi Arabia na farko, ofishin da ya rike daga alif dubu biyu da tare 2009 zuwa shekara ta alif dubu da sha ukku 2013.

Abdulrahman bin Abdulaziz Al Kelya
President of the Supreme Court of Saudi Arabia (en) Fassara

28 ga Faburairu, 2009 - 15 ga Janairu, 2013 - Ghaihab bin Mohammed Al-Ghaihab (en) Fassara
Rayuwa
ƙasa Saudi Arebiya
Harshen uwa Larabci
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a mai shari'a
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Al Kelya ya yi aiki a matsayin babban alƙali a kotuna daban-daban a kasar Saudiyya na tsawon shekaru 40, kuma matsayin Babban Alƙali a Kotun Kashewa a kasar Makka. A shekara ta alif dubu daya da tare 2009, an bayyana shi a cikin wata kasida a cikin Arab News a matsayin "ɗaya daga cikin ƙwararrun mutane a fagen dokar kasar Saudiyya".

A watan Fabrairun shekara ta alif dubu biyu da tare 2009, an nada Al Kelya a matsayin Babban Alkalin Kotun Koli.[1] Sarki Abdullah ne ya kirkiro Kotun Koli a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen shari'a da ya sanar a shekara ta alif dubu da ba Kwai 2007, kuma Al Kelya shine babban alƙali na farko da aka nada. Naɗin nasa yana ɗaya daga cikin canje-canje da yawa ga tsarin shari'a da aka nufa don ƙirƙirar tsarin kotu wanda ya fi dacewa da ayyukan duniya. A watan Janairun shekara ta alif dubu da sha ukku 2013, Al Kelya ya sauka a matsayin Babban Alkalin. Dokar da ta sanar da canjin, a cewar Arab News, ta ce "an cire shi daga mukamin a kan bukatarsa".

  1. "King Abdullah makes major government appointment". Royal Embassy of Saudi Arabia, Washington D.C. 14 February 2009. Archived from the original on 12 June 2010. Retrieved 19 September 2012.