Abdullahi Bawa Wuse (an haife shi a shekara ta 1963) lauyan Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda aka zaɓe shi a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Neja a shekarar 2019. An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar jiha a karo na farko a watan Maris din shekarar 2019 a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) don wakiltar ƙaramar hukumar Tafa.[1][2][3] An yi watsi da odar majalisar ne domin baiwa ‘yan majalisar damar tsayawa takara a zaben. Wuse ya kasance ɗan takara ɗaya tilo a zaɓen kuma ya zama kakakin majalisar ne ta hanyar kuri’ar da aka kada bayan da Ahmed Mohammed Marafa ya nuna shi ko ya zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar wanda shi ne shugaban majalisar kafin Abdullahi Wuse.[4][5][6]

Abdullahi Wuse
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Nan take magatakardan majalisar Abdullahi Mohammed Kagara ya rantsar da Wuse a matsayin kakakin majalisar inda ya yi alkawarin jagorantar majalisar kamar yadda doka ta tanada.[7] Wuse ya kasance babban lauya kuma kwamishinan shari'a a gwamnatin gwamna Babangida Aliyu a jihar Neja. Wuse ya kasance shugaban ƙaramar hukumar Tafa (wato Ciyaman din Tofa).[8]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Wuse emerges Speaker of Niger Assembly". Punch Newspapers (in Turanci). 11 June 2019. Retrieved 2020-06-13.
  2. "First-time lawmaker Abdullahi Wuse is Niger Assembly Speaker" (in Turanci). 2019-06-11. Retrieved 2020-06-13.
  3. "Hon. Bawa emerges Speaker for Niger State Assembly". peoplesdailyng.com (in Turanci). Retrieved 2020-06-13.
  4. theledgerng.com. "Niger Assembly, Wuse Emerges Speaker" (in Turanci). Archived from the original on 2020-06-13. Retrieved 2020-06-13.
  5. lifestyleuser (2019-06-12). "Bawa Wuse New Speaker 9th Niger Assembly". mediaviews.ng (in Turanci). Archived from the original on 2020-06-13. Retrieved 2020-06-13.
  6. "Niger assembly Speaker agrees to swear in PDP member after violent protest". Pulse Nigeria (in Turanci). 2019-07-20. Retrieved 2020-06-13.
  7. "Niger assembly Speaker agrees to swear in PDP member after violent protest". Pulse Nigeria (in Turanci). 2019-07-20. Retrieved 2020-06-13.
  8. Ajobe, Ahmed Tahir; Minna (2019-06-11). "Niger: Ex-AGF Wuse emerges Assembly speaker". Daily Trust (in Turanci). Archived from the original on 2020-06-13. Retrieved 2020-06-13.