Abdelhamid Aït Boudlal ( Larabci: عبد الحميد آيت بودلال‎  ; an haife shi 16 Afrilu 2006) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Morocco wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin mai tsaron baya na Mohammed VI Football Academy .

Abdulhamid Aït Boudlal
Rayuwa
Haihuwa Marrakesh, 16 ga Afirilu, 2006 (18 shekaru)
ƙasa Moroko
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Muƙami ko ƙwarewa centre-back (en) Fassara
Tsayi 1.9 m

Aikin kulob gyara sashe

A ranar 11 ga Oktoba 2023, jaridar Ingila The Guardian ta nada Aït Boudlal a matsayin ɗayan ƴan wasan da aka haifa a 2006 a duk duniya. [1] [2]

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

An kira Aït Boudlal zuwa tawagar 'yan kasa da shekara 17 ta Morocco don gasar cin kofin kasashen Larabawa ta U-17 na 2022, inda ya taimakawa Morocco zuwa matsayi na biyu, bayan da ta yi rashin nasara da ci 4-2 a bugun fenareti a wasan karshe da Algeria mai masaukin baki. [3] An sake kiran shi a gasar cin kofin Afrika na U-17 na 2023, inda ya zira kwallaye biyu, ciki har da kwallon farko a wasan karshe, yayin da Morocco ta sake zama ta biyu, a wannan karon Senegal . Domin bajintar da ya yi, da suka hada da bajinta a wasan da Maroko ta doke Algeria da ci 3–0 a wasan daf da na kusa da na karshe, an sanya shi cikin tawagar gasar . [4] [5] [6]

A ranar 8 ga Nuwamba 2023, An zaɓi Aït Boudlal don shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA U-17 na 2023 . [7]

Manazarta gyara sashe

  1. Christenson, Marcus; Bloor, Steven; Blight, Garry (11 October 2023). "Next Generation 2023: 60 of the best young talents in world football". theguardian.com. Retrieved 11 October 2023.
  2. "غارديان البريطانية تصنف الموهبة المغربية عبد الحميد ايت بودلال ضمن أفضل 60 موهبة في العالم" [The British Guardian Ranks Moroccan Talent Abdelhamid Ait Boudlal Among The 60 Best Talents In The World]. rue20.com (in Larabci). 12 October 2023. Retrieved 13 October 2023.
  3. "كاس العرب لأقل من 17...المدرب شبيا يوجه الدعوة لـ 23 لاعبا" [Arab Cup for Under 17...Coach Shebia invites 23 players]. sports.lematin.ma (in Larabci). 19 August 2022. Retrieved 13 October 2023.
  4. "عبد الحميد أيت بودلال..مانح الأمان لدفاع الأشبال" [Abdelhamid Ait Boudlal..the security provider for the Cubs’ defence]. almountakhab.com (in Larabci). 11 May 2023. Retrieved 13 October 2023.
  5. "اختيار اللاعب المغربي آيت بودلال ضمن التشكيل المثالي لكأس إفريقيا للناشئين" [Moroccan player Ait Boudlal was selected in the ideal squad for the African Junior Cup]. alyaoum24.com (in Larabci). 21 May 2023. Retrieved 13 October 2023.
  6. "المغربي أيت بودلال ضمن الأفضل لكأس إفريقيا أقل من 17" [Moroccan Ait Boudlal is among the best for the Under-17 African Cup]. sports.lematin.ma (in Larabci). 21 May 2023. Retrieved 13 October 2023.
  7. "FIFA U-17 World Cup Morocco U-17 Squad unveiled". CAF (in Turanci). 2023-08-11. Retrieved 2023-11-08.