Abdi Hassan Muhammed, "Hijaar" ( Somali , Larabci: عبدي حسن محمد حجار‎ ) babban jami'in 'yan sandan Somaliya ne kuma tsohon jami'in Soja. Shi ne kwamishinan 'yan sanda na rundunar 'yan sandan Somaliya a halin yanzu .

Farkon rayuwa da karatu

gyara sashe

An haifi Hijar a yankin Sool a shekarar 1953. Ya kammala karatunsa na firamare a yankin Benaadir, inda ya kammala karatunsa na jami'ar ƙasar Somaliya a shekarar 1975.

Shekarun aiki

gyara sashe

A shekarar 1977, ya shiga aikin soja a ƙasar Somaliya inda ya samu horo na farko a makarantar Janar Daud. Kamfanin dillancin labaran SONNA ya bayar da rahotan cewa, ya samu horon kwamandojin ƙasashen Amurka da Jamus, kuma ya taɓa zama mai horas da sojoji a wata makarantar horas da su. Bayan yaƙin basasar Somaliya, ya zama Daraktan Hukumar Shige da Fice ta Ƙasar Somaliya.

An naɗa Janar Abdi Hassan Mohamed a matsayin ƙaramin jakadan Somaliya a Djibouti a shekarar 1989. Daga shekarar 2007, zuwa 2008, ya kasance babban kwamandan sojojin ƙasar Somaliya, kuma daga shekarar 2008-2019, ya kasance mai kula da sojojin ƙasar Somaliya a ƙasar Saudiyya.

A watan Afrilun 2019, an naɗa shi mataimakin kwamandan sojojin ƙasar Somaliya, kuma a ranar 22 ga watan Agusta, 2019, aka naɗa Janar Abdi Hassan Mohamed a matsayin kwamandan 'yan sandan Somaliya.

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe