Abdelhamid Hergal ma rattaba kalma Harguel,Hargel ko Herguel ( Larabci: عبد الحميد الهرقال ), An haife shi ne a ranar 27 ga watan Janairu shekara ta alif 1959 [1] a Tunis, dan wasan kwallon kafa ne na kasar Tunisia wanda ya taka leda a matsayin dan wasan gaba [2] tare da kungiyar Stade Tunisien, Espérance Sportive de Tunis da kungiyar kwallon kafa ta Tunisia . Shine yafi kowa zira kwallaye a raga a tarihin Stade Tunisien da kwallaye 85.[Ana bukatan hujja] Masanin fasaha ne na gaske kuma mai ban mamaki, wanda aka zaba shi ne mafi kyawun ɗan wasan ƙwallon ƙafa a duk lokacin da ya buga wa Tunisia wasa.