Abba Ibrahim Garko
Abba Ibrahim Garko (An haife shi ranar 1 ga Agusta, 1963), a garin Garko. Ɗan siyasa ne.
Abba Ibrahim Garko | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1963 (60/61 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Nigeria Peoples Party |
Farkon rayuwa
gyara sasheYa yi makarantar firamare ta Garko (1971 – 1978). Sannan ya halarci makarantar sakandaren kasuwanci ta Wudil tsakanin 1978 – 1983. Hon. Ya yi aiki a matsayin Auditor da Gwamnatin Jihar Kano. Ya yi ritaya da radin kansa ya shiga harkokin siyasa a shekarar 2007. [1]
Siyasa
gyara sasheAn zabe shi mataimakin shugaban jam’iyyar All People’s Party (ANPP) 2007 – 2010. Ya kuma rike mukamin Karamar Hukumar Mulki Sole (Takai Local Government). An zabi Honorabul Garko a matsayin dan majalisar jiha sau biyu. A halin yanzu shi ne shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi. [2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://dailytrust.com/amp/3-lg-caretaker-nominees-fail-screening-at-kano-assembly
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-11-09. Retrieved 2021-11-09.