Abayi Okoroato
Abayi Okoroato birni ne a cikin ƙaramar hukumar Obingwa a Jihar Abia,[1][2][3] Najeriya .
Tarihi
gyara sasheAbayi Okoroato yana nan a Obingwa, jihar Abia, shiyyar yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Ƙauyen ya ƙunshi Ƙungiyoyi guda takwas:
- Umu-Uje
- Umu-Onyeike
- Umu-Alioha
- Umu-Imegwu
- Umu-Atali
- Umu-Naocha
- Umu- Diji
- Umu-Nwagbaghioso
Adadin kiyasin mutanen Abayi Okoroato a halin yanzu mazauna 56,426. Al’ummar yankin sun kunshi mutanen yankin Ngwa na kabilar Igbo.
Yaren Ngwa na yaren Igbo dai anfi amfani da shi a yankin yayin da addinin Kiristanci ya zama ruwan dare a yankin. Shahararrun bukukuwan da aka gudanar a karamar hukumar Obingwa sun hada da bikin Sabuwar Doya.
Tattalin Arziki
gyara sasheSaye da sayarwa i wani muhimmin al’amari ne na tattalin arzikin Abayi Okoroato inda ake samun kasuwanni kamar kasuwar Ahia Eke inda ake saye da sayar na dimbin kayayyaki. Har ila yau noma wani muhimmin al’amari ne na harkokin tattalin arziki da al’ummar Abayi Okoroato suka gudanar tare da noma irin su dawa, rogo, koko, da kayan lambu da ake nomawa da yawa a yankin.
Noman dabino na daya daga cikin muhimman hanyoyin samun kudin shiga ga mutanen Abayi Okoroato. Sai dai gonakin dabino na kauye, duk itatuwan dabino na kauye ne, kuma ana sayar da su ga mutanen waje da mutanen gari don samar da kudaden shiga ga kauyen.
Majami'u masu rinjaye
gyara sasheMajami'u masu rinjaye a garin Abayi Okoroato galibinsu cocin Orthodox ne, ciki har da, Seventh-day Adventist Church (SDA). United Evangelical Church (UEC). Cocin Kristi (CoC).
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://nigeriazipcodes.com/4131/list-of-towns-and-villages-in-obioma-ngwa-lga//%7Ctitle=List[permanent dead link] Of Towns and Villages in Obioma Ngwa LGA|newspaper=Nigeria Zip Codes|access-date=2020-10-22}}
- ↑ https://www.medianigeria.com/list-of-towns-and-villages-in-obi-ngwa-abia-state/%7Ctitle=List[permanent dead link] Of Towns and Villages in Obingwa Abia State|newspaper=Median Nigeria|access-date=2020-10-22}}
- ↑ https://nigerianinfopedia.com.ng/abia-state-local-government-areas-towns/%7Ctitle=Abia[permanent dead link] State Local Government Area's Towns|newspaper=Nigerian Infopedia|access-date=2020-10-22}}