A Screaming Man, fim ne na wasan kwaikwayo ne na shekarar 2010 na Mahamat Saleh Haroun,[1] tare da jarumi Youssouf Djaoro da Diouc Koma.[2] An tsara shirin a cikin shekara ta 2006, ya shafi yakin basasa na Chadi, kuma shirin ya ba da labarin wani mutum da ya tura ɗansa yaki domin ya dawo da mukaminsa a wani otel mai girma. Shirin ya nuna darasi tsakanun da' da uba da al'adun yaƙi. An dauki muhimman sassan fim din a wurare kaman N'Djamena da Abéché. Fim ɗin ya sami kyautar lambar yabo ta Jury a shekarar 2010 Cannes Film Festival.[1]

A Screaming Man
Asali
Lokacin bugawa 2010
Asalin suna Un homme qui crie
Asalin harshe Faransanci
Larabci
Ƙasar asali Faransa, Beljik da Cadi
Distribution format (en) Fassara video on demand (en) Fassara
Characteristics
Genre (en) Fassara drama film (en) Fassara
During 92 Dakika
Launi color (en) Fassara
Direction and screenplay
Darekta Mahamat Saleh Haroun (en) Fassara
Marubin wasannin kwaykwayo Mahamat Saleh Haroun (en) Fassara
'yan wasa
Samar
Editan fim Marie-Hélène Dozo (en) Fassara
Other works
Mai rubuta kiɗa Wasis Diop (en) Fassara
Director of photography (en) Fassara Laurent Brunet (en) Fassara
Kintato
Narrative location (en) Fassara Ndjamena
Muhimmin darasi Yaƙin Basasar Chadi (2005–2010)
External links

Adam ( Youssouf Djaoro ), tsohon zakaran wasan ninƙaya na tsakiyar Afirka, ya kasance mai lura da tafki a wani otal na alfarma.[3] Ana kiranshi da Champ. A ma'aunin tattalin arziki Mrs. Wang, manajan otal din, ta rage mashi matsayi zuwa mai gadin ƙofa sannan kuma ɗansa Abdel ya zama mai kula da tafkin. Basaraken yankin ya matsa wa Adam lamba da ya ba da kuɗi don yaƙi da Chadi ke yi da dakarun 'yan tawaye, tare da hukunta shi da rashin halartar wani taro. Sarkin ya gaya wa Adamu yadda ya aika ɗansa ɗan shekara 17 ya yi yaƙi. Ya kuma shaida wa Adamu cewa yana da kwanaki uku ya biya kudi don tallafa wa harkar. Don sake samun mukaminsa Adam sadaukar da dansa Abdel ga Sojojin Chadi (watau Chadian Ground Forces), kuma sojojin sun zo har gida suka dauki Abdel suka tafi dashi a idon jama'a. Adamu ya koma aikinsa a matsayin mai kula da tafkin.

Wata mata ƴar shekara 17, budurwar Abdel mai juna biyu, ta koma gidan Adam kuma anyi maraba da ita ana kula da ita. Rikicin ya munana kwarai kuma mutanen gari sun fara gudu. Adamu ya gaya wa surukarsa ha’incin da yayi sai tayi bakin ciki. Adam ya sake tunanin kan matsayinsa na uba sai ya dauki babur ɗinsa da motar gefe zuwa filin yakin don maido dansa Abdel gida. Ya iske Abdel da munanan raunuka a idanunsa, wuya, hannun dama da kuma cikinsa. A wannan daren Adam ya dauki Abdel daga asibiti, ya saka shi a motar gefen ya nufi gida dashi. Ana cikin tafiya sai Abdel ya ce yana son yin iyo a cikin kogi. Abdel ya mutu yayin da suke isa kogin. Adamu ya sanya gawar a cikin kogin har ruwa ya janye gawar.

Ƴan wasa

gyara sashe

Jaruman shirin sun hada da;[4]

  • Youssouf Djaoro a matsayin Adam
  • Diouc Koma a matsayin Abdel
  • Emile Abossolo M'Bo a matsayin hakimin gundumar
  • Hadjé Fatimé N'Goua a matsayin Mariam
  • Marius Yelolo a matsayin David
  • Djenéba Koné a matsayin Djeneba
  • Heling Li a matsayin Mme Wang
  • John Mbaiedoum a matsayi Etienne
  • Abdou Boukar a matsayi Le maître d'hôtel
  • Gerrard Ganda Mayoumbila a matsayi Le sous-officer
  • Tourgodi Oumar a matsayi Soldat barrage 2
  • Hilaire Ndolassem a matsayi Radion speaker (voice)
  • Remadji Adele Nagaradoum a matsayi Souad
  • Sylvain Nbaikoubou a matsayi Le nouveau cuisiner
  • Fatimé Nguenabaye a matsayi La voisine
  • Mahamat Choukou a matsayi Soldat barrage 1
  • Hadre Dounia a matsayi Joune Soldat blessé
  • Laure Cadiot

Dangantakar Adam da Abdel ita ce babban abin la'akari a labarin shirin, sannan kuma a cewar daraktan ya shafi labarin kasar Chadi a yau: “a tsakanin uba dansa akwai alaka ta jini, kwayoyin halitta, da al’adu. Labarin na da mahimmanci a nan saboda maza suka haifar da rikicin Chadi. An kwashe shekaru 40 ana rikici a ƙasar Chadi, kuma uba ne ya cusa wa dansa ra'ayin yaki, domin idan ba don haka ba, babu dalilin da zai sa dan ya shiga lamarin yakin."[5] Mahamat Saleh Haroun da gangan ya ki yin cikakken bayani game da yakin basasa na Chadi da kuma harkokin siyasa: "Fim ɗin ya ba da labarin ra'ayin wannan uba kuma bai samu matsayi a wajen 'yan tawaye ko kuma a wajen gwamnati ba; babu ruwan kowa da rayuwarsu. don haka ko da ace sun zama 'yan tawaye ko kuma sojojin gwamnati ba zai dakatar da yaƙin ba”. [5]

Taken fim ɗin wani zance ne daga rubutaccen adabi Return to My Native Land na Aimé Césaire.[6] Cikakkun jimlar ita ce "Mutumin da ya yi kururuwa ba mai rawa ba ne".[7] Haroun ya ce babban jigon Adam shine "kururuwar Allah ne kawai, ba kururuwar wahala ba".

Anyi tunanin labarin shirin a cikin shekara ta 2006 a lokacin gudanar da shirin Daratt . A ranar 13 ga watan Afrilu ne dakarun 'yan tawaye suka shiga N'Djamena, babban birnin kasar Chadi, a daidai lokacin da Haroun ke bada umurnin fim, kuma nan da nan aka dakatar da aikin. Taurarin fim ɗin, ciki har da matashin jarumin da yake cika shekara 18 a ranar, sun makale a cikin jeji ba tare da wata hanyar sadarwa ba. Hakan ya sanya Haruna tunanin yadda zai nuna halin zaman cikin tsoro a lokacin da suka makale babu wani taimako.[8]

Kamfanin Pili Films na Faransa da Goï Goï Productions na Chadi ne suka shirya fim ɗin a tare. An bayar da ƙarin tallafin haɗin gwiwa daga kamfanin Belgium Entre Chiens et Loups. An bada taffin Euro miliyan biyu daga Cibiyar Cinematography ta Faransa, da saka hannun jari na farko daga Canal +, Canal Horizons, Ciné Cinéma da TV5Monde.[9]

An yi fim ɗin a cikin makonni shida a wani wuri a Chadi, ya fara daga 30 ga watan Nuwambar shekarar 2009. Da yawa daga cikin 'yan wasan kwaikwayon da suka fito a shirin sun haɗa da ainihin ma'aikatan otal, 'yan yawon b6019418562ude ido da sojoji wadanda Haroun ya bukaci su yi wasan a matsayin kansu domin a gane gaskiya a bayyane. Daraktan ya ba da labarin yin fim a N'Djamena a matsayin wanda ba shi da matsala. Duk da haka, lokacin da ake shirya wannan shiri a Abéché, akwai tsoro matuka a zukatan duk wani dake cikin shirin, an kasance da tsoro a tsakanin duk wanda ke da hannu a cikin samarwa. Haroun ya ga alamaun kalubale kafin kammala shirin kada wani abu ya faru, yayin da ya kuma yi kokarin dakewa da kyakkyawar niyya.[10]

Sakin shiri

gyara sashe

Shirin "A Screaming Man" ya fito a ranar 16 ga watan Mayun 2010 a gasar a bikin Fim na Cannes na 63.[11] Daga baya an nuna shi a wuraren bukukuwa da yawa ciki har da bikin Fina-Finan Duniya na Toronto . Rarraba Pyramide ya fitar da shi a cikin gidan wasan kwaikwayo na Faransa a ranar 29 ga Satumba 2010.[12]

Muhimmanci amsoshi

gyara sashe

Fim ɗin ya sami kyakkyawan sharhi daga masu suka. Rotten Tomatoes mai yin bita ya ba da rahoton cewa kashi 89% cikin 36 na ƙwararrun masu suka sun ba fim ɗin kyakkyawan bita, tare da matsakaicin ƙimar 7.2/10. [13]

Thomas Sotinel ya sake nazarin fim ɗin don Le Monde . Ya yi tunanin cewa tana da kyan da ba za a iya musantawa ba, amma ya ci gaba da cewa, “Wannan kyawun kuma mai rauni ne, domin Mahamat Saleh Haroun ba shi da isasshen albarkatun da za su iya bayyana hangen nesansa. Yana da matuƙar bacin rai cewa jerin ƙaurawar mutanen N'Djamena da kyau ya nuna cewa mai shirya fim zai iya canzawa zuwa babban tsari lokacin da batunsa ya umarce shi."[14]

Julien Welter na L'Express ya yaba da zaɓin da Haroun ya yi na rashin yin nazari mai yawa kan rikicin kasar Chadi, ko kuma wani karin waƙe-waƙe game da wahalhalun da ya janyo. Babban abin da ya fi damun Welter shi ne ya yi tunanin ingancin rubutun ya ragu a lokacin aiki na uku, amma ya ƙare bitar ta hanyar shelanta Haroun a matsayin "fiye da kowane lokaci mai fasaha da za a bi."[15]

Wani mai sukar fina-finan Amurka, Roger Ebert ya bayyana cewa, “ya yabawa fim ɗin matuka, yana mai cewa, “Kyakkyawan ingancin fim din shi ne kallon rayuwar Adam, da yadda yake ɗaukar aikinsa kusan fiye da dansa, da kuma irin matsayin da wani ɗan fim ya ba shi. Western hotel sun yi masa sihiri."[16]

Fim ɗin ya karɓi kyautar Jury na Cannes Film Festival. Hakan ya sanya Haroun ba wai kawai darakta ɗan ƙasar Chadi na farko da ya fara yin fim a babbar gasar ba, har ma ya zama na farko da ya samu kyautar daya a daga cikin bikin lambobin yabo na festival's awards.[17] Wani Mutum mai kururuwa ya lashe kyautar Hugo na Azurfa don mafi kyawun wasan allo a Bikin Fina-Finan Duniya na Chicago na 46 . Youssouf Djaoro ya samu kyautar Silver Hugo a matsayin tauraron jarumi (best actor).[18] A lambar yabo ta Lumière ta shekarar 2011, da 'yan jaridu na kasashen waje da ke birnin Paris suka yanke shawarar, fim din ya lashe kyautar mafi kyawun Fim na Faransanci daga wajen Faransa.[19] An zabi fim ɗin don lambar yabo ta Magritte a cikin nau'in Mafi kyawun Fim ɗin Waje a cikin Haɗin gwiwa a cikin shekarar 2012, amma ya ɓace zuwa Romantics Anonymous.[20]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 "A Screaming Man / Un homme qui crie | African Film Festival, Inc". Retrieved 28 January 2022
  2. "A Screaming Man – review". the Guardian. 14 May 2011. Retrieved 28 January 2022.
  3. Gabara, Rachel (2013-09). "FEATURE FILMS - Mahamat-Saleh Haroun. A Screaming Man. Original title: Un homme qui crie. 2010. Chad and France. French and Chadian Arabic, with English subtitles. 91 min. Film Movement and Pyramide International. $24.95". African Studies Review. 56 (2): 227–228. doi:10.1017/asr.2013.68. ISSN 0002-0206.
  4. Haroun, Mahamat-Saleh (2011-04-13), Un homme qui crie (Drama), Pili Films, Entre Chien et Loup, Goi-Goi Productions, retrieved 2022-01-28
  5. 5.0 5.1 Aftab, Kaleem (2010-07-21). "Visible Africa: Cannes winner Mahamat-Saleh Haroun". The National. Archived from the original on 10 October 2012. Retrieved 2010-08-09.
  6. Lemercier, Fabien (2009-10-23). "Haroun readies to shoot Screaming Man". Cineuropa. Archived from the original on 21 July 2010. Retrieved 2010-04-28.
  7. Collett-White, Mike (2010-05-16). "Father-Son Film in War-Torn Chad Lights up Cannes". af.reuters.com. Thomson Reuters. Archived from the original on 12 May 2011. Retrieved 2011-01-17.
  8. Aftab, Kaleem (21 July 2010). "Visible Africa: Cannes winner Mahamat-Saleh Haroun". The National. Archived from the original on 10 October 2012. Retrieved 9 August 2010.
  9. Lemercier, Fabien (23 October 2009). "Haroun readies to shoot Screaming Man". Cineuropa. Archived from the original on 21 July 2010. Retrieved 28 April 2010.
  10. Cuyer, Clément (29 September 2010). "'Un homme qui crie' : rencontre avec Mahamat Saleh Haroun". AlloCiné (in French). Tiger Global. Archived from the original on 9 March 2011. Retrieved 29 October 2010.
  11. "The screenings guide" (PDF). festival-cannes.com. Cannes Film Festival. Archived from the original (PDF) on 19 January 2012. Retrieved 26 May2010.
  12. "Un Homme qui crie". AlloCiné (in French). Tiger Global. Archived from the original on 21 April 2010. Retrieved 26 May 2010.
  13. A Screaming Man - Rotten Tomatoes
  14. Sotinel, Thomas (29 September 2010). "'Un homme qui crie' : dans le chaos tchadien, la tragédie d'Adam, père déchu en quête de rédemption". Le Monde (in French). Archived from the original on 2 October 2010. Retrieved 29 September2010. Cette beauté est aussi fragile, parce que Mahamat Saleh Haroun n'a pas eu tout à fait les moyens nécessaires à la pleine expression de sa vision. C'est d'autant plus rageant que la séquence de l'exode de la population de N'Djamena montre bien que le cinéaste sait passer au grand format lorsque son propos le commande
  15. Welter, Julien (28 September 2010). "Un homme qui crie". L'Express (in French). Archived from the original on 23 January 2011. Retrieved 29 October2010. Mahamat-Saleh Haroun est plus que jamais un artiste à suivre.
  16. "Ebert, Roger (24 May 2010). "Cannes postmortem. Is that the wrong word?". Chicago Sun-Times. Archived from the original on 27 May 2010. Retrieved 25 May 2010.
  17. Chang, Justin (23 May 2010). "'Uncle Boonmee' wins Palme d'Or". Variety. Archived from the original on 3 December 2012. Retrieved 23 May 2010.
  18. "46th Chicago International Film Festival Award Winners Announced". Archived from the original on 8 July 2011.
  19. Lemercier, Fabien (17 January 2011). "Of Gods and Men crowned Best Film at Lumières". Cineuropa. Retrieved 17 January 2011.
  20. Engelen, Aurore (10 January 2012). "Nominations announced for 2nd Magritte Awards". Cineuropa. Retrieved 12 January 2013.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe
  • A Screaming Man at IMDb