Ƙungiyar Wasan Kwallon Kaffa ta Star Base
Ƙungiyar Kwallon kafa Star Base[1] ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce ta Najeriya da ke Ogudu, Legas, wanda Adeoye Segun Hakeem ya kafa acikin watan Satumba 2014.
Ƙungiyar Wasan Kwallon Kaffa ta Star Base | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi
gyara sasheAn kafa kungiyar kwallon kafa ta Star Base[2] ne a shekarar 2014 lokacin da wanda ya kafa kungiyar kuma shugaban kungiyar, Mista Adeoye Segun Hakeem, ya yanke shawarar hada wasu kwararrun matasa masu hazaka a filin wasan kwallon kafa na barikin 'yan sanda ta Mobile Police Barrack Ori-oke dake Ogudu Legas domin samar da wata tawagar kwararru 'yan wasa
Adeoye ya kan buga wasan kwallon kafa na karshen mako tare da kungiyar ‘all star’ mai suna Alapere Mopol FC a barikin ‘yan sanda na Ori-oke Mobile Police Barrack, Ogudu Legas kuma wasu yaran da suka yi wasa tare da shi a cikin kungiyar tauraro da kuma bayansu sun burge shi.
Dangane da hazakarsu, Adeoye ya yi magana da matasan game da mayar da soyayyarsu ga wasan wani abu da zai iya samar musu da sana’a. Don haka sai ya tara su ya sanya wa kungiyar suna Star Base Football Club, Ogudu.
Star Base suna shiga gasar ƙwallon ƙafa ta Fusion,[3] ƙungiyar FA ta jihar Legas ta amince tawaga yan wasan.
'Yan wasa na yanzu
gyara sasheTun daga Janairu 2022
|
|
Masu horarwa
gyara sasheMatsayi | Suna |
---|---|
Koci | Olu Akinfolarin |
Mataimakin Koci | Sonuyi Saheed |
Masu Gudanarwa
gyara sasheMatsayi | Suna |
---|---|
Shugaban kasa | Adeoye Segun Hakeem |
Mataimakin shugaba | Olanrewaju Lekan Muyideeb |
Sakataren kungiyar | Kalejaiye David |
Manajan kungiyar | Rufai Olalekan Azeez |
Mataimakin manajan kungiyar | Sonuyi Saheed |
Manajan jin dadi | Idris Waheed |
Fitattun 'yan wasa
gyara sashe- Robert Odu
Manazarta
gyara sashe- ↑ "StarBase FC". www.finelib.com. Retrieved 22 May 2020.
- ↑ Okugbe, Jerry (29 August 2021). "Fusion Football Championship: 'We Were The Better Team' - Starbase FC's Ibrahim Agoro Says After Netting Brace In Win Over GSC FC". Latest Sports and Football News in Nigeria | Sports247. Retrieved 26 January 2022.
- ↑ "Bamisebi, Samuel (30 July 2021). "Eguavoen Goal Not Enough To Save Starbase FC From Huge Loss". Latest Sports and Football News in Nigeria | Sports247. Retrieved 26 January 2022.