Mantšebo (a cike: 'Mantšhebo Amelia 'Matšaba; 1902-1964) ta kasance mai mulki Basutoland (Lesotho na yanzu) daga 1941 zuwa 1960, a matsayin mai rikon waryan kujerar ɗanta, Moshoeshoe II na gaba.

'Mantšebo
King of Lesotho (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1902
Mutuwa 1964
Ƴan uwa
Abokiyar zama Seeiso of Basutoland (en) Fassara
Sana'a
Sana'a sarki
Kyaututtuka

'Mantšebo ita ce ta farko daga cikin matan Seeiso uku, wanda suka kasance babban shugaban daga 1939 zuwa 1940. An zabe ta a matsayin sarauniya ta rikon kwarya wata daya bayan mutuwarsa, ta zama mace daya tilo mai mulki a lokacin mulkin mallaka na Lesotho. Shekaru na farko a cikin iko sun kasance da rikice-rikice akan halaccin mulkinta da kuma kula da ɗanta (mai gajiyar Seeiso). Koyaya, 'Mantšebo ta riƙe kujerar sama da shekaru 19, kuma ta kafa ginshikin mulkin sarautan Lesotho na yanzu.

Rayuwa ta farko

gyara sashe

'Sunan Mantšebo a lokacin haihuwa itace Moipone Nkoebe . Ta kasance 'yar Sempe Nkoebe ce, wacce ta kasance shugaba a yankin Quthing kuma "memba mai matsayi na daular masarautat". Bayan kammala karatunta na firamare, 'Mantšebo ta auri Seeiso Griffith, ɗan Griffith Lerotholi (wanda ya gaji ɗan'uwansa Letsie Lerotholi a matsayin babban shugaban Basutoland a 1913). Ta kasance matar ta farko (ko "uwar gida") ga mijinta, kuma ta haifa masa 'ya, Ntšebo (wanda bai cancanci ya gaji kursiyin ba [1]). Seeiso ya sake yin aure sau biyu, kuma tana da ɗa ɗaya da kowannensu daga matansa biyun. Ɗansa da matarsa ta biyu, Bereng (mai zuwa Moshoeshoe II), ya zama magajinsa lokacin da ya hau gadon sarauta a watan Yulin 1939.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. Roper, E. R. (1943). "The Basutoland Regency Case". South African Law Journal. 60: 300–306.