Zumunci wata al'ada ce mai girma a tsakanin mutane wanda kan ƙara haɗa huddar, dangantaka da yarda Mai karfi da juna, zumunci kan ƙara ilimi a tsakanin masu sada shi kuma zumunci abu ne da addinanmu suka umurce mu da mu sada shi saboda falalar shi.[1]

abota
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na interpersonal relationship (en) Fassara
Amfani aboki
Yana haddasa farin ciki
Hannun riga da enmity (en) Fassara
zumunci

Dalilin zumunci

gyara sashe
 
Tafiya zumunci
  1. Domin sada gaisuwa
  2. Domin kara ilimi
  3. Domin farin ciki
  4. Kaucewa bala'i
  5. kara son juna
  6. Domin biyayya ga umarnin Allah.
  7. Domin samun babban rabo a lahira. Da dai sauran su.

lokutan zumunci

gyara sashe
 
sada zumunci lokacin bikin sallah

Akwai lokutan da galibi akan yi zumunci duk da za a iya yin shi a kowane lokaci.

  1. Lokacin bukukuwan sallah
  2. Karshen shekara
  3. Lokacin hutun makaranta
  4. Lokacin bukukuwa ya
  5. Kowane lokaci.

Nau’o’in  Zumunci

gyara sashe

Al’amarin zumunci a al’ummar Hausawa abu ne da za’a ce yana da rassa ko yana yaduwa fiye da kowace kabila ko al’ummar dake makwabtaka da Hausawa.

1.Zumunci na jini (haihuwa ko zuriyya)

gyara sashe

Wannan kan gunshi mutane irin su uwa da uba, yayan tsatso, yan uwa, yan uba, kawu, inna, gwaggo, baffa, yaya, kani da sauransu.

2. Zumunci na aure (auratayya)

gyara sashe

Wannan kan shafi mutane irin su miji da mata, suruki, suruka, agola,dan riko.

3. Zumunci na zamantakewa (ma}wabtaka)
gyara sashe

Wannan kan shafi mutane a wurin makwabtaka na gida, ko kasuwa, ko gona, da sauransu.

4. Zumunci na mu'amulla (sana'a, moriya)
gyara sashe

Wannan kan shafi mutane masu sana'a iri daya ko kuma abokan ciniki, barantaka, almajiiri, dalibta da sauransu.

5. Zumunci na ra'ayi (tunani)
gyara sashe

Wannan kan shafi mutane da suka yi tarayya a ra'ayi kamar addini, ko siyasa, ko kulob, ko wasanni da sauransu.

6. Ziyara
gyara sashe

Na nufin ka tafi gari, ko gidan wani da nufin ku gaisa da dalili, ko babu. Ana iya cewa wannan al’ada ko ba a daina to Bahaushe ya rage yinta matuka. Wannan kuwa baya rasa dalili na sauyin zamani. Domin zamani ya kawo abubuwan sufuri ba za a yi tafiya sai da kudin mota, a wani lokaci da yar tsaraba da matafiyi zai rika don yara.

Haka shi kuma mai masauki zai tanaji abin da zai yi wa bakonsa hidima da kuma abin sallama. To yanzu son abin duniya da ganin gari da bakar rowa sun hana ziyartar juna. Kowa sai ya fake da babu, ana iya samun dan uwa na jini sun yi shekara da shekaru ba'a ziyarci juna ba. Ba wai wa]anda suke garuruwa daban-daban ba, a a hatta waɗanda suke gari daya.

7. Gudunmowa
gyara sashe

Wannan wata hanya ce ta taimakawa juna wajen yi ma mutum wani hasafi na musamman a lokacin wani sha'ani kamar na aure ko suna, don a zamanto taimakwa wanda abin ya shafa. Sau da yawa a kan taimaka da hatsi, ko kudi, wani lokaci ma har da tufafi da dai duk wani abu mai amfani. Akwai kuma gudunmuwa da akan yi wa wadanda suka yi gobara, ko kuma wadanda aka yi wa sata.

Wannan ma wata hanya ce ta taimakawa juna, amma ta wajen aiki. Aikin gayya ba a yin shi sai da dalili, kamar rashin lafiya ko kuma wata larura ta musamman. A kan taimakawa mutum a aikin gona, ko kuma aikin gida da sauransu. dan uwa da abokan arziki na unguwa su ne su kan taru su taimaka.

Baya ga taimakawa da a kan yi wa juna kuma, sarki ko mai unguwa ya kan yi gayya don a rage masa  aiki. Idan sarki ya kira gayya, to kusan ba wanda ba zai amsa wannan kira ba.

Mata su ma suna yin gayya irin ta su, misali in an yi sabon daki za a yi dabe. Duk wanda ya yi gayya, to dole ne ya yi abincin gayya saboda jama'ar da suka zo aiki su ci.

9. Aikin Gayya
gyara sashe

Wannan shi ma wani aiki ne da ake taimakawa juna ta hanyar haduwa a yi aikin taimakon kai da kai, ko kuma idan wani bashi da lafiya ya kasa gyara gonarsa sai a yi gayyar fan uwa da abokan arziki da ya kamata a tafi a nome masa kyauta. A irin wannan har akan yi fura da kunu ko tuwon gayya don ma’aikata su ci ko su sha. A nan ne ma har aka samu karin magana mai cewa "kowa ya sha furar gayya dole ya yi aiki".

Shata Katsina sai ya ce "ka sha furar mutane kace zaka yi kwance a a ku tashi gumi na nake ci" . Zamani ya zo yayi barin makauniya da wannan dabi’a. A yau komai sai dai kudinka ya baka ko yasa a yi maka. Bahaushe ya tabbatar da wannan a inda ya kirkira wata magana mai cewa: “Nasara ya hana aikin banza”. Ko kuma: “Kowa tashi ta fisshe shi”.

10. Zaman Gandu
gyara sashe

Wani zama ne da ake yi, a inda za a iske kaka, da ubada da uwa, da da da matarsa, da jikoki duk a gida daya ga dakin wannan ga na wannan. A irin wannan zama ana kasancewa komai tare ake yi. Da damuna za a tafi gona ta mai gida da ake kira gonar gandu a wurin aiki. Bayan an dawo, maigida ne zai ciyar da kowa, ko da kowa dansa yana da mata da yaya, dole shi ne zai ciyar da su.

Irin wannan rayuwa tana da dadi matuka, domin ana taimaka wa juna a harkokin rayuwa ta fuskoki da yawa.

Ba a farga ba, zamani ya zo ya yi tafiyar ya ji da wannan ɗabi’a. Musamman samuwar aikin gwamnati, a inda za a ɗauki mutum ya koma wani garin da ba nasa ba, ko kuma ko yana gari, sai ka iske ya ware gidansa shi kaɗai wai kar a dame shi. A nan ne ake rayuwa irin ta daga ƙwauri sai gwiwa, ko kuma mu ce ba ruwan wani da wani wai mahaukaci ya yi baƙo. ba abin da wannan yake koyarwa sai Ƴar karen rowa.


Zumunci

TSAKURE: Maƙasudin wannan muƙala shi ne ƙoƙarin gano tare da yin nazari a kan matsayin da zumunci ke da shi a rayuwar Bahaushe. Haka kuma nazarin zai waiwaya baya don ƙyallaro yanayin da zumunci yake a zamanin da,tare da fito da halin da zumunci ke ciki a zamanin yanzu.

Bayan wannan kuma zamu dubi irin gurɓacewar da harkar zumunci ta yi.Fayyace wasu dalilai waɗanda suka yi sanadin haka, da kuma tasirin da hakan ya yi a rayuwar Bahaushe a yau. Haƙiƙa akwai wasu matsaloli,  da suka taimaka sosai wajen lalacewar, ko taɓarɓarewar harkar zumunci, wanda a ƙarshe ya shafi zamantakewar Bahaushe baki ɗaya.

Wannan muƙala ta kawo waɗannan matsaloli gami da dalilan da suka yi sanadin hakan. Domin ƙarawa daɓe da makuba, d  nazarcin wasu litattafai, kundayen bincike tare da wasu muƙala waɗanda suka yi magana a kan irin amfanin zumunci da kuma  moriyar da ake samu. Bayan mun dubi matsalolin sai kuma mu jero wasu shawarwari da zasu  taimaka wajen fito da Bahaushe daga cikin wannan hali:

BITAR AYYUKAN MAGABATA

Babu shakka, an yi rubuce-rubuce da dama, da suka shafi zumunci da matsayinsa a rayuwar Bahaushe. Kowanne masani da irin gudunmowar da ya bayar. Wannan kuwa ya faru ne, a dalilin cewa, kowanne marubuci akwai inda ya fi mayar da hankalinsa. Watau wasu marubutan sun yi amfani da wasu bayanai da suka shafi  zumunci kai tsaye.

Wasu kuma a matsayinsa ta fuskar addini, wasu kuma, wasu kuma al’adan ce,suka kalle shi,waɗansu kuma a siffar rubutun zube da sauransu. An yi rubuce-rubucen ne a wasu littattafai da aka wallafa, da wasu kundayen digirin M.A., da na B.A.,  ko mujallu, ko muƙala, ko jaridu da sauransu.

A’isha Umar Wali(1990) a kundinta na Digiri na biyu mai take Hausa KingshipTerm.

Duk da yake Turanci a ka yi yana da alaƙa da muƙalar.

Mu’azu M.S.(1998) a kundinsa na Digiri na ɗaya mai taken  Zumuncin Bahaushe.Wannan aikin yana da alaƙa da muƙalar.

Banta Margaret(1990) a kundinta na Digiri na ɗaya mai taken  A survey on the adjustment Problems of Widows and Single Parents in our Society.Duk da yake Turanci a ka yi yana da alaƙa da muƙalar.

Jabiru Abdullahi(1958)a littafinsa mai suna Nagari Na kowa.littafin yana da alaƙa da muƙalar.

Imam A.(1937) a littafinsa mai suna Magana Jari ce, littafin yana da alaƙa da muƙalar.

Imam A.(1937) a littafinsa mai suna Ruwan Bagaja, littafin yana da alaƙa da muƙalar.

Habibu Sarki A.(2000) a littafinsa mai suna Zuwan Musulunci  a Afrika,da shigowarsa ƙasar Hausa, littafin yana da alaƙa da muƙalar.

GABATARWA

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinqai, Mai kowa, Mai komai, Mai aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so,  a sadda Ya so, a yadda Ya so, ko ana so ba a so tilas bayi su so. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu(sallallahu alaihi wasallam), da Alayensa da Sahabbansa,da sauran Mabiyansa umuman.

Wannan muƙala na da ƙudurin yin tsokaci a kan matsayin da zumunci ke da shi a rayuwar Bahaushe. Haka kuma,tare da fito da irin gurɓacewar harkar zumunci da kuma tasirin da haka ta yi a rayuwarsa a yau.Haƙiƙa akwai wasu matsaloli  da suka zama ƙashin baya wajen lalacewar ko taɓarɓarewar harkar zumunci, ko kuma a ce zamantakewar Bahaushe baki ɗaya.

Wannan muƙala babu shakka tana da muhimmanci, saboda za ta yi magana a kan irin amfanin zumunci da kuma  moriyar da ake samu. Bayan haka,za’a dubi wasu matsalolin da suka taimaka wajen jefa Bahaushe cikin wannan hali. Waɗannan matsaloli sun watsu a gida da daji,sannan kuma,Bahaushe na karo da su ta fuskoki daban-daban.

Wannan ne ma yasa na kira muƙalar da cewa: “Taɓarɓarewar zumuncin Bahaushe a yau. ”(Lalacewar zamantakewa a ƙasar Hausa).Watau abin da nake nufi shi ne,matsayi ko halin da zumuncin Bahaushe ke ciki a rayuwarmu ta yau,sannan kuma da irin tasirin da hakan ta haifar. Babu shakka,ko ba a shafa ba maruru ya fi kaluluwa in ji makaho. Tabbas dukkan wanda yake cikin hayyacinsa ya san cewa Bahaushe ya samu kansa na gaba kura baya siyaki. Wannan mawuyacin hali kuwa,shi ne, na lalacewar, ko gurɓacewar  zumunci a zamanin da muke ciki.Tarihi ya nuna cewa Bahaushe na da al’adar kyakkyawar zamantakewa a da. To sai dai kuma yanzu  ya tsinci kansa a cikin wani rami  mai gaba dubu. Domin kuwa Bahaushe ya ce “tsalle ɗaya kan yi ka faɗa rami, ka yi dubu ba ka fita ba”.Haka kuma ya ce “ruwa baya tsami banza” ma’ana babu abin da zai faru sai da dalili.

Don haka taɓarɓarewar harkar zumuncin Bahaushe bai rasa wasu dalilai. Bisa dogaro da waɗannan maganganu ya sa  za mu kalli al’amarin zamantakewar Bahaushe a yau, da irin halin da ta faɗa,tare da duba wasu daga cikin dalilan da suka yi jagorar hakan.     

Bugu da ƙari kuma, na tsara muƙalar tawa kashi uku kamar haka: Kashi na farko,ya ƙunshi taken muƙalar ,sai gabatarwa,da ma’anar kalmar taɓarɓarewa,da ta  zumunci tare da ire-irensa da kuma dalilai ko sanadinsa.

Kashi na biyu kuma,zai kawo wasu daga cikin matsalolin da zumunci ke fuskanta, a nan kuma za mu dubi waɗanne irin matsaloli ne,kuma me ya kawo su ?

A kashi  na uku,zai ƙunshi wasu shawarwari game da wasu hanyoyi da nake ganin, idan aka bi su  za  a iya samun mafita. A qarshe na rufe ta da kammalawa da madogara.  


Ma’anar Zumunci  

         

Da zarar an ambaci kalmar zumunci a al’ummar Hausawa, babu  abin da zai zo masu a zuciya da ya wuce wata dangantaka ta musamman da ke tsakanin mutum da mutum wadda ta shafi dukkan fannonin rayuwa.To sai dai wasu Masana sun ba wannan kalma ma’anoni daban-daban,kamar haka:   

Zumunci na  nufin wata dangantaka ce ta jini (haihuwa), ko ta aure,ko ta zamantakewa (maƙwabtaka ko mu’amulla). Zumunci na  nufin dangantaka, ko dangi, ko ƴan uwa.

Zumunci wata alaƙa ce tsakanin mutum biyu, ko ƙungiyoyi,ko ta zamantakewa (maƙwabtaka ko mu’amulla). Zumunci wata alaƙa ce tsakanin abubuwa,ko dangi,zuriya ɗaya a dalilin haihuwa,ko tabanni(goyon hankaka mai da ɗan wani naka ), ko aure.


Bisa la’akari da bayanai da suka gabata, muna iya cewa, Wannan kalma ta zumunci,da kuma ma’anoni daban-daban, da masana, suka bayar muna iya cewa zumunci wata alaƙa ko dangantaka,ko nasaba,ko jituwa ce dake ƙulluwa ko haɗa mutane daban-daban kan harkokin da suka shafi rayuwa ta yau da kullum.

NAU'O'IN ZUMUNCI

Al’amarin zumunci a al’ummar Hausawa abu ne da za’a ce yana da rassa ko yana yaɗuwa fiye da kowace ƙabila ko al’ummar da ke maƙwabtaka da Hausawa. A wannan mataki za mu yi nazarin nau’o’in zumunci al’ummar  Hausawa da dalilan a kansa a sami wata mu’amulla da kan haifar da zumunci. Akwai nau'in zumunci ko zumunta iri daban-daban waɗanda kan wakana a tsakanin al'umma bisa wasu dalilai kamar haka: -

1.  Zumunci na jini (haihuwa ko zuriyya):- Wannan kan ƙunshi mutane irin su uwa da uba, Ƴaƴan tsatso, Ƴan uwa, Ƴan uba, kawu, inna, gwaggo, baffa, yaya, ƙani da sauransu.

2. Zumunci na soyayya (auratayya):- wannan kan shafi mutane irin su miji da mata, da suruki,da  suruka,da agola,da ɗan riƙo,ko tabanni.

3. Zumunci na zamantakewa (maƙwabtaka): - wannan kan shafi mutane a wurin maƙwabtaka na gida, ko kasuwa, ko gona, da sauransu.

4. Zumunci na mu'amulla (sana'a, moriya) : - wannan kan shafi mutane masu sana'a iri ɗaya ko kuma abokan ciniki, barantaka, almajiiri, ɗalibta da sauransu.

5.  Zumunci na ra'ayi (tunani): - wannan kan shafi mutane da suka yi tarayya a ra'ayi kamar addini, ko siyasa, ko kulob, ko wasanni da sauransu.

ZUMUNCIN JINI  (HAIHUWA KO ZURIYA)

Zumunci na jini shi ne,wata dangantaka ko alaƙa da ta shafi haihuwa ko zuriya ,wato ta dalilin haɗuwar iyaye ko kakanni. Wannan zumunci na iya kasancewa na kusa ko nesa. Akan sami zumunci ne a samakon kyakkyawar dangantaka tsakanin mutanen da suka fito tsatso ɗaya, suka kuma haɗa uwa ko uba ɗaya wannan shi ake kira shaƙiƙin ɗan uwa .

Dangantaka ta kusa kan iya ƙulla zumuncin  jini a tsakanin  ƴaƴan da ma’aurata(mace da namiji) suka haifa, ko  ƴaƴan da mace ta haifa waɗanda ba ubansu ɗaya ba, ko kuma ba uwansu ɗaya ba. Ƙulla irin wannan zumuncin  ba  abin mamaki ba ne a al’ummar Hausawa, tun  da yake yawancin su musulmai ne, kuma ƙa’idar  addinin ta yarda  namiji ya auri mace fiye da ɗaya (amma ka da ya wuce huɗu).

Ita ma mace tana iya yin wani aure, idan ta fito daga gidan wani mijin, a sakamakon rasuwarsa  ko rabuwar  aure. Domin  haka ana iya samun zumunci tsakanin Ƴaƴan da suke uwa ɗaya, uba ɗaya, da waɗanda suke uba ɗaya uwa kowa da ta sa. Haka kuma a tsakanin Ƴaƴan da suke uwa ɗaya, uba kowa da nasa.

Baya ga wannan  zumunci na kusa,  akan  samu na nesa, kamar  waɗanda suke kakanni ɗaya, wato ɗan wa da ɗan ƙani, ko kuma ɗan mace,  da ɗan namiji.

Wani irin nau’in  zumuncin  jini  kuma, da ake samu a tsakanin  Hausawa, shi ne irin dangantakar da ake samu a dangin uwar mutum, ko ta dangin uba. A dangi uwa akan samu wannan, Wa to ƙanin uwa waɗanda ake kira kawu. Haka kuma akan samu Ƴar uwa ko ƙanwar  uwa waɗanda ake kiransu da Inna. Ta ɓangaren dangin uba akwai wan uba, ko ƙanin uba, akan kira shi da Baba ko Baffa,sannan  sai kuma Ƴar uba ko ƙanwar uba ana kiransu da Gwaggo.

Kyakkyawan zumuncin da Bahaushe ya gada kan sanya a girmama waɗannan, kamar  yadda zai girmama iyayensa da suka haifeshi ko ma fiye.Tare da ɗauke masu ɗawainiyar wasu al’amura, kamar aikace -aikace ko taimaka masu da wani abin da ya mallaka.

Irin wannnan zumunci yakan yi danƙo a al’ummar Hausawa, a yayin  da yaro kan iya tashi a gidan ƙannai ko yayyen  iyayen sa. Ba tare da samun wani bambanci na tarbiyar, ko rashin nuna ƙauna ba, kamar yadda zai iya samu a gidan iyayensa. Haka kuma dangantakar kasancewar yara ƴaƴan maza (ƴaƴan wa da na ƙani) kan sanya  a samu kyakkyawan zumunci a tsakaninsu.

Musamman na girmama juna da shawartar juna a kan lamura, kai ka ce dai uwarsu ɗaya uba xaya. Dangantakar Ƴaƴan mace da na namjii waɗanda akan kira taubasai al’ummar Hausawa ya haifar da wasan ba’a,ko raha a tsakaninsu. Waɗannan wasannin na ba’a ko raha sukan sa a samu kyakkyawan zumunci mai ɗorewa wanda a wasu lokutan ma yakan kai ga auratayya, ban da wannan kuma akwai kuɗin shara da taubasai kan ba junansu a duk ƙarshen shekara, shi ma wannan ba ƙaramar gudummawa ya yi ba. A sakamakon bai wa zumunci muhimmanci da Bahaushe yake yi, shi  ya sa Hausawa ba su ƙyashin haɗa dangantakar aure a tsakanin ƴan uwan jini (wanda shari’a ba ta hana ba) don ƙara danƙon wannan zumuncin. Wannan shi ya sa Hausawa ke kiran sa auren zumunci. Wannan irin ƙaunar juna ta al’adar zumunci ta kawo haɗa kai da bai wa kowa matsayinsa a  cikin  zuriya guda.Kamar Babba ya ja girmansa ya tausayawa na ƙasa ko yaro. Shi kuma yaro ya girmama Babba ta hanyar yi masa ladabi da biyayya. A dalilin haka ne ya sa ko da yaushe Babban shi ke wucewa gaba ko da kuwa kan hanya ce, wato in ana  tafiya.Haka kuma shi ne mai ɗaukar nauyin duk  wani na ƙasa da shi. Za mu iya kafa hujja da wasu al’adu da ake gudanarwa a al’umar Hausawa, kamar wajen harkar aure.A inda za ka samu ana gudanar da wasu al’amura a gidajen ƴan uwan iyaye kamar haka: in har mutum na da na gaba da shi kamar  wa. To in dai za a zo neman auren ƴarsa, to ba za a zo wurinsa kai tsaye ba, sai dai a tafi wurin na gaba da shi,sannan kuma  ya bayar da ita.  Ban da neman aure, ko wajen maɗaurin  auren ma  dai ƙanin  uba yake  ɗaura auren  a matsayin waliyi. Haka kuma ko wajen sanya yarinya a lalle,da  zaman lalle, uwar wanka da sauransu. Duk za a tarar ƴan uwan iyaye ke gudanar da su, ko da kuwa a ce ga iyayen ana gani. Haka kuma taimakawa mai wata hidima da ƴan uwa  suke yi, wato gudummawa ta kuɗi,ko sutura,ko  abinci. Kai wani lokaci ma har da muhalli, sai ka ga an yi sha’ani ba tare da mutum ya wahala ba. Ban da wannan kuma ƴan uwa na jini kan zama kamar alƙalai, ko mahukunta,saboda sau da yawa in an samu saɓani tsakanin ma’aurata (mata da miji). Manya a gida, ko zuriya su kan sulhuntasu, ko ma ba ma’aurata ba. In dai har aka samu saɓani a tsakanin ƴan uwa to sai ka ga an kira su don a yi sulhu. Haka kuma, ta fuskar haihuwa ma zumunci bai kau da kai ba, nan ma ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa zumunta

ZUMUNCIN SOYAYYA

Zumuncin Soyayya na nufin kyakkyawar dangantaka ko mu’amulla da ta ƙullu a tsakanin mutum biyu ko fiye a sakamakon ƙauna, ko tausayi, ko kuma auratayya. Wato waɗannan kamar wasu matakai ne na samar da zumuncin soyayya.

AURE:

Dangane da zumuncin da aure yake ƙullawa ana iya duba abin ta fuskoki da yawa. Akan sami zumunci tsakanin miji ko maigida da matarsa ko matansa, sai kuma tsakanin matan su kansu. Wato kishiya da kishiya, ko kuma tsakanin miji da iyayen mata wato surukai, har ma ya zuwa dangin matar. Akan samu zumunci tsakanin mata da iyayen miji, wato surukanta. Irin wannan zumunci yakan yi naso har ya zuwa ga dangin miji gaba ɗaya. Haka kuma akan samu zumunci da dangantakar aure ta samar, kamar tsakanin maigida da ƴaƴansa na cikinsa da ƴaƴan da matarsa ta zo da su (agola) da dai Sauransu. Bisa ga yadda zumunci ke gudana a tsakanin miji, ko maigida da matarsa ko matansa. Abu ne da ba a iya faɗa gaba ɗaya ba, sai dai a kwatanta. Wannan kuwa ya haɗa da yadda suke gudanar da harkokin gida, kamar ƙaunar juna da kare mutunci da riƙe amana a tsakaninsu da ɗaukar ɗawainiyar gida ga miji. Misali kamar ciyarwa da shayarwa, da tufatarwa da kuma muhalli da sauransu.

Ita kuma matar wasu ƙananan hidimomi na gida kamar dafa abinci, kula da yara da tsabtace muhalli da dai sauransu al’amura. Zumunci tsakanin mata da miji kan yi danƙo ƙwarai idan kowane ya ɗauki ɗawainiyar da ke kansa, ba tare da cuta ma wani ba. Irin wannan zumunci idan ya yi kyau yakan fi na jini, musamman da yake ana gudanar da rayuwar tare a kullum.

Bayan wannan kuma, sai mu duba yadda dangantakar kishiya da kishiya ke samar da zumunci a al’ummar Hausawa. A irin yadda suke gudanar da al’amuran gida, kamar raba kwana da miji zai riƙa yi a tsakaninsu. Ko kuma raba girki, da dai duk wani abu da ya shafi harkokinsu a wurin miji. Idan zama tsakanin kishiyoyi ya yi kyau, to sai ka ga gida ya zauna lafiya. Domin za a ga kishiya na girmama wadda ta riga ta shigowa gidan, tana kiranta da suna yaya, ko kuma mamar wane da makamantansu. Wato saboda ƙarfafa zumunci.Al’adar Bahaushe ta hana amarya ta kira uwargida da sunanta kai tsaye. Da yake Bahaushe mutum ne mai ɗaukar nasa kamar ba nasa ba, zumuncin Bahaushe na tsakanin kishiyoyi kan sa ƴaƴan uwargida su tashi (girma) a ɗakin  Amarya, ko kuma na Amarya su tashi a ɗakin uwargida ko kuma duk ƴaƴan mijin su tashi a ɗakin uwargida. Wato sukan samar da kyakkyawar zumunci da akan kasa bambance ɗan wannan da na waccan. Zumunci tsakanin kishiyoyi ma idan ya yi kyau, yakan yi naso har ga ƴan uwansu.

Wata rawar da zumuncin aure ke takawa, a wajen ƙarfafa zumunci, shi ne yadda Hulɗa ke gudana a tsakanin miji da dangin matarsa, ko kuma matar da dangin mijinta. Domin kuwa in har aka yi dace, zama ya yi kyau ana zaune lafiya, to sai a ga ana gudanar da kyakkyawan zumunci. Ko da yake, idan aka kuskure aka yi rashin sa’a aka samu Ƴar ɓaraka,ma’ana in babu jituwa a tsakanin sai ka tarar ana zaman-doya-da-manja. Ko da kuwa ma’aurata na son junanasu. Wannan kuwa na faruwa mafi yawa a inda aka yi auren ƙi, ko na kangara. Wato a samu wani sashi na dangin ma’auratan ba sa son auren.

Dangantakar aure a al’ummar Hausawa yakan samar da kyakkyawan zumunci tsakanin maigida da ƴaƴan da mace ta zo da su (Agola) ko tsakanin mace da ƴaƴan riƙon mijinta. A al’adance maigida in ba ya nuna bambanci tsakanin ƴaƴansa da waɗanda ba nasa ba.

Domin yakan ba su abinci iri ɗaya, sutura iri ɗaya, makaranta ɗaya, kai har da ɗaukar ɗawainiyar aure da sauran harkokin rayuwa. Akan gane kawai cewa ba ƴaƴansa ba ne,har sai  an zo rabon gado, ma’ana bayan rasuwarsa. Ita ma mace takan ɗauki ƴaƴan da mijin yake riƙo kamar ƴaƴan cikinta. Wato ba a iya bambance ƴaƴanta da waɗanda ba nata ba. A al’adar auren Hausawa musamman na budurwa, takan tafi gidan miji da wata  ƙanwarta, ko wata ƴar uwarta, wadda akan kira ƴar zaman ɗaki ko ƙanwar rana. Maigida da sauran mutanan gida ba su kan nuna wa ita wannan ‘yar zaman xaki bambanci ba, takan saje da ‘yan gidan.

A ci da ita a yi mata duk abin da za a yi wa ‘yangida. Idan zumunci ya yi danƙo, a nan za a nemi aurenta mijin uwar xakinta ya zama uban auren. A  ala’adar Bahaushe akan yi wasannin raha tsakanin matar wa da ƙanin miji. Haka ita ma mace takan yi irin waɗannan wasanni da ƙanin miji da kuma taubasai. Wannan al’ada kan haifar da kyakkyawan zumunci tsakanin  mutanen  da suka ƙullu da dangantakar ko da kuwa auren ya rabu.

Haka kuma haihuwa, wani ginshiƙi ne da ke ƙara ƙarfafa zumuncin aure. Da zarar aka ce ma’aurata sun sami haihuwa a tsakaninsu, to zumunci ya ƙullu ke nan. Ko da kuwa aure ya rabu, ko kuma ɗaya daga cikin iyayen sun mutu, akan samu wata hulɗa na gudana a tsakaninsu. Haka kuma wannan haihuwar kan zama wata abin yin inkiya, saboda a wani lokaci sai ka ji ana cewa ai wane ne uban ƴaƴanta, ko kuma wance ce uwar ƴaƴansa. Dole ne iyayen, ko ƴan uwan ƴaƴan su kasance a wuri ɗaya a wasu shagulgula da suka shafi ƴaƴan nasu kamar sha’anin aure ko haihuwa. Haka ma idan wani abin baƙin ciki ya faru kamar mutuwa, ko gobara da dai sauransu. Bayan haka kuma, haihuwa kan haifar da wata alaƙa da ta zama kamar zare da ta ɗinka tsakanin ma’aurata da iyayensu, wato kakanninsa abin da aka haifa, saboda wannan jituwa ne ta ke tsakanin jika da kaka ake samu wata ƙauna mai ƙarfi  ta sarƙu. Wannan ne kan sanya ake jin kaka mace na kiran jikanta “miji” ko maigida. Haka shi kuma kaka namiji ya na kiran jikarsa da matata. In kuma jikan namiji ne sai ya ce aboki. Haka ita ma kaka mace ta kan kira jikarta da ƙawa, ko kishiya da dai sauran wasanni na raha don nishaɗi da nuna ƙauna.

A sakamakon al’adun aure a al’umar Hausawa, akan samu kyakkyawar dangantaka na surukuta. Surukai su ne iyayen matar  da ya ke aure (maza da mata) da kuma yayyenta maza da mata. Haka ita ma iyayen mijin mace maza da mata da kuma yayyensa maza da mata sun zama surukanta. Namiji yakan girmama surukansa kamar yadda yake girmama iyayensa ko fiye. A al’adance dole ne a ce mutum na jin kunyar surukansa, a inda ba ya iya sakin jiki ko ya furta wasu maganganu a muhallin da surukansa suke, haka ita ma macen. Tsakanin mutanen da iyayensu ke auren juna ma akan sami kyakkyawar fahinta wannan kyakkyawar dangantaka, da ladabi, ko girmama juna da ake samu a lamarin surukuta a al’ummar Hausawa.Tabbas shi ke haifar da kyakkyawar zumunci tsakanin mutane da suka ƙullu da dangataka. Zumuncin  da auren Hausawa kan samar, kan yi naso har  ya kai ga samun kyakkyawar dangantaka tsakanin  ƙauyuka, ko garuruwa. A  sakamakon  auratayyar da akan samu tsakanin wannan ƙauyen da wancan, a al’umar  Hausawa yakan sa a samar da kyakkyawan zumunci a tsakanin ƙauyukan. A  inda za a ga suna yin ruwa suna  yin  tsaki akan duk  wani lamari da ya shafi ɗaya ƙauyen. Haka kuma a wasu lokutan akan samu wasannin raha a tsakanin al’umma a sakamakon irin wannan auren.

A taƙaice muna iya cewa ba don ɗebe sha’awa kawai da samun zuriya ake yin aure ba. A’a har da  samar da zumunci a al’umma da kuma kyautata shi,sannan yana taka mahimmiyar rawa a lamarin aure. Wato ta kowane ɓangare aka dubi dangantarkar da aure ke ƙullawa a al’umar  Hausawa. Haƙiƙa za a tarar da wani zumuncin  da ya ginu wanda ana iya cewa ba zai taɓa  rushewa ba har abada. Ko da kuwa auren ya rabu ko ma’auratan sun rasu.

RIƘO KO GOYO

Riƙo ko goyo shi ne, wani mutum ya riƙe ɗan wani, tun daga yarinta har zuwa girma. Idan yaro namiji ne, a wasu wuraren akan mayar da shi wurin ubansa. In kuwa mace ce, da zarar yarinya ta isa aure, to daga nan shi ke nan, riƙo ko goyo ya ƙare ke nan. Riƙo ko goyo yakan gudana a tsakanin ƴan'uwa da ɗan uwa, ko kuma aboki da aboki, ana yinsa ne, saboda wasu dalilai da suka haɗa da: -

i. Zumunci.

ii. Haihuwa.

III. Ƙauna.

vi Tausayi.

V  Moriya

vii Tabanni

ZUMUNCI: Goyo ya kan taka rawa mai muhimmanci ga rayuwa ta wajen ƙarfafa danƙon zumunci.Domin za ka iya samun wani ya kama ɗan ƙanin sa ko ɗan ɗanwarsa ya riƙe tun daga yarinta har zuwa girma. Sau da yawa wani riƙon kan fara ne tun daga yaye, watau lokacin da aka cire yaro daga mama, nan ma ya fi faruwa ne a tsakanin ƴan uwa kamar kaka, ko Ƴar uwa ko uba.

Wannan abu ya kan ƙara ƙarfafa zumunci, don kuwa yakan faru in ka samu wani gidan inda ake riƙon wani, ba za ka iya banbance ɗan gidan ba ko ɗan riƙo ba, za ka gansu babu wata wariya. Komai nasu iri ɗaya ake yi masu, sutura, abinci kai har ma aure, wannan kan ƙara ƙulla zumunci.

HAIHUWA: A wata fuska kuma, a kan ɗauki riƙo ko goyo ne, don kwaɗayin samun haihuwa. Kamar yadda wasu Hausawa musamman ma mata kan camfa, cewar, idan mutum ba ya haihuwa, to lallai ne in ya ɗauki goyo, Allah Zai ba shi nasa. Haka nan kuma, wasu don dai ba sa haihuwa, to sai su ɗauki goyon don dai su rinƙa samun na aike. A ƙarshe akwai masu ɗaukar yara don sabo, misali in sun aurar da yaransu, to don kawai su ɗauke kewa, sai su ɗauko wani.

ƘAUNA: Baya ga waɗannan, akwai kuma masu ɗaukar goyo don ƙauna, kamar inda za ka samu cewa wasu mutane na ɗaukar goyo ne kawai, don ƙauna, watau soyayya. Inda za ka samu babu dangin iya, babu na baba, ma'ana babu dangantakar komai sai dai aminci, watau abotaka. Misali  aboki, ko maƙwabci da maƙwabci, inda za ka tarar ɗaya ya kama yaron ɗaya ya riƙe, babu bambanci kamar shi ya haife shi. A wani lokaci ma yakan fifita shi a kan waɗanda ya haifa.

TAUSAYI: Akan yi goyo a wani lokacin don tausayi, ma'ana shi ne, in wani mutum ya ga wani yaro a wani matsayi na ƙaƙa ni ka yi to don tausayawa, ko da ace yana tare da iyayensa ne, akwai ma inda za ka tarar ana riƙon yaro ko yarinya, sannan kuma ana taimakawa iyayenta a lokaci guda.Bayan wannan kuma, sai a wata fuska inda za ka samu an riƙe almajiri don tausayawa. Misali in almajirin ƙarami ne za ka samu ya yi uwar ɗaki wadda zai riƙa samun taimako na abinci, ko sutura. Haka kuma akwai waɗanda uwarsu ta mutu bayan haihuwa watau talle, su ma don tausayi akan ɗauke su. Ko da babu dangantaka, ko yaron da aka tsinta.

MORIYA: Akan yi goyo don moriya, a inda za ka samu an ajiye bara, ko yaron gida yana yi wa mutanen gidan hidima.Watau kamar dai mai aiki, akan samu mai yin hidima, wani tun yana  yaro har girmansa ko da mace ce, ko kuma namiji.Sannan kuma akwai waɗansu masu yin sana'a, inda sukan mallaki barori masu kula da harakokin kasuwanci. Su ma wasu tun daga yarinta har zuwa tsufa, har ma wani lokacin su ma su samu su kafu su yi ƙarfi su samu abin hannunsu.

AGOLA: Goyon  agola yakan faru ne, in aka auro mace mai ɗa ko ƴa, to akan kirasu da sunan agola ko Kolo. A bisa al'adar  Bahaushe  riƙon agola yakan zama dole ne, misali idan uban yaron ko yarinyar ya mutu.Ko kuma dangin uban yaron ba su a garin, ko kuma yaron bai yi girma ba. Su kansu dangin uba ba sa son a tafi da yaronsu wani gida ya zama agola don gudun wulakanci. Ko kuma kar a  raba shi da ƴan uwa, shi yasa wasu duk juyin da za a yi ba za su yarda a kai yaronsu wani gida ba. Shi yasa in mace ta fita, to sai a yaye yaron daga mama a sanya wani a cikin dangi ya & auka don kawai ƙyamar agolanci.

TABANNI: Wannan  goyo  akan yi shi ne a wani lokacin don tausayi, ma'ana shi ne in wani mutum ya ga wani yaro a wani matsayi na ƙaƙa–ni- ka -yi.To don tausayawa, ko da a ce yana tare da iyayensa ne, ko kuma Maraya. Akwai ma inda za ka tarar ana riƙon yaro ko yarinya, sannan kuma ana taimakawa iyayensu a lokaci guda. Bayan wannan, sai kuma a wata fuska, inda za ka samu an riƙe almajiri don tausayawa, misali in almajirin ƙarami ne, za ka samu ya yi uwar ɗaki wadda zai riƙa samun taimako na abinci, ko sutura. Haka kuma akwai waɗanda uwarsu ta mutu bayan haihuwa, watau talle, su ma don tausayi akan ɗauke su, ko da babu dangantaka, ko kuma yaron da aka tsinta.

To amma kuma, daga ƙarshe sai a mayar da su kamar ƴaƴan tsatso, watau za su iya gadon mai riƙonsu. A wani lokaci akan kira irin wannan goyo da  goyon hankaka mai da ɗan  wani naka.  

   

ZUMUNCIN ZAMANTAKEWA

Zumuncin zamantakewa, shi ne wanda ya shafi sha’anin zaman tare da yadda ya danganci harkokin rayuwa yau da kullum. Kamar maƙwabtaka, da abota, da almajirci da kuma barantaka da dai sauransu.

MAƘWABTAKA

Zumunci da ya shafi maƙwabtaka yakan faru ne, a sakamakon kusantar juna ta fuskar Muhalli. Bahaushe kan kira mutanen da suke kewaye da gidansa da maƙwabta. Wato waɗanda suke gabas da yamma, da kudu da arewa. Haka kuma akan ɗauki duk gidajen da ke anguwa ɗaya a matsayin maƙwabtan juna. To sai dai mafi kusanci dangane da lamarin maƙwabtaka su ne, waɗanda suka haɗa katanga ko wanda suke kallon juna dab da dab. A al’umar Hausawa akan samu zumunci maƙwabtaka tsakanin unguwa da unguwa, ko tsakanin gari da gari.

Bayan wannan kuma, yanzu an samu ci gaban zamani.Ta inda akan samu zumunci ta haɗuwar gunduma ɗaya, ko ƙaramar hukuma ko Jiha ɗaya.Ko kuma Ƙasa baki ɗaya.To amma wannan ya fi  faruwa in ana nesa da gida.

Zumunci maƙwabtaka ba ƙaramar rawa yake takawa ba,ta hanyoyi da yawa. A wasu lokuttan, sai a samu yaran maƙwabta sun tare a gidan maƙwabci. A wani karon ma ba za a iya bambance ɗangida da wanda ba ɗangida ba. Haka nan kuma, wannan Hulɗa kan haifar da cuɗanya da shaƙuwa ta harkokin yau da kullum. Kamar are-aren wasu kayan aiki, misali  dagi, da tsani, da kwangiri,ko adda da sauransu.Wannan ya haɗa da musayar kyaututtuka da nuna damuwa kan wani abin da ya shafi maƙwabci,tun daga kan maza har mata. Ban da wannan kuma su kansu mazan sukan haɗu, kowa ya kawo abincinsa a taru a ci gaba ɗaya(ciyayya).

Game da su kuwa mata, akan samu musayar kyauta musamman abinci dangin kayan marmari da ake kira kawo ƙwarya,ko ɗauki. Haka kuma a lokacin bikin sallah, ko wani biki, ko kuma wata tsaraba, ko kuma haka nan kawai.

Al’amarin maƙwabtaka ba ƙarami ba ne, don kuwa Bahaushe ya ɗauke ta da muhimmanci.Wannan kuwa, tun gabanin zuwan addini Musulunci ƙasar Hausa. To da addinin Musulunci ya zo kuma, sai ya zamanto ya ƙara ƙarfafa sha’anin maƙwabtaka, kamar yadda ya zo a cikin littafin Riyadil Salihin.

Inda wani hadisi yace, Abdullahi  Ɗan Umar yace: Manzon Allah (S.A.W) ya ce:

“ Akwai wata rana da mala’ika Jibril ya zo  masa ya faɗa masa (Annabi)  haƙƙoƙin maƙwabci a kan maƙwabci, har sai da Annabi ya yi tsammanin maqwabci zai iya gadon maƙwabcinsa, saboda tsananin kusanci da nuna dangantaka”.

Haka kuma, akwai abubuwa da suka faru tsakanin Annabi Muhammadu (S.A.W) da wani Bayahude maƙwabcinsa.

“An ruwaito cewa Annabi(S.A.W.) ya kasance da wani maƙwabci Bayahude.Wanda ya riƙa watso wa Manzon Allah (S.A.W) shara a gida.Duk da haka Manzon Allah bai ce masa komai ba.Aka kwana biyu,Manzon Allah bai ga an zuba shara ba.Don haka sai Manzo ya  tambaya, shin ina Bayahudan nan? Sahabbai suka ce: “ba shi da lafiya”, sai Manzo yace mu tafi mu gaishe shi”.

Waɗannan suna iya zama madogara dangane da yadda Addinin Musulunci ya ƙarfafa sha’anin maƙwabtaka a tsakanin al’umma. Addini da ma ya iske Hausawa na da al’adar zumunci a tsakanin maƙwabta.To sai dai ya faɗaɗa matsayinta, kamar yadda aka samu wasu bayanai masu yawan gaske. A  inda Annabi Muhammadu (S.A.W) ya nuna mana cewa:

Maƙwabtaka kan fara ne daga gida ɗaya, zuwa gida arba’in hannun hagu, haka kuma gida da zuwa arba’in hannun dama.Haka kuma gaba ko baya su ma daga gida ɗaya zuwa arba'in. Wannan ya ƙara ba Bahaushe ƙarin ƙarfin gwiwa,wanda ya haifar da kyakkyawar zumunci a al’ummansa.

ZUMUNCIN ABOTA

Zumunci da abota kan ƙulla kan faru ne, saboda wasu dalilai masu tarin yawa da suka shafi rayuwa ta yau da kullum. Wannan zumunci kan iya ƙulluwa a tsakanin jinsi ɗaya ko wani jinsi, da wani, ko tsakanin tsara da tsara, ko tsakanin babba da yaro da dai sauransu.

Bisa ga dalilan da kan sa  abota ta ɗore shi ne, dacewar abokan. Musamman in aka yi sa’a ra’ayinsu ya zo ɗaya, ko kuma ɗaya ya fi ɗaya haƙuri . Akan samu abokai na jinsi ɗaya, misali kamar aboki da aboki, wato duk maza ne, ko ƙawa da ƙawa,mata.

Dangane da yadda abota kan ƙullu ta yi ƙarfi har ta haifar da zumunci a tsakanin mutane.Ba ya rasa nasaba da irin asalin abin da ya yi sanadin haɗuwar su.Tare da kuma irin mahimmancin da suka bai wa Al’amarin. Misali kamar waɗanda suka haɗu a makaranta, ko kasuwa, ko wurin ibada, ko wurin wani taro na musamman da Sauransu. Abota kan ƙullu a tsakanin ɗalibai ko almajirai, ko ƴan makaranta da suke karatu tare.Tabbas makarantar na iya kasancewa ta Arabiyya, wato ta allo ko kuma makarantar tsangaya.

A inda za a iske an haɗa wa Malami yara, a wani lokaci na gari ɗaya, ko na garuruwa daban- daban, duk suna harka tare. A samakon haka abota kan ƙullu. Da yake yanzu zamani ya zo da wani  sauyi, akan samu makarantun Islamiyya.Inda za a samu an haɗa yara maza da mata a aji ɗaya, amma ba Ƙur’ani kaɗai ake koya masu ba har da sauran ilimin addinin.

Akwai kuma makarantar ilimi na littattafai (zawiyya),a inda nan za a iske manyan mutane suke ɗaukar karatu a wurin wani malami.Wanda yake ya sha bamban da na makarantar yara, wato da ta allo da kuma ta Islamiyya.

Haka shi ma ilmin boko yakan zama mafarin ƙulluwar abota a tsakanin mutane da al’ummar Hausawa a matakai daban- daban. Kamar a makarantun firamare, da na gaba da firamare, da kuma manya-manyan makarantu.

Da farko dai, akan kai yaro ko yarinya makaranta elemantare, ko firamare, sannan kuma ya wuce makarantar sakandare ko ta horan malamai. A makarantar firamare da na gaba da firamare. Duk yaron ko yarinyar da suka haɗa aji za a ga ana samun kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu wadda kan haifar da zumunci zuwa gaba. Haka ma waɗanda ba su haɗa aji ba, in dai sun yi makaranta ɗaya, irin wannan zumunci kan ƙullu. A manyan makarantun ilimi ma kamar jami’o’i, zama tare ko gudanar da wasu (abubuwa) al’amura kan sa a ƙulla abota wanda kan haifar da zumunci mai ɗorewa.Wato bayan an gama makaranta har ya zuwa ga Ƴaƴa da jikoki.A inda za a iske ana kafa ƙungiyoyin tsofaffin xalibai.

Haka ma harkar kasuwanci kan sa a ƙulla dangantaka wanda kan haifar da zumunci. Haɗuwa a wurin cin kasuwa da irin ragowar da akan samu a wurin saye da sayarwa, tsakanin mutane da dai sauransu.Wannan shi ma kan sa a saba, da kuma yarda da juna a zama abokai.Ta fuskar kasuwa kuma da  sauran lamura, wato zumunci yana  ɗorewa. Hasali ma dai, a al’ummar Hausawa mutanen da suke sana’a ko kasuwanci iri ɗaya sukan zama kamar tsintsiya. Bisa ga wata abotar da ta kan ƙullu ta sanadiyyar haɗuwa a wuraren ibada, nan ma za mu iya cewa ba ƙaramar rawa su ke takawa ba kamar masallaci, aikin hajji da umra ko jana’iza da sauransu. Wato wasu harkar da addini kan sa a shaƙu a zama abokai har zumunci ya shigo a zama kamar uwa ɗaya uba ɗaya. A wata fuskar kuma, akan samu ƙulluwar abota a sakamakon haɗuwa a wasu wuraren tarurruka na rayuwa. Kamar wasan al’adun gargajiya, kamar  wasannin dambe,ko kokuwa, kalankuwa, ko irin na taron siyasa da dai sauran makamantasu.

Waxannan kan taimaka ainun dangane da ƙulla abota a tsakanin mutane a cikin alumma.A  inda wannan abota kan ɗore har ga ƴaƴa da jikoki, ta fuskar ziyartar juna, ko musayar kyaututtuka a tsakaninsu, ko halartar duk wani lamari da ya shafi aboki.

Dangantakar abota dai a al’umar Hausawa abu ne da kan ƙulla kyakkyawan zumunci a tsakanin mutane.A wanda wani lokaci ma yakan fi zumuncin jini danƙo. Idan irin wannan zumunci ya yi kyau, aboki kan iya ɗaukar ɗawainiyar iyalan aboki.Musamman idan ba ya da rai, ko wata rashin lafiya ta kama shi, ko idan ya yi tafiya. Haka kuma aboki kan iya zama uban auren ƴaƴa abokinsa. Wato ya ba da su ga wanda yake so, ya kuma yi masu duk wasu ɗawainiya fiye ma da yadda zai yi ma ƴaƴan sa.

ALMAJIRCI  KO ƊALIBTA

Almajirci  ko ɗalibta abu ne da kan haifar da dangantaka kyakkyawa,a tsakanin mutane, wanda daga ƙarshe zumunci kan ƙullu. Dangantakar kan ƙullu ne ta fuskoki da yawa kamar tsakanin malamai da Almajiri ko tsakanin  almajri ko  xalibi da xan’uwansa ko kuma a tsakanin almajiri ɗalibi da jama’ar  gari.

Dangane da yadda, almajirci na fannin ilimin addini ke ƙulla zumunci a tsakanin malamai da almajiri. shi ne, kamar inda za a tarar malami ya zama kamar uba ga almajirin.Balle ma a ce sun tafi zuwa wani gari wanda ba garinsu ba. To a nan ban da karantar da shi da malami ya ke yi, to kuma shi ne, matsayin ubansa. Wannan dangantaka ta kan ɗore ko bayan almajirin ya sauke Alkur’ani ya koma gida, sai a samu ya na ziyartar malami. Bayan wannan kuma akan samu dangantaka a tsakanin malamai da iyayen almajiri.Iyayen kan girmama malami ne, saboda baiwar da Allah ya ba shi ta ilimi, da kuma karantar da Ɗansu da ya yi wanda a sakamakon haka za su amfana duniya da lahira. Irin wannan dangantaka ta girmamawa kan haifar da zumunci, a inda za a iske har ziyarar juna ake yi da halartar shagulgulan da suka shafi juna.

Haka kuma akwai wani zumunci da ke ƙjulluwa a tsakanin  alamajirai.  A duk inda a ka ce almajirai suna zaune dole ne a samu kusantar juna tsakanin mutum biyu ko fiye. Idan an tafi yawon bara akan tafi tare, duk abin da aka samu a ci tare irin wannan dangantarkar kan ɗore har zuwa girma ya haifar da zumunci.

A sakamakon barin gida a shiga duniya neman ilim, almajiri kan ce “ a rashin uwa akan yi uwar ɗaki” Domin ya ɗebe wannan kewar almajirin kan samu wata mata a cikin gari wadda zai rinƙa kai mata wasu ƴan koke-koke, tana share masa hawaye, ko kuma ya rinƙa kai mata tarin kuɗi ko ajiyar wani kayansa na musamman.

Akan kira wannan mata da sunan uwar ɗaki ko kuma in namiji ne, sai a ce masa ubangida. Samun uwar ɗaki ko uban gida yakan faru ne a wani lokaci da aka fara zuwa bara, ko aike, ko kuma ta fara yin rubutun sha, wato almajirin kan yo wa matar da yake so ta zama uwar ɗakinsa rubutun sha, musamman lokacin zumi,ko wata larura in taso. Wanda idan ya tashi tafiya gida, ita kuma sai ta yi masa hasafi na abin da ya sauƙaƙa tare da godiya.

Ta fannin maza kuwa wato uban gida shi an fi samun mai yi masa wata hidimar yau da kullum, kamar cefane da wanki ko share-share. A wani lokacin akan yi sa’a wani ubangida ya riƙe almajiri har girmansa wani ma har yakan yi masa aure. Wato ya yi masa duk abin da zai yi wa ɗan cikinsa. Irin wannan zumunci yakan yi naso har ya kai ga iyayen Almajiri. A inda sukan girmama shi, kuma ya mutuntasu, saboda ƙarfin halin da suka nuna na barin ɗansu ya yi masa barantaka.

Bisa ga yadda ɗalibta ta ɓangaren ilimi zamani ko na boko, ke ƙulla zumunci shi ne, inda za a samu zumunci tsakanin ɗalibi da malaminsa. Nan ma akan gudanar da zumunci kamar yadda yake tsakanin ɗa da uba. Don kuwa baya ga koyar da shi da malami ke yi, yakan ba shi wasu shawarwari da za su taimakeshi a harkokin rayuwarsa ko da bayan ya gama karatu.

Da yake ɗalibta suna suka tara, za mu iya kasa ta kashi uku dangane  da  mastayin ko mataki. Misali akwai ɗalibta  da akan fara a makarantun firamare, wato tun ana ƙanana. A nan malami shi ne, zai lura da yaro kamar mai raino wato kamar uwa,don kuma shi zai nuna masa  cewar ya yi wannan, ya bar wannan. A irin wannan makarantar, malamai kan ɗauki yara kamar ƴaƴansu, su koya masu yadda ake tarbiya, da tsabta da sauransu.Wannan kan sa dangantaka  ta ɗore tsakanin malamai da ɗalibi, musamman idan jininsu ya  haɗu.

Daga wannan kuma sai mataki na biyu na ɗalibtar da yaro kan yi a lokacin da yake makarantar gaba da firamare ko kwalejin. A irin wannan muhalli dangantaka kan iya zuwa ne ta fuska biyu. Da yake yaro ya fara sanin ciwon kansa.Yakan sami ƙulla dangantaka  da yaran ajinsu,ko ƴan ɗakinsu kwanansu.Haka kuma akan samu ubangida  wanda ya fi shi daɗewa  a makarantar.

Irin wannan ubangida kan rinqa kulawa  da shi da al’amarin yaron. Irin wannan  dangantaka  kan ɗore ya haifar da zumunci, ko da bayan an bar makaranta.

Bayan wannan sai kuma mataki na ƙarshe,wato ɗalibtar da mutum kanyi a manya-manyan makarantu, ko  jami’o’i. A lokacin da ya zama mutum cikakke, wato ya riga ya mallaki hankalinsa ba dole ne malami ya wahalar da kansa  wajen horar dashi ba, sai dai jawo hankali da shawarwari. A irin wannan mataki  ma akan samu kyakkyawar dangantaka tsakanin  ɗalibai da  suka zo daga wurare daban-daban,wanda kan sa zumunci. Ta fuska ta biyu kuma ita ce zumuntar da  kan ƙullu a tsakanin xalibi da Malamai. A samakon irin ƙauna da kuma horon da malami ya yi ma ɗalibi,da kansa yakan ƙi mantawa da shi, idan sun zama  wani abu. Ɗalibi kan kyautata ma malamai kamar yadda zai kyautawa iyayensa.

BARANTAKA (UBANGIDA DA BARANSA)

Barantaka a al’umar Hausawa yana nufin ajiye wani mutum, ya rinƙa kula da gudanar da wasu lamura na rayuwa. Ko dai a biya shi a ƙa’idance, ko kuma ya dogara ga duk abin da Allah ya ciyar da shi daga ubangidansa.

Ubangida kan ɗora wa baransa hidimar cefenen gidansa, ko kulawa da wurin kasuwancinsa, ko wasu dabbobi da yake kiwo, da sauransu. A al’umar Hausawa an fi samun barantaka ne a tsakanin masu mulki da talakawa, ko tsakanin masu hali da talakawa. Hanyoyin da dangantakar barantakar ke ƙulla zumunci a al’ummar Hausawa na da yawa.

Domin a mafi yawan lokuta in dai har mai gida na kyautata wa barorinsa, sai a samu dangantakarsu ta zama kamar ta xa da mahaifi. Akan samu inda ubangida ke yi wa Baransa aure ya ba shi gida ko gona. Kai abin har yakan zama kamar wani ɗan uwa ne na jini. A wasu wuraren, bara yana ƙulla zumunci da ƴan uwan ubangidansa, kai ka ce shi ma ɗan uwa ne na tsatso.

Idan dangantkar bara da ubangida ta yi ƙarfi, to sai a tarar ana yin zumunci a tsakanin dangin bara da dangin ubangida. Wannan kuwa yakan haɗa da ziyartar juna, da halartar wasu bukukuwa ko dai wasu lamura da suka shafi juna musamman in baran daga karkara yake.

Haka idan dangantaka  ta yi ƙarfi tsakanin bara da ubangidansa kusanci da yarda kan fi na tsakanin ɗa da mahaifi. Ubangida kan sanar da baransa wasu daga cikin sirrorinsa wanda ɗan cikinsa ma ba ya tava sani.

Barantaka a al’ummar Hausawa suna ta tara. Akan samu barorin da ke gidan sarakuna waɗanda sukan sha bamban da na gidan masu kuɗi.

Barorin sarakuna waɗanda akan ɗauka a matsayin fadawa, ko kuma na jikin fada, ciyar da su, da shayarwa, da tufatarwa, da aure, da muhalli duk suna wajen basaraken da suke ƙarƙashinsa ne. Game da barorin da suke ƙarƙashin mai kuɗi kuwa al’amarinsu ya saɓa da na sarakuna, saboda suna yin aiki ne da nufin a biya su.

Ko da ma kuwa ciyarwa, da shayarwa, ko muhalli bai zama dole ba, sai dai don kyautatawa balle kuma a ce a yi masu aure. Ko da ya ke akan samu a wasu wurare ana yin haka, amma ba dai kamar irin na Sarakuna ba.

Barantaka a wannan zamani ya bambanta da na zamanin da.

Ana samun wasu ‘yan bambance -bambancen ne, kuma a sakamakon ci-gaban zamani da aka samu, wanda suka haɗa da samuwar ilmin boko, da aikin gwamnati, da na kamfanoni, da kasuwanci, da sufuri, da aikin jinga da dai Sauransu. Dangane da yadda samuwar ilmin boko ya yi tasiri akan dangatakar barantaka shi ne kasancewar ilmin boko ne ya zo da aikin  ofis, ko mu ce na gwamnati da na kamfanoni da kuma leburanci.

A sakamakon haka ne aka samu sauyi a cikin tsarin barantaka. Aikin gwamnati ya tanadar wa manƴan manƴan ma’aikata barori, waɗanda za su dinga yi masu hidima. Kamar masinja, da direba, kuku wato mai dafa abinci da boyi-boyi wato Mai aikace-aikacen gida kamar shara da wanki da sauransu. Idan aka yi sa’a wannan dangantakar ta yi kyau yakan sa a samu ƙulluwar zumunci. Bara sai ya zama tankar ɗan ‘uwa na jini. A wasu lokutan ma, ko da ubangidan ya bar aiki, dangantakar kan ɗore.

A  zamanin da an fi samun maza majiya ƙarfi a harkar barantaka, don kuwa mafi yawa aikin ƙarfi ake yi kamar noma,da huɗa, ko  aikin gini, ko faskare da ɗiban ruwa da dai sauransu. To sai a yanzu aka samu ayyuka kamar raino, ko girki, ko wanke-wanke ko kuma cefane da dai sauran ayyuka waɗanda a da ba a ɗaukar barori masu yi.

Wannan rayuwa da harkar barantaka ta samu ne saboda sauyawar zamani. Irin wannan dangantaka kan ƙulla zumunci musamman da yake yanzu ya shafi mata waɗanda a al’ummar Hausawa ana iya kiransu iyayen zumunci. Ta fuskar sufuri ma a yanzu an samu wani tsari na barantaka. Ana iya kiran direba bara ga mai mota, musamman saboda danƙa masa mota da aka yi, don ya ci abinci. Shi kuma direba yakan samu yaran mota ko mai gyaran mota wanda yake kamar bara ne a gare shi (direba). Shi kuma saboda koya masa mota da yake yi wanda ake sa ran nan zuwa gaba ya zamar masa sana’a. To duk waɗannan mu’amuloli idan suka yi kyau, zumunci kan shiga a kuma zama kamar uwa ɗaya uba ɗaya.

ZUMUNCIN ADDINI

Idan aka ce zumuncin addini ana nufin irin kyakkyawar dangantakar da harkokin addinin suka ƙulla tsakanin mutane. Da yake a baya mun ce Bahaushe ya fara ƙulla zumunci ne tun kafin zuwan addinin musulunci.

To kamata ya yi mu waiwaya baya mu ga yadda lamuran addinin gargajiya na Bahaushe ya samar masa da zumunci, sannan mu dubi yadda abin ya inganta bayan zuwan addini na musulunci. Masana tarihi sun nuna cewa al’ummar Hausawa a wancan lokacin suna da addinin da yawa. Da suke gani sun dace da yanayin rayuwar su, kuma kowane yana gani akwai abin bautawa kuma yake ba da ummarni ko hani. Haka kuma akwai shugabanin masu jagorancin wannan addini na gargajiya ko bauta. Misali a  Kano suna da tsumburbura da a ƙarƙashin jagorancin Barbushe a kan Dala da Gwaron Dutse,da Sarki maciji a Daura, da Madara a Kufena a Zariya, da magiro a kan dutsen Kwatarkwashi a Zamfara da sauransu.

Da yake shi ma bori wani nau’i ne na addnin gargajiya al’ummar Hausawa, akan keɓe wasu lokuta na musammana waɗanda ake gudanar da waɗansu shagulgula na bori kamar girka ko raƙon wata, ko cire kurwa(inuwa) da sauransu.

Dangane da yadda addinin gargajiya ko bori ya haɗa kan waɗanda suka yi imani da shi ko kuwa mu ce mabiyansa ba ƙaramar rawa ya taka ba. Musamman in mu ka yi nazarin yadda rayuwar Bahaushe ta kasance, saboda ko ba komai addinan sun haɗa dangantaka ta ƙut da ƙut. Za a samu ko da ba zuriyar mutum ba ne, in har a ka ce ga wani abu ya faru in dai har sun yi tarayya a abin imani ɗaya wato sun yarda da wani aljani, ko wani abin bauta, sai ka iske irin zumuncin da suke yi, kai ka ce ƴan uwa ne na jini. Domin babu mai son abin da zai ɓata wa wani rai, sai dai dole.

Zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa ya taka muhimminyar rawa wajen sauya rayuwar Bahaushe musamman da yake Musulunci addini ne da ya shafi rayuwa gaba ɗaya. Bahaushe ya rungumi Musulunci kai tsaye, ya yi kuma watsi da sauran al’adunsa da addinansa na gargajiya.

Daga cikin koyarwar addinin musulunci wanda Bahaushe ya runguma har da zumunci. Wannan bai rasa nasaba da horan da Allah ya yi a cikin Alkur’an mai girma inda yake cewa: a suratul Nahal Ayata : 90

                 

  “ Lalle Allah Ya na ummarni da kyautatawa da Adalci

     ku ba ma’abota zumunta haƙƙinsu kuma ya yi hani

     al fasha da mummunan aiki………….”

Suratul Furƙan Ayata 54

           

      “ Shi ne (Allah) wanda ya halice ku daga ruwa kuma

        ya sanya dangantaka da surukuta Allah Ya kasance                Ubangijinka mai iko……..”

Haka shi ma Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa a cikin “ Buguyatul Musulmi

Ba zai shiga Aljanna ba” wanda ya yanke zumunci”

“Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira to ya              kyautatawa  ma’abota zumunci (ƴan uwansa)”

Bisa ga waɗannan dalilai da kuma wasu da yawa waɗanda ba a bayyana su ba, kasancewar Bahaushe Musulmi sai ya inganta lamarin zumunci a rayuwarsa fiye da yadda abin yake a lokacin maguzanci.

A  koyarwar  addinin musullunci ,Allah (S.W.T) Ya  umarci waɗanda suka yi imani da su so ƴan uwansu, su tausaya wa marasa hali, masu rauni, da marayu da dai duk wani wanda wata hulɗa ta rayuwa ta haɗa su.

Kamar a aya ta 36 suratul Nisa’i.

     

“Kuma ku bauta wa Allah kuma ka da ku haɗawani da shi  kuma ga mahaifa ku yi kyautatawa, kuma ga ma’ abota zumunta da marayu da matalauta da maƙwabci

ma’abucin kusanta, da maƙwabci manisanci, da aboki

a gefe da xan hanya da abin da hannuwanku na dama suka mallaka. lalle ne Allah ba ya son wanda ya kasance mai takama, mai yawan alfari.”

Baya ga ƙulla zumunci da Bahaushe ke yi, ta yin la’akari da horon da Allah (SWT) a cikin Alƙur’ani mai girma da koyarwar Annabinsa Muhammmad (S.A.W). Akwai wasu lamura na addini da ke ƙulla zumunci a al’ummar ta Hausawa.

Misali haɗuwa a koyaushe a masallaci unguwa, ko na juma’a, ko a masallacin idi, lokacin sallah ƙarama da babba kan ƙulla dangantaka wanda ke iya haifar da zumunci tsakanin mutane. Haka kuma haɗuwa a taron ɗaurin aure, ko zanen suna, ko jana’iza, nan ma ana iya ƙulla dangantaka wadda kan iya ginuwa har ya haifar da zumunci. A sakamakon bambanci ko saɓanin fahintar addini, ya haifar da kafuwar ƙungiyoyin addini. A inda aka sami fahintar juna a tsakanin mutane wanda ya haifar da wasu mutane suka shiga wasu ɗariƙu, kamar ƙadiriyya ko Tijjaniyya da Sauransu. Wannan ya sanya duk waɗanda suka yi tarayya a rukuni ɗaya suna gudanar da zumunci a tsakaninsu. Idan abin farin cikin ya tashi mabiyan wannan ɗarikar duk za a taru a taya shi murna. Haka idan kuma abin baƙin ciki ne za a taru a taya shi baƙin ciki, a ba shi haƙuri daga nan zumunci ya ƙullu.

Baya ga waɗannan kuma, a yanzu ana samun wasu ƙungiyoyi na addini kamar ƙungiyar jama’atul Nasarul Islam, ko Fitiyanul Islam, ko Jama’atu Izalatul Bid’a Wa’iqamatus Sunna, ko Jundullahi da dai sauransu. Waɗannan ƙungiyoyi su ne da hanyoyi da dama ta nuna zumunci kamar taron yin wa’azi da kuma wurin wasu ibadu, taimakon al’ummar ta yin wasu ayyukan ci gaban al’umma.

Kamar dai kowane addinin shi ma addinin kirista ya ƙulla zumunci ga Hausawa mabiyansa ta fuskoki da yawa kamar wajen zuwa majami’a (coci) domin sujadar safe, ko ta yamma ko sujadar mako, ko kuma wajen bikin kirsimati da ista monde da dai sauran al’amuran addinin. A taqaice  dai muna iya cewa Bahaushe mutum ne da ya taso  tun fil’azal da zumuncinsa, wato tun lokacin addinin gargarjiya. To bayan zuwan addinin Musulunci sai abin ya ƙara ƙarfafa da yake daman zumunci na ɗaya daga cikin koyarwa addinin.

Tasirin zumunci a al’ummar ta Hausawa ya kai har ana ba shi muhimmanci fiye da wasu al’amura da addinin ya wajabta. Wato dai zumunci a wurin Bahaushe kamar tsoka ne da jini wanda kuma aka samu ba ya gudanar da zumunci, to akan ɗauke shi fanɗararre, jama’a su rinƙ ƙyamarsa.

MU'AMALA

ZUMUNCI SANA’A

Zumuncin sana’a kan ƙullu ko faru ne ta sakamakon tarayya a sana’a iri ɗaya, sau da yawa akan samu mutane masu sana’a ɗaya, suna gudanar da harkokin rayuwa ta yau da kullum wadda kan haɗ ziyarar juna.

Hasali ma dai, a al’adar Bahaushe, masu sana’a iri ɗaya sukan zauna a wuri ɗaya  a gari, ko a kasuwa. Misali a garuruwan ƙasar Hausa akan samu unguwa mahauta,ko unguwar maƙera,ko Soron ɗinki,ko unguwar masaƙa, ko marina,da unguwar majema da sauransu. Baya ga zumuncin maƙwabtaka da zai shiga tsakaninsu. Akan samu zumunci na auratayya saboda suna sana’a ɗaya, kuma suna zaune wurin ɗaya.

Zumunci sana’a kan haifar da ziyarar juna tsakanin masu sana’a iri ɗaya. Kamar misali idan an yi wa wani haihuwa ko bikin aure ko rasuwa da dai sauran harkokin rayuwa. A yanzu zamani ya kawo ci gaba ta fuskar kafa ƙungiyoyi na sana’a iri – irin kamar ƙungiyar mahauta da ƙungiyar maƙera da ƙungiyar manoma har da ƙungiyar makaɗa da mawaƙa.

Hulɗar da kan wakana tsakanin masu gudanar da sana’o’i  iri ɗaya, da kuma ƴan ƙungiyar masu sana’a ɗaya kan yi. Yakan haifar da zumunci da taimakon juna a tsakaninsu. A wasu ƙungiyoyin akan samu wani asusu da akan Buɗe, a inda akan ɗora wa kowa haraji daidai ƙarfina. A irin wannan kuɗi ne ake taimaka wa ƴan uwa, idan sun shiga wata matsala ko wani sha’ani ya same su. Kafa irin wannan ƙungiyoyi ba ya kan tsaya ne a gari ɗaya kawai ba. Har akan samu rassan ƙungiyar a ko’ina da cibiyar a wuri ɗaya.

Wato ke nan zumunci na iya naso har tsakanin gari da gari ko ƙasa da ƙasa. Domin mahimmancin zumuncin sana’a da ƙara masa danƙo da armashi a al’ummar Hausawa.  An samar da wasanni na raha a  da barkwanci tsakanin wasu masu sana’a daban daban.

Wannan kuwa akan yi shi ne don samun nishaɗi da annashuwa. Sannan kuma akwai adana al’ada da riƙon zumunci. Wannan wasa kan faru ne, ko dai don a nuna fifikon wasu masu sana’ar kan wasu masu wata sana’a ta daban. Ko kuma don a nuna irin matsayinta ga rayuwar al’umma gaba xaya. Misalin wannan kamar maƙera da Buzaye, ko mahauta da masunta (masu kamun kifi),ko mahauta da majema, ko marina da masaƙa da sauransu.

Wani zumunci da sana’a ke ƙullawa shi ne ta wajan cinikayya tsakanin mai saye da mai sayarwa. Bisa kuma ga ragowa da ake samu a tsakanin kan sa a ji ana cewa wane abokina ne. Shi ma a kan samu wani zumunci mai ƙarfi da ke ta ƙulluwa. A inda har akan lamunci juna abin har takan kai ga ziyartar juna da halartar wata hidima in ta samu da dai sauransu.

Zumuncin sana’a kan taimaka wa mutum a lokacin da ya shiga wani hali. Misali kamar in ya sauka a wani gari a matsayin baƙo, Ko kuwa a ce bai san kowa ba. Da yake sana’a abu ne da Bahaushe ya ba mahimmnaci don neman abin da zai gudanar da rayuwa cikin jin daɗi. To sai ya zama wajibi ga Bahaushe ya sa wannan lamarin na zumunci a harkar sana’arsa yadda har ba a iya bambance zumunci na jini da wadda sana’a ta haxa.

ZUMUNCIN TAFIYA

Tafiya na nufin mutum ya tashi daga wani wuri zuwa wani wuri, don gudanar da wasu lamura na rayuwa. Tun a zamanin da, har zuwa yanzu ba ma a ƙasar Hausa kaƙai ba. Tafiya kan haɗa mutane daban- daban a kan hanyarsu ta zuwa wani wuri wadda kan haɗa wata dangantaka a kan hanya ya zama zumunci. Ko da bayan an isa wurin da za ayi, zumunci yakan  yi naso har Ƴaƴa da jikoki.

A zamani da, wato kafin samun abubawan hawa kamar mota da babur,da keke da sauransu. Idan za a yi tafiya musamman na kasuwanci akan yi ƙungiya-ƙungiya da akan kira ayari. A wasu lokuta sai a tarar sun fito gari ɗaya a wani lokacin kuma sai dai su haɗu kawai saboda wasu dalilai. Ayarin fatake masu fatauci daga wannan gari zuwa wancan sukan samu shugaba da ake kiransa Madugu. Shi wannan mutum shi ne, mai faɗa a ji, ya ba da umarni na yi ko hani. Wannan ayari kan ƙunshi jama’a maza da mata da dabbobi kamar jakuna, da dawaki, da raƙuma.

A wani lokaci kuma akan samu shanu da akan yi takarkari da wasu daga cikinsu, don a ɗora masu kaya. Sannan in akwai wani yaro, ko mai larura to sai ya hau ɗaya daga cikin takarkarin. Su kuma sauran ƴan ayarin  duk da ƙafa ake tafiya, sai in an samu wani wuri a yi zango, in an ga dare ya yi. Irin wannan tafiya kan sa ƙulla kyakkyawar dangantaka tsakanin matafiya wanda kan iya samar da zumunci na mu’amulla da na auratayya  a tsakaninsu.

Baya  ga wannan kuma tafiya kan ƙulla zumunci ta fuskar ibada kamar zuwa aikin hajji a ƙasar  Makka. Inda za a samu matafiya sun zama kamar ƴan uwa ɗaya, uba ɗaya, ba  a da ba, lokaci da ake tafiya a ƙasa har ma a wannan zamani. A sakamakon tafiya aikin hajji, Hausawa kan ƙulla dangantaka da waɗanda suka yi tafiya tare. A  inda zumunci kan ɗore ko bayan an dawo gida.

Zumuncin da tafiya ke ƙulluwa a al’ummar Hausawa ya ci gaba da ƙarfafa. Bayan shigowar hanyoyin sufurin na zamani,kamar motoci, da jirage da dai sauransu. Da zarar Bahaushe ya haɗu da wani a cikin mota akan hanyarsu ta zuwa wani gari. Wasu daga hira dangataka za ta fara ginuwa har ya kai ga an yi wa juna tayin wani abinci. Daga nan sai tambayar wurin zama,da kaɗan-kaɗan za a yi ta ziyartar juna har zumunci ya ƙullu.

ZUMUNCIN RA’AYI

RA’AYI

Ra’ayi na iya ɗaukar ma’anar fahimta, da amincewa, da kuma karkata rai(zuciya) ga wani lamari na rayuwar duniya. Wato bukata,ko tunani bisa al’amuran rayuwa, shi ake kira ra’ayi a taƙaice karkata ko tarayya akan ra’ayi ɗaya  da mutane daban-daban kan sa a samu kyakkyawar dangataka a tsakanin mutane wanda kan haifar da zumunci.

Wannan  zumuncin ci gaban  zamani ya zo mana da shi.To amma da yake ya iske Malam Bahaushe da ma yana da zumunci, sai aka dace. Akan samu jituwar ra’ayi a kulob-kulob, ko ƙungiyar masu sauraran rediyo da karanta jaridu, ko ƙungiyar zaɓi- sonka da dai sauransu.

A sakamakon haɗuwar kai, ko dacewar ra’ayi, akan  samu mutune daga wurare daban-daban ko asali daban-daban.Ra’ayin siyasa ya haɗasu, kai ka ce ƴan ‘uwa ne na jini. Irin wannan zumunci kan kai har ga Ƴaƴa da jikoki. Misali a siyasar jamhuriya ta ɗaya ƴan Nepu kan sami kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu.

Wanda ya haifar da zumunci a al’umar Hausawa har kawo wa yau. Haka su ma ƴan jam’iyyar N.P.C. da Sauransu. To haka ma abin ya kasance a janhuriya ta biyu.Wannan shi ne ya yi naso zuwa zamaninmu  na yau. Baya ga wannan kuma dagantakar ƴan kulob-kulob a gari ko unguwa kan samar da zumunci. A inda akan ga sun haɗu kansu, don kawai su taimaka wa kansu da kansu. Wato haɗa kansu su gudanar da wasu aikace-aikace da ci gaban al’umma gaba ɗaya, ta hanyar amfani da ƙarfinsu ko kuma da aljihunsu. Wannan bai yiwuwa, sai ra’ayi ya zo ɗaya, sannan ake samun haɗin kai Wani ɓangaren da zumuncin ra’ayi ya ƙarfafa shi ne, wajen nuna ƙauna ga wani mutum. Ko da ba a taɓa ganin shi ido da ido ba. A wannan fuskar za mu iya kawo misalin ƙungiyoyin masu sauraron rediyo da kuma ƴan zaɓi sonka. Waɗanda za a iske mutum bai taɓa ganin mutum ba. To amma a sakamakon jin sunansa a rediyo, sai a ga abota ta ƙullu tun ana gaida juna ta gidajen Rediyo. Wata rana har sai ka ga an ziyarci juna.

Su ma ƙungiyoyi na taimakawa junansu kamar ta yin ajo, wato gudanmuwa. Idan wata hidima ta sameshi kamar haihuwa, ko aure, ko kuma in ya yi wata asara.

A ƙarshe dai zamu iya cewa lallai haɗuwar ra’ayi ba ƙaramar rawa yake takawa ba, wajen ƙulla zumunci.

Ko da yake zamani ya kawo wannan zumunci, to dama “iska ta iske kaba na rawa”.Wato zamani ya zo ya tarar da Bahaushe yana gudanar zumuncinsa.


MATSAYIN ZUMUNCI A DA DA YANZU

Idan  a ka yi nazarin yadda ake gudanar da lamarin zumunci, a al’umar Hausawa a da, da kuma yanzu. Za mu ga ba za su taɓa kwatantuwa ba. A kowacce al’umma yanayin rayuwa kan canza daga lokaci zuwa lokaci. Daga cikin abubuwan da kan canza rayuwa akwai tasirin baƙin  al’umma da al’adu, da kuma ci gaban  zamani. To sai dai a wasu lokutan ci gaban kan zo da wasu illoli, kamar yadda ya yi wa lamarin zumunci a al’ummarmu  a yau. A wannan mataki za a kwatanta matsayin zumunci a da, da kuma yanzu. Sannan kuma da dalilan da suka sa ya taɓarɓare ko matsalolin da yake fuskanta.

A zamanin da, al’adar Bahaushe ta shimfiɗa wasu abubuwa da suka ƙara ƙarfafa zumunci a cikin al’ummar. Tun kafin isowar addinin musulunci da kuma bayanarsa. A al’ada ta Bahaushe ya gaji wasu manyan  al’amura da ba za a iya mantawa da su ba, in dai har aka zo yin maganar zumunci. Waɗannan al’amura kuwa sun haɗa da rungumar juna tare da taimakon juna, da kunya, da girmama al’ada da dai sauransu.

Bahaushe ya gaji rungumar juna a al’adance, saboda tun ta hanyar nazarin yadda gidansa yake ya isa misali. Ta fuskar ƙaunar juna kuwa duk inda Bahaushe yake a da, za a same shi bai ƙaunar wani abu mara kyau, ko wata mumunar ƙaddara ta faɗa wa ɗan uwansa. In har ya same shi za a iske shi yana taya shi baƙin ciki.

Haka kuma in aka ce abin farin ciki ya samu ɗan uwan Bahaushe, a nan ma ba a barinsa a baya. Misali idan aka yi wa wani haihuwa, ko kuma a shagalin aure ƴan uwa za su tara masa gudunmuwa, na kuɗi, ko na hatsi, ko tufafi da sauran su. Idan abin ɓacin rai ya same shi, za a tarar duk ƴan ‘uwan su nuna damuwarsu, kamar wajen ciwo ko mutuwa, ko wata asara kamar gobara, ko sata da makamantansu. Kulawa da wannan kuwa shi ne babban sinadarin da ke  ƙulla zumunci fiye da komai.

Duk da yake cewa, har yanzu ana samun irin wannan kyakkyawar dangantaka a al’ummar Hausawa. To a gaskiya,yanzu abin ya yi rauni ƙwarai. Wato ba za a kwatanta shi da yadda zumunci ke gudana a tsakanin jama’a a yanzu ba. Ba abin mamaki ba ne ƴan uwa na jini su shekara ba tare da an sa juna a ido ba. Ko kuma ya rinƙa gudanar da harkokinsa daga shi sai matarsa da ƴaƴansa.

Al’ummar Hausawa na da al’adar kunƴa a zamanin da,kuma takan taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa zumunci. Idan muka lura a yau kunya  ta ɓace.

Bugu da ƙari, shi kansa Bahaushe ya yi watsi da wasu abubuwa, da ba su zama dole ba. Sannan kuma hatta yanayin hanyoyin gudanar da rayuwa sun sauya su. Domin a zamanin da Bahaushe yafi ƙarfin abinci,da  muhalli da sauransu. To amma, yanzu sai ga shi duk suna neman fin ƙarfinsu. A da Bahaushe kan mallaki abincin shekara da shekaru, saboda halin noma sannan kuma ga kiwo. Saɓanin yanzu harkar noman ta zama, sai mai hannu da shuni,wanda zai iya amsa kira in an yi.

Don haka ashe dole ne mutum ya rage wasu abubuwa, kuma ya shiga matse hannu, amma fa a dole don  ba yadda za’a yi. Ban da wannan kuma, ko da yanayin muhallin da Bahaushe ya gada, ya samu tasiri, saboda dai an san Bahaushe a gidansa ya kan mallaki ɗakin matarsa, ko matansa, da turaka, sai zaure a wani lokocin kuma da ɗakin baƙi. To amma yanzu abu ya shaddada ya kai lahaula wala ƙuwata, sai ka samu mutum daƙyar zai samu ya gina ɗaki ɗaya ma, balle har a yi ma maganar ɗakin baƙi.

MATSALOLIN ZUMUNCI A  YAU

Al’amarin zumunci yana fuskantar matsaloli da dama, a sakamakon faruwar sauye-sauyen da zamani ya kawo, a rayuwar Bahaushe ta yau da kullum. Bisa faruwar abubuwa, kamar cuɗanya da wasu ƙabilu. A inda aka samu shigowar baƙin al’adu, sannan kuma suka yi tasiri, Haka kuma zuwan ilmin boko shi ma ya yi tasiri ƙwarai a kan zumuncin Bahaushe. Don kuwa ya zo da wasu ɗabi’u, sannan ya kuma kawar da wasu ɗabi’u da a ka gada kaka da kakanni.Misali zaman gidan haya da wasu ƙabilu,sannan kuma ɗaki ɗaya ko ciki da falo.

Baya ga waɗannan kuma, sai wasu dalilai kuma da suka ƙara kawo matsaloli ga harkar zumunci, sun haɗa da yanayi tattalin arziki, ci gaban zamani, sannan kuma sai gurɓacewar hali da sauransu.

Zumunci ya fuskanci babbar matsala ta fuskar Hulɗar yau da kullum, musamman da aka durƙusar da jama’a da dama. Kamar lalacewar harkar nama,da kasuwanci, da kuma faɗuwar darajar naira. Wannan al’amari ya bugi kowa, don haka ne, sai ya sa kowa yana ta kansa. Kasancewar kowa a cikin irin wannan hali,na talauci, sai ya kawo wasu abubuwa sababbi waɗanda da ba a sansu ba. Kamar rowa,da ƙyamar haihuwa,da gudun dangi. Haka kuma ana iya cewa ya kori wasu abubuwa waɗanda da yake an san Bahaushe da su. Kamar taimakawa mabuƙata, da suka haɗa da ƴan ‘uwa ne, ko bare? da aka san Bahaushe da shi. To dalilin wannan durƙushewar da tattalin arziki ya yi, sai ya kawar da wannan. Don kuwa ya zama dole, saboda ya ya mutum ya iya da kansa? balle har ya ji da ɗaukar nauyin ɗan uwa?. Domin haka sai aka samu giɓi a tsakanin ƴan uwa, ko maƙwabta. Musamman masu hannu da shuni, wannan kuwa ya ƙara nesanta jama’a da dama da sauran ƴan uwa da abokan arziki.

Wanda babu shakka ya kawo lalacewar zumunci a wurare da yawa. Domin sau da yawa kyauta na ƙara qulla zumunci,rowa kuma na tsinka shi.  A halin da ake ciki a wannan zamani ba maƙwabci ba, kai ko da ɗan uwa ne,  ko kuma malami ne yanzu in ya hori yaro, sai ka ga an nuna ɓacin rai. Wai cewar ya tsargi yaron ko ya sa masa ido ne ,ba domin gyara halin yaron ne ya hore shi ba. Bayan haka kuma, sai wani dalilin kuma da ya kawo gurɓatar hali shi ne kuwa, rashin girmama na gaba. Wanda shi ma ya ƙara durƙusar da zumunci ƙwarai da gaske. Domin idan aka dubi baya a zamanin da, za mu ga cewar an san Bahaushe da girmama na gaba da shi.

Don ba a gida ɗaya ba, ko a unguwa ɗaya ake ,da zarar a ka ce ga wani babban wanda ake girmama shi. Haka kuma da zarar babba ya yi magana a kan wani abu zai yi a saɓa. Duk kuma abin da ya hukunta, ko mene ne ya zauna, babu mai tayarwa, saboda irin matsayin sa.

Bayan haka kuma, a da akan samu biyayya a tsakanin ƴan uwa kamar wa (yaya) ya na da iko a kan ƙaninsa. Ma’ana in ya yi hukunci ta zauna. Haka shi kuma ƙanin ba shi da ikon ya yi jayayya, don biyayya tare da girmamawa.

Haka kuma yake har akan Ƴaƴansu. Shi kuma wannan na da ikon yin hukunci da na ƴan uwa, babu wata fargaba,don ya san ya fi ƙarfin abin. Kai ko babu jinin dangantaka a tsakani, ko ta abota ta haɗa mutum da iyaye wani. To sai ka samu ana girmama, wannan mutum a matsayin uba. A wannan zamani abin ya zamanton saɓanin haka. Gurɓacewar halayen mutane, wanda ya sa suka yi watsi da waɗannan lamuran ya sa zumunci da aka sani a tsakanin Hausawa ya yi rauni. Kowa kansa ya sani, to amma sai  wasu na ganin cewa ci gaba ne.

GURƁACEWAR HALI

Zumunci ya samu nakasa ta dalilin gurɓatar hali da aka samu a cikin al’ummar Hausawa. Don kuwa a da an san Bahaushe da wasu halaye, kamar kunƴa, da girmama na gaba, da rungumar juna, ko ƙaunar juna, da ɗaukar ƙaddara da Sauransu. Bahaushe an san shi da kunƴa,(na nufin jin nauyi,tare da kamun kai), da kawaici, ko kara (kawar da kai,a kan wasu al’amura) waɗanda a yanzu  sun ɓace gaba ɗaya.

Wannan ɓacewa kuwa ya taimaka da gaske wajen gurɓatar halayen Bahaushe a yau. Don kuwa a zamanin da, sai ka iske mutum na da ikon ya yi hukunci akan ɗan wani. Ma’ana in ya ganshi ya na abin da ba daidai ba, sai ya hukuntashi ba tare da fargabar ko iyayen yaron zasu nuna ɓacin ransu ba.Ta dalilin wannan shi ya kawo kyautatuwar tarbiya a zamanin da, saboda an ɗauka ɗa na kowa ne; kuma haƙƙin kowa ne, ya kula da  ɗan wani kamar yadda zai kula da nasa.

Masu hikima na cewa, “ka ƙi naka duniya ta so shi, ka so naka duniya ta ƙi  shi” to wannan ya nuna a sarari irin yadda rayuwar Bahaushe take a da. A yanzu maganar kunya ko kawaici ko kara sun ɓace.

Sannan kuma son Ƴaƴa ya yi yawa, kowa ba ya son a taɓa ɗansa. Domin  kuwa, wani ko dai dai da tsawa in ka yi wa ɗansa, sai ya tuhumeka kan wane dalili ne za ka matsa wa yaronsa?. A wani lokaci ma in har ba’a yi sa’a ba, sai abin ya kai su ga tashin hankali, ko kuma wani lokaci har ya kai su zuwa ga hukuma, watan kamar ƴan sanda ko Alkali.

An nan an samu akasin ɗabi’un da a ka Bahaushe da su, don kuwa a zamani da ana kawar da kai a kan ɗa, amma yanzu kowa nasa ya sani. Ma’ana son Ƴaƴa shi ya sanya zumunci ya naƙasa. Saboda gaba ɗaya an saki layi sai bin son zuciya.

Gurɓacewa hali ya zama kamar ci gaban mai haƙar rijiya ne, don kuwa babu  inda za a in dai har  ana cikin wannan hali. Bugu da ƙari a zamanin da, an san Bahaushe da rungumar juna, ko kuma a ce ƙaunar ɗan uwansa. Don kuwa in aka ce ga abu ya samu ko ya faru ga ɗan uwa.To lallai su ma danginsa za su nuna damuwarsu, a kan wannan al’amari, saboda za su yi iyakar ƙoƙarinsu, sai sun ga inda ƙarfinsu ya ƙare.

Ko da yake yanzu abubuwa sun sauya, domin kuwa duk wanda ka samu zaka iske shi ma yana da al’amarin da ya dameshi. Da zarar garin Allah ya waye zaka samu kowa ya kama gabansa, sai ɗai ɗai ne, zaka ga wai suna lura ko biyawa ta kan ƴan uwa,sai dai kowa ya yi ta kansa. Wanda yake  wannan wata sabuwar rayuwa ce, kuma baquwa da Turawa suka kawo mana.

BAƘIN AL’ADU

Zumunci ya fuskanci matsaloli masu ɗimbin yawa a wannan zamani. musamman saboda cuɗanyar  al’ummar Hausawa da wasu ƙabilu, ya sa dalilin haka aka samu surkin al’adun Bahaushe da baƙin al’adu don haka ne sai aka samu tasirin baƙin al’adu akan al’adun Bahaushe kamar kunya, taimakon juna da tausayi da sauransu.

A inda ko dai suna gurɓata, ko kuma ma suka ɓace gaba ɗaya. Sai baƙin suka maye gurbin su. Bisa ga yadda aka san Bahaushe a al’adunsa akwai kunƴa wadda ita ce takan yi masa takunkumi  yin wasu abubuwa.

Wannan kuwa zai iya haɗawa da kawaici kan wasu abubuwa. Kamar yadda wata karin magana ta ce “Ɗa na barin halal don kunya” manufa shi ne ko da wannan abu haƙƙinka ne, to ka na iya kau da kai don kunƴa, zamu iya dangantashi da sha’ani  ƴaƴa.

Domin  a da ɗa dai na kowa ne, ko ɗan uwa ko amini, ko maƙwabci, ko malami. Kai, ko da ma wani Babba ne, a unguwa yana da ikon ya tsawatarwa yaro, kai har horo ma idan ta kama. Ban da yanzu, abin ba haka yake ba, saboda cuɗanya da wasu al’umma, sai aka samu akasi.

A yanzu duk wanda ya taɓa ɗan wani, to sai ka ji ana kai ruwa rana. A wani lokaci kuma har, sai kaga abu ya kai ga zuwa Alkali akan maganar Ƴaƴa, ko kuma kaga faɗan yara ya juye zuwa na Manƴa.

A zamanin da an san Bahaushe da rungumar juna wato taimakon ɗan uwa ta kowace fuska, a inda sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Sannan kuma wata karin magana mai nuna cewar “ Naka naka ne ko bai maka aiki komai,” sannan Bahaushe ya yarda da ra’ayin nan mai cewa  “namu ya samu sai ci”. Manufa shi ne, in Allah ya wadata ɗan uwa, to ɗan uwansa ya warke ke nan, saboda shi ne zai shaida. Malam Bahaushe ya kuma ƙara cewa “ai Babba juji ne” don haka dole ne ya ɗauki nauyin na ƙasa da shi. Sannan kuma wata karin magana mai cewa “kowa ya taimaki wani Allah na taimakonsa”

Yanzu zamani ya sauya gaba ɗaya, saboda haka Bahaushe ya tsinci kansa cikin wani hali na rashin sanin tabbas.

Bisa dalilin shigowar al’adar Malam Bature. Wanda shi a rayuwa irin tasa, bai yarda da tsari irin na Malam Bahaushe ba. Shi abin da ya fi amincewa shi ne, kowa tashi ta fissheshi, ko kuma muce daga ƙwauri sai gwiwa. A nan manufa shi ne daga shi sai ƴaƴansa da matarsa, a wani lokaci kuma da karensa. Shi bai yarda da ya ɗauki nauyin kowa ba, kai ko da mahaifansa in suka tsufa, sai ya kai su gidan gajiyayyu, sai dai ya rinƙa kai masu ziyara daga lokaci zuwa lokaci.

ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA

Wannan irin dogon zama da aka yi, na shekaru masu yawa. Shi ne  ya haifar da abubuwa da yawa  da suka yi tasiri a kan rayuwar Bahaushe gaba ɗaya. Shi wannan irin tasirin kuwa,  zamu iya karkasa shi zuwa kashi huɗu ko kuma su mutanen kamar haka:

Akwai mutanen da tasiri ya yi masu jirwaye suka yi dabbare- dabbare.

Akwai mutane da suka yi rabi  da rabi  kamar ragon uda, ko akuya mai gyauto(gefe rabi fari, rabi baƙi).

Akwai mutane da suka yi baƙi-baƙi.

Akwai mutanen da suka rikiɗe  gaba ɗaya  sun  yi  baƙiƙƙiirin. Sun ƙuna ba su gudun ƙauri. Kowane daga cikinsu ba ya rasa dalili da  ya sanya  shi  zama hakan;

1. Rukunin mutane na farko su basu yi boko  ba, amma sun fi ƴan bokon zaƙewa.

2. Rukunin mutane na biyu, ana iya samun ƴan boko   zalla watau waɗanda  suka yi karatun zamani kuma suka ɗauki ra’ayin  boko, amma kuma suna  gaurayawa da al’adunsu.

3. Rukunin na uku ,su ne boko sana’a, suna cin moriyar ta,  amma ba su dulmiya ba.

4. Rukunin mutane na huɗu su ake kira boko aƙida, kuma tunanin su yafi na Bature, tun da su rayuwarsu ta yi  ban –tafin- makafi  da

Manazarta

gyara sashe