Zamantakewa
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Zamantakewa Masana da dama sun bayyana ra'ayinsu dangane da ma'anar zamantakewa kamar haka: Dalijan B.M. a shekarar (2016), a wata makala da ya gabatar mai taken "Zamantakewar Hausa a jiya" ya bayyana ma'anar zamantakewa da "Asalin kalmar zamantakewa daga zama ne. wato abin da ake nufi anan shi ne zama tare ko dai ta fuskar zumunta ko makwabta ko sana'a ko wurin aiki ko kuma ta sauran hidimomin duniya da sauransu". Ya ci gaba da cewa: "Zamantakewa kuma na iya nufin halin zaman tare na al'ummar Hausawa".
Zamantakewa na nufin kamar yadda sunan ya nuna daga kalmar zama wato abin nufi a nan shi ne zaman tare, ya Allah ko dai ta fuskar zumunta ko makwabtaka, ko kuma ta fuskar yanayin sana'a, ko da yake ma'anar takan iya wuce wannan idan aka yi la'akari da ire-iren dangantakar da ake samu tsakanin al'umma, misali Zamantakewa tsakanin shugabanni da mabiyansu, malamai da kuma ɗalibansu, mata da mazajensu, iyaye da yaransu.
Ire-iren Zamantakewa
gyara sasheAkwai ire-iren Zamantakewa da dama a garin Mayanci, za mu yi bayani a kan wasu daga ciki.
- Zamantakewar Aure
- Zamantakewa Tsakanin Malami Da Ɗalibai
- Zamantakewar Zumunta
- Zamantakewar Makwabta
- Zamantakewa Tsakanin Shugabanni Da Talakawa.
Zamantakewar Aure
gyara sasheAure dai wata alaka ce halattacciya, wadda ta halatta zaman tare tsakanin ma'aurata guda biyu, wato miji da mata. Ana yinsa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali, da mutunci da kiyayewar uwaye. (Gusau, a shekara ta 2012).
A Zamantakewar aure, zama ne na taimakekeniya tsakanin mata da miji, ta hanyar da mata ke yi wa mijinta biyayya tare da tattala duk wani abu da ya kawo gida, haka ma takan kyautatawa iyayen mijinta da dukkan 'yan'uwansa, shi kuma mijin zai kiyaye dukkan Hakkokin matarsa tare da kyautata mata da iyayenta da kuma sauran danganta.
Wannan magurza ta yi tasiri kwarai da gaske dangane da Zamantakewa aure, domin kuwa bakin da suka shigo garin Mayanci ta sanadiyyar zuwan magurzar auduga sun yi ta yin auratayya tsakaninsu wanda sakamakon auratayyar nan ya zama dalilin yaduwar iyali tsakanin su har suka zama abu daya.
Zamantakewar Zumunta
gyara sasheZumunta ita ce a sami wata alaka ta jini a tsakanin 'yan'uwa. Wadannan 'yan'uwa su ne ake kira dangi a Bahaushiyar al'ada. Dangi kuwa su ne 'yan'uwa na kusa da na nesa. Bahaushe mutum ne mai son Zumunci, har ma a cikin karin magana yana cewa: "Zumunta a kafa take" wani lokaci kuma: "dan'uwa rabin jiki".
Magurzar auduga ta garin Mayanci ta yi tasiri kwarai da gaske bangaren Zumunci, domin kuwa bakin da suka shigo ci rani saboda zuwan wannan magurzar har suka gidandance a garin, mazauna garin na asali sun dauke su 'yan'uwan juna. Kenan wannan magurza ta yi tasiri kwarai da gaske bangaren Zumunci.
Zamantakewar Makwabta
gyara sasheMakwabtaka na nufin zama kusa a wajen muhalli na gida ko wajen sana'a ko kuma ta hanyar ma'aikata (Daliban,a shekara ta 2016).
Ya ci gaba da cewa: " Idan akwai zama mai kyau na makwabtaka, lalurar da ta shafi makwabcinka tamkar kai ta shafa. Hasali ma akwai karin maganar da ta ce: "Abin da ya taba hanci idanu ruwa suke yi". Sa'annan kuma an ce makwabcinka a lahira shi ke ba da sheda ga makwabcinsa.
Idan muka yi la'akari da irin wannan rayuwa ta makwabtaka, wannan magurza ta yi tasiri kwarai da gaske dan gane da makwabtaka, domin ta haifar da abubuwa masu kyau, kuma na alheri da kulla kyakkyawar dangantaka, kenan wannan magurza ta taka muhimmiyar rawa wajen Zamantakewar makwabtaka. Idan akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali da aminci tsakanin maƙwabta, kowane irin alheri yana samuwa ba a kan aikin gona kadai ba, har ma da dukkan sauran al'amurran rayuwar duniya.