Yosra Frawes, haifaffiyar Djedeida, lauyar kasuwanci ce 'yar Tunisiya, mai fafutukar kare hakkin dan adam kuma mai rajin kare hakkin mata.[1]

Yosra Frawes
President of Tunisian Association of Democratic Women (en) Fassara

ga Afirilu, 2018 - ga Yuni, 2021
Monia Ben Jemia (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Djedeida (en) Fassara, 20 century
ƙasa French protectorate of Tunisia (en) Fassara
Tunisiya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Neji Khachnaoui (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Lauya, gwagwarmaya da Mai kare hakkin mata
Yosra Frawes
Yosra Frawes Acikin Taro
yosra frawes

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

A kan yunƙurin malaminta na ilimin zaman jama'a, ta halarci muhawarar shekarar 1995 kan rawar da matan Tunisiya ke takawa a cikin shahararrun wasan kwaikwayo na soap operas Daga nan ta shiga ƙungiyar matasa ta Ƙungiyar Matan Dimokraɗiyya ta Tunisiya yayin da take kamfen a ƙungiyar ɗaliban Tunisiya. A shekara ta 2000, ta ƙaddamar da koke na neman daidaiton jinsi a cikin gado.[2]

Bayan juyin juya halin Tunusiya na shekarar 2011, Yosra ta shiga ƙungiyar masana shari'a waɗanda suka tabbatar da rubutun sauyin mulkin demokraɗiyya a cikin Babbar Hukuma don Gane Manufofin Juyin Juya Hali, Gyaran Siyasa da Canjin Demokraɗiyya. A halin yanzu, ta dukufa wajen yin tir da take hakkin dan Adam da rashin daidaito. Sannan ta yi aiki da wani kudiri na cin zarafin mata wanda majalisar wakilan jama’a ta amince da shi a watan Yulin 2017.[3]

Ta shahara da fafutukar kare hakin bil'adama ta shiga cikin sakin Jabeur Mejri, wanda ake zargi da kai hari ga ɗabi'a, batanci da kuma tada hankalin jama'a saboda ta wallafa hotunan Muhammad a shafukan sada zumunta a shekarar 2012. Bugu da kari, ta ci gaba da yin Allah wadai da wuce gona da iri da kuma kare matan da aka zalunta.[4] [5] ·

Ita ma wakiliya ce ta kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa a Tunisia kuma mai magana a cikin taruka da tarurrukan karawa juna sani a matakin kasa, yanki da na kasa da kasa.[6] Daga shekarar 1999 ta kasance memba na Ƙungiyar Matan Demokraɗiyya ta Tunisiya wadda ta zama shugaba a cikin watan Afrilu 2018. [7] Ta shiga ƙungiyar mata ta Tunisiya don binciken ci gaba (ma'ajin kuɗi a shekarar 2002 inda ta ɗauki matsayin manajan horo daga shekarun 2005 zuwa 2008.

Wallafe-wallafe

gyara sashe

Yosra Frawes ita ce marubuciyar, ko mawallafin, na jagora, bayanin kula da rahotanni kamar:

  • Jagora ga Matakai 100 don kawo karshen cin zarafin mata (mawallafin haɗin gwiwa)[8]
  • Tabbatar da haƙƙin ɗan adam: daga Kundin Tsarin Mulki zuwa dokoki (marubuci)[9]

Haka nan ta yi fice wajen rubuce-rubucenta da kuma kasidunta na wakoki ta buga wakoki da kasidu da dama kan gudunmawar mata a adabin Larabci. [10]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Égalité dans l'héritage: Yosra Frawes évoque l'obstacle de "l'alliance sacrée de l'argent, de la religion et de la politique" | Al HuffPost Maghreb" [Equality in inheritance: Yosra Frawes evokes the obstacle of "the sacred alliance of money, religion and politics]. huffpostmaghreb.com . Retrieved 26 August 2019.
  2. "Samsung double Apple pour le premier trimestre aux USA | Clickpresse.com | Actualité et Infos au Maroc et dans le monde" [Tunisia: who is Yosra Frawes, the new president of the Association of Democratic Women?]. clickpresse.com . Retrieved 26 August 2019.
  3. "Tunisia passes historic law to end violence against women and girls | UN Women – Headquarters" . unwomen.org . Retrieved 27 September 2019.
  4. "Yosra Frawes - Expertes France" . expertes.fr . Retrieved 26 August 2019.
  5. "Education, the key to preventing and combating violent extremism" . unesco.org . 9 March 2016. Retrieved 22 April 2018.
  6. "Yosra FRAWES - International Federation for Human Rights" . fidh.org . Retrieved 27 September 2019.
  7. Tunisia: who is Yosra Frawes, the new president of the Association of Democratic Women ?
  8. "Guide des 100 mesures pour l'éradication des violences à l'encontre des femmes" . fidh.org (in French). 12 May 2017. Retrieved 22 April 2018.
  9. "Droits humains garantis : de la Constitution à la législation" (pdf). fidh.org (in French). Retrieved 22 April 2018.
  10. "Yosra Frawes" . turess.com (in Arabic). Retrieved 22 April 2018.