Yonas Kinde (an haife shi a ranar 7 ga watan Mayun shekarar 1980) ɗan wasan tsere ne daga Habasha, amma yanzu yana zaune kuma yana ɗan ɗaukar i horo a Luxembourg, wanda kwamitin wasannin Olympics na duniya (IOC) ya zaɓa don ya fafata a gasar Olympics ta 'yan gudun hijira a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2016 Rio de Janeiro, Brazil. Yves Göldi ne ke horar da shi. Yonas ya yi gudun marathon mafi sauri da sa'o'i 2 da mintuna 17.

Yonas Kinde
Rayuwa
Haihuwa Habasha, 7 Mayu 1980 (43 shekaru)
ƙasa Luksamburg
Sana'a
Sana'a long-distance runner (en) Fassara da marathon runner (en) Fassara
Athletics
Sport disciplines 10K run (en) Fassara
half marathon (en) Fassara
marathon (en) Fassara
road running (en) Fassara
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 
Nauyi 57 kg
Tsayi 172 cm

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Yonas, dan asalin Habasha ne. Yana zaune a Luxembourg tun 2012 kuma yana ƙarƙashin kariya ta ƙasa da ƙasa a Luxembourg tun 2013.[1] Yonas yana magana da Faransanci, Ingilishi, Luxembourgish da Amharic, kuma yana aiki a matsayin mai ilimin Massage.[2] [3][4]

Aikin wasanni gyara sashe

Yonas ya fara gudu ne a ƙasar Habasha tun yana matashi, musamman a tseren gudun mita 10,000 da Half Marathon, inda daga ƙarshe ya kai ga cikakken tseren gudun marathon. A lokacin da yake dan ƙanƙanin aikinsa na tsere a Turai, wanda Yves Göldi ya jagoranta, ya lashe kofuna da dama a Luxembourg, Faransa da Jamus.[5] A Frankfurt, Jamus ya gudanar da mafi kyawun sa a cikin shekarar 2015 a cikin sa'o'i 2 da mintuna 17.

Saboda matsayinsa na gudun hijira, Yonas ba zai iya shiga gasar kasa da kasa ba, duk da cewa ya yi saurin samun cancantar shiga gasar.[ana buƙatar hujja]A ranar 3 ga Yulin shekarar 2016, IOC ta sanar da cewa Yonas zai kasance cikin tawagar 'yan wasa goma da aka zaba don matsayin tawagar 'yan wasan Olympics na 'yan gudun hijira a gasar Olympics ta lokacin rani ta shekarar 2016 a Rio de Janeiro, Brazil.[6] Ya yi takara a tseren gudun marathon na maza.[7]

Gasa gyara sashe

Shekara Gasa Wuri Matsayi Taron Bayanan kula
Representing Refugee Athletes
2016 Summer Olympics Rio de Janeiro, Brazil 90th Marathon 2:24:08

Mafi kyawun mutum gyara sashe

  • 1500 m - 3:56.56 a cikin Kirchberg (LUX) ranar 18.02.2014
  • 3000 m - 8:38.10 a cikin Kirchberg (LUX) ranar 30.01.2016
  • 5000 m - 14:32.69 a cikin Schifflange (LUX) ranar 04.08.2013
  • 8 Hanyar kilomita - 23:05 a cikin Trier (GER) akan 31.12.2013
  • 10 Hanyar kilomita - 30:01 a Langsur (GER) akan 09.11.2013
  • Half marathon - 1:03:22 a cikin Remich (LUX) ranar 28.09.2014
  • Marathon - 2:17:31 a Frankfurt (GER) ranar 25.10.2015

Manazarta gyara sashe

  1. tetrik.ch. "Ethiopian,Yonas Kinde, selected for Refugee Olympic Team for Olympic Games Rio 2016 - IOC News Room" .
  2. Davis, Rebecca (2016-08-01). "From Peace Run to Rio: The Story of Refugee Olympic Team" . NBC News . Archived from the original on 2017-02-07. Retrieved 2017-02-07.
  3. Armstrong, Jeremy (2016-08-02). "10 inspirational stories of the first Refugee Olympic team at Rio 2016" . Mirror. Archived from the original on 2017-02-07. Retrieved 2017-02-07.
  4. Blair, Olivia (2016-08-09). "The inspirational stories behind the Olympic refugee team" . The Independent. Archived from the original on 2017-02-07. Retrieved 2017-02-07.
  5. "ARRS - Runner: Yonas Kinde" .
  6. "Refugee Olympic Team to Shine Spotlight On Worldwide Refugee Crisis" . International Olympic Committee. 3 June 2016. Retrieved 3 June 2016.
  7. "Refugee Olympic Team" (PDF). International Olympic Committee. Retrieved 5 June 2016.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe