Yanyin kasar Hausa
Ka duba wannan shafin domin sanin yanda zaka gyara wannan mukalar Koyon rubuta mukala
Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba. |
Kasar Hausa, galibinta shimfidaddiya ce mai yawan sarari. Wato, bata da yawan tddai da kwazazzabai. Manyan Kogunanta guda biyu ne, wato kogin Rima da Kogin Hadeja. Har ila yau, tana da baban daji da ya kusa kewaye kasar, kuma yana da yanayi guda biyu, wato, daga kuduncin kasar yana da duhu da dogayen bishiyoyi, amma daga arewaci ba shi da duhu sosai domin bishiyoyinsa ma jifa-jifa ne kuma gajajjera. Ana kiran dajin kasar Hausa da sunaye daban-daban a garuruwa daban-daban. Ma'ana, a Bauchi ana kiransa dajin YANKARI, a Kano ana kiran sa dajin FALGORE, a Katsina ana ce masa dajin RUGU, Amma a Sakkwato a ce dajin GWAMNA.