Yam balls wani nau,in abincine wanda akeyinshi da doya kamar da Azumi wasu sunayinshi amadadin kosai ko kuma fanke

Yam balls

Kayan hadin yam balls

gyara sashe

1.doya

2.mai

3.kwai

4.lawashin albasa

5.sinadarin dandano

6.citta

7.tafarnuwa

8.fulawa

9.kori

Yanda ake hadashi

gyara sashe

da farko ki fere doyanki sannan ki dafata idan tadahu sai kisauketa sannan ki zubata acikin turmi sai ki dakata samsara basai tayi laushiba kamar sakwara bayan kin gama dakata saiki juyeta acikin roba sai ki yanka lawashiki ki zuba aciki ki daka cittarki da tafarnuwarki kizuba insan samune kisamu danyar citta sai kizuba korinki sannan saiki mulmulashi kamar ball bayan kin gama sai ki Dora manki asaman wuta ma,ana ki soyashi sannan kifasa kwanki kisama wannan mulmulallan doyanki Fulani ta yanda kwanki ze zauna ajinshi sannan sai ki soyashi.