Yakubu Yakson Sanda (an haife shi a shekara ta 1965) ɗan, siyasar Najeriya ne daga Bicizà wanda aka zaɓe shi a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Filato ta tara a shekarar 2021.[1] Sanda shine ɗan, majalisa na farko da aka zaɓa daga Mazaɓar Pengana a jam'iyyar All Progressives Congress a 2019. Ƴan majalisar ne suka zaɓe shi a matsayin, kakakin majalisar bayan tsige Rt. Hon. Abok Ayuba.[2][3]

Yakubu Yackson Sanda
Rayuwa
Haihuwa 1965 (58/59 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Ilimi gyara sashe

Yakubu Yackson Sanda ya halarci kuma ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a makarantar firamare ta UNA da ke Jos, inda ya kammala karatunsa na Sakandare a Kwalejin Metropolitan, Jos.

Ya yi karatun Economics a Jami'ar Jos da ke Jihar Filato. Bayan haka, ya yi aiki da Hukumar Wasanni ta Jihar Filato a matsayin Akanta.

Sana'a gyara sashe

A matsayinsa na ma’aikaci kuma Akanta daga Sana’a Yakubu Sanda ya samu muƙamin Daraktan kuɗi da samar da kayayyaki a ma’aikatan gwamnatin jihar Filato a ma’aikatar wasanni ta jihar Filato.

Ya taɓa yin aiki a Majalisar Wasanni ta Jihar Filato, da Akanta a Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Plateau HighLand, da Manajan Ƙungiyar ta Plateau United FC.

Siyasa gyara sashe

Ya fara tafiyar sa ta siyasa tun yana matashi sama da shekaru 20 da suka wuce, lokacin da aka zaɓe shi ya jagoranci ƙungiyar ci gaban matasa ta Buji a matsayin shugaban ƙungiyar ta ƙasa.

Bayan haka ya tsaya takara a zaɓen majalisar dokokin jihar Filato a 2003, 2007, 2011 don wakiltar mazaɓar Pengana, wanda ya sha kaye.

A ƙarshe an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar tarayya a zaɓen 2019, kuma an zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar bayan an tsige tsohon shugaban majalisar.

Rayuwa ta sirri gyara sashe

Yakubu Yakson Sanda Kirista ne. Ya auri Nancy Yakubu Sanda kuma auren nasu da sukayi sun samu ƴaƴa uku.

Manazarta gyara sashe