Xolisile Zamisa (Née Zondi) ko kuma kawai Xoli Zondi-Zamisa (an haife ta ranar 17 ga watan Satumba 1983), ƴar wasan kwaikwayo ce ta Afirka ta Kudu. An fi saninta dalilin rawar da ta taka a cikin shirye-shiryen talabijin na Family Bonds, Generations da Single Galz.[ana buƙatar hujja]

Xoli Zondi
Rayuwa
Haihuwa 17 Satumba 1983 (41 shekaru)
Sana'a
Sana'a jarumi, ɗan wasan kwaikwayo da stage actor (en) Fassara
IMDb nm8009514

Rayuwa ta mutum

gyara sashe

An haifi Zondi ranar 17 ga Satumba 1983 a Hammersdale, Afirka ta Kudu. Ta kammala difloma a fannin wasan kwaikwayo daga Jami'ar Fasaha ta Durban a shekara ta 2003.[1]

Ita ƴa ce ga Mandy daga dangantaka tun tana ƙarama, inda ta yi ciki tana da shekara 16. Ta auri Phiwokuhle Zamisa, mai ba da shawara, inda aka yi bikin auren a ranar 2 ga watan Disamba 2017. Ma'auratan suna da 'ya ɗaya, Ukusa Zamisa wacce aka haifa ranar 26 ga watan Oktoba 2018.[2][3]

Fina-finai

gyara sashe
Year Film Role Genre Ref.
2006 Family Bonds Winnie TV series
2010 Generations Zodwa Mabena TV series
2013 eKasi: Our Stories Smangele TV series
2014 Zaziwa Herself TV series
2014 Mzansi Love Londiwe TV series
2014 Single Galz Ntsiki TV series
2015 Him, Her & the Guys Ntombi Mkhize TV series
2015 Zabalaza Amahle TV series
2016 Greed and Desire Nqobile Gigaba TV series
2017 Easy Money Khosi TV series
2019 Isipho Nkanyezi Shezi TV series
2021 Imbewu: The Seed Violeta Vilakazi TV Series

Manazarta

gyara sashe
  1. "Xoli Zondi: TVSA". www.tvsa.co.za. Retrieved 2021-10-29.
  2. Mkhize, Lesego. "IN PICS: Actress Xoli Zondi reveals pregnancy". Drum (in Turanci). Retrieved 2021-10-29.
  3. Gwala, Nompilo. "PIC: Xoli Zondi gives birth to her daughter". Drum (in Turanci). Retrieved 2021-10-29.

Hanyoyin Hadi na waje

gyara sashe