Kamar yadda aka zayyana a baya, za'a bada kyaututtuka ga waɗanda suka yi nasara a gasar da kuma cewa dan a ƙarfafa gwiwar shigowar mata aka wata kyauta ɗaya gare su, haka yasa muka cika alƙawarin mu. Insha Allah zamu tuntuɓe kowa ta imel dan baiwa kowa kyautar sa cikin wannan mako.

  1. . Smartphone Infinix (ko makamanciyarta)
  2. . Smartphone Infinix (ko makamanciyarta)
  3. . Hard Drive.

Masu nasara: Muna farin cikin sanar da sakamakon waɗanda suka yi nasarar lashe gasar murnar Wikipedia 20 kamar haka.. Sakamakon gasa

Maza
Mata

Alƙalan gasa gyara sashe

Wannan gasar ganin cewa anyi rubutu da dama cikin ƙanƙanin lokaci fiye da tsammani. Alƙalancin maƙalolin zai gudana ne daga ƴan'gasar (waɗanda suka fafata a gasar) ta yadda kowa zai duba wa ɗan'uwansa aikinsa. Ga yadda dubawar zata kasance;

  • Sabon maƙalar da aka ƙirƙira = 2
  • Maƙala mai rubutu maikyau wanda babu kurakurai = 2
  • Ga kowane reference (manazarta) da akayi anfani dashi a maƙala = 1
  • Hoto da aka sanya a maƙala = 0.5
  • Category da aka sanya a maƙala = 0.5

Jimillar abunda ingantacciyar maƙala zata samu shine maki 2+2+1+0.5+0.5 = 6

Kira ga Abubakar A Gwanki, Yusuf Sa'adu, Aliyu shaba, Mbash Ne, Salihu Aliyu, Mrym009, Umar-askira, Justice Mudansir da Bello Na'im. ƴan'gasa da su tan-tance muƙalolinsu akan tsarin da aka bayar a sama dangane da yadda za'a bada maki ga kowace muƙala da aka ƙirƙira a gasar, wannan na daga cikin ire-iren tsari da ake amfani da su a gasa daban-daban dan tan-tance muƙaloli. Adadin lokacin da aka ware wa wannan aiki shine mako biyu, sai mako na uku zamu bibiya mu tabbatar da aikin kowa daga nan sai mu sanar da sakamako waɗanda suka yi nasara. Allah ya bada Sa'a.