Wikipedia:Gasar murnar Wikipedia20
Barka da zuwa Gasar murnar Wikipedia20 dan ƙirƙira, ingantawa da faɗaɗa shafukan Wikipedia!
Gabatarwa
gyara sasheA ran 15 ga watan Janairu, 2021 Wikipedia ta cika shekara 20 da farawa. An fare ta ne a 15 ga watan January na 2001. Hausa Wikimedians User Group na fatan kasancewa tare da sauran ma'abuta Wikipedia a sauran sassa na duniya domin shirya kwarya-kwaryan biki domin murnar zagayowar wannar rana.
Wikipedia ta kasance kundi ce ta ilimi. A cikin shekaru ashirin da suka gabata ta tattara bayanai akan ilimomi na fannonin rayuwa daban-daban dan samar da ilimi ga kowa da kowa, da kara haɓaka nazari da bincike. Wikipedia itace mafi shahara kuma kundi ce data tara ilimi daka taba yi yawa, sannan babban madogra ga masu son fara bincike akan wani al'amari. Manufar Wikipedia shine kowane dan'dam yasamu ilimi akan kowane abu batare da biyan wani abu ba o shan wahala a wajen neman wanna bayi.
Wikipedia tayi ƙarko da masana da masu nazarce-nazarce a kanta basu yi tsammani ba. A lokain da aka fara ta mutane da yawa sunyi kirdadon ko zaton bazata kawo wannan lokaci ba, to saidai gashi ta kawo kuma ma har zata wuce.
#Wikipedia20 Bikin Wikipedia20 za'ayi shine domin godiya da samuwar wannan kundi mai muhimmancin a garemu, da kuma tattauna abubuwan da ya kamata muyi domin bada tamu gudummuwar domin cigaban wannan ginin da ba mai karewa ba.
Shiri A Kaduna a ranar Asabar 21, ga watan January na shekarar 2021.
Gasa Akwai kwarya-kwaya gasa kuma da za ayi tsakanin 01 zuwa 15 ga watan Maris domin bada kyaututtuka duk acikin wanna bikin nacikar Wikipedia shekara 20.
Ƙa'idoji
gyara sashe- A koda yaushe abu mai amfani shine idon nasara!
Akwai wasu muhimman ƙai'doji da za a bi domin kasancewa a cikin wannan gasar:
- Muƙala da aka rubuta ta kasance cikin daidaito na adalci ba tare da son zuciya ba.
- Muƙala da aka rubuta da kyau, a taƙaice, kuma ba tare da kwafin rubutu daga wani wuri ba, ko kuma yawan kurakuran ƙa'idojin rubutun Hausa.
- Muƙala da aka rubuta da ingantattu kuma sanannun manazarta kuma a cikin tsari.
- Yana da kyau muƙalar ta zama tana da hoton a inda hakan ya dace, ko zai kara sa makaranci fahimtar jigon saƙon.
- Dukkan hotuna ya zama an bayyana matsayin haƙƙin mallakarsu, kuma an bayar da bayanin amfanin sa hoton.
- An sanya muƙalar a cikin rukunan da suka dace. Yana da kyau a samu aƙalla rukuni guda uku ko sama da haka.
- An bi ƙa'dojin rubutun wikitext ta hanyar amfani da mahaɗa ta ciki da ta waje zuwa wasu shafukan.
- Dukkan bayanan da ke cikin muƙalar su zama masu sahihanci, da kuma rubutu mai kyau.
- Wanda sukayi rijista a wurin taron bikin murnar Wikipedia20 suna da maki da aka ware.
- Domin tabbatar da daidaito da ƙarfafa mata, an ware masu kyauta ɗaya gare su.
Mukaloli
gyara sashe- Shiga nan dan jera muƙalolinku da ku ka rubuta
- Me gasar ke dauƙe da ita: Wannan gasa ce da zata ƙara yawa da inganta muƙalolin shafukan Wikipedia dan faɗaɗa yawan ilimin mu.
- Yaushe ne: Gasar zai fara daga 00:01 a 1st Maris (GMT+1) har zuwa 23:59 15 Maris 2021 (GMT+1).
- Ya-ya gasar take: Gasar ta ta'allaƙa ne kacokan dan samar da wayoyin smartphones ga waɗanda ke nema dan cigaba da ayyukansu na yin rubuce-rubuce a manhajojin Wikipedia, da ƙarfafa basira da fasahar editoci masu ƙwazo.
- Waye ke iya shiga: Kowa na iya shiga dan taimakon rubuta maƙala da/ko fassara(mai-inganci) muƙala akan a'dabu (halaye na kwarai). Duk edita mai akwatin dake da rijista (akan wannan manhajar) na iya shiga, sai dai akwai tsari ga waɗanda suka halarci gasar Wikipedia20 a Kaduna. Dan shiga ku rubuta sunayen ku anan ta hanyar sanya alama kamar haka '''"~~~~"'''.
- Dalilin gudanar da gasar: Wannan gasar na ƙarƙashin gudanarwan Hausa Wikimedians User Group ne da tallafi daga Wikimedia Foundation. Wikipedia ta ƙarancin muƙaloli akan abubuwa da dama, kuma ta hanyar wannan gasar muna saran mu inganta muƙaloli akan a'dabu da halaye na ƙwarai akan tunanin cikakken hankali ba kirdadau da bitan sautin gari ba! Wannan gasa nada muhimmanci sosai a gare mu dan mu tabbatar da masu yin karatu a shafukan mu sun sami ingantattu Kuma sahihan bayanai.