Shandado wasa ne da ake gudunar dashi a fage. Fage fili ne da ake zuwa ayo wasani na wargi, idan aka aiki yaro,ko aka sa shi kiwo ya kiya ko ya yado busashe, ana sa mayan fage suyi masa hukunci. Idan kaka tayi za'a tara jama'a sai a fidda sarkin dado,za'a tara makada,samari da yan mata, yan mata zasuyi girki,su daka fura, suyi dambu,su tatsi nono daga busashe.Yan garuruwa da yawa makusanta sukan zo(akan yi wasan da dare).Idan gari y waye yan gari sai su dauki baki su kai gidajensu su basu abinci,fura,dambu da nono,idan yamma tayi baki zasu koma garuruwansu,sai a yanke kaji a soye da goro a basu su tafi dasu.Ana yin wasan duk shekara.Idan yan wani gari suma sukaje wasan shan dado a garin da aka gayyacesu sukan linka masu garan da suka basu.

Yadda ake gudanar da wasan gyara sashe

Idan ana gudanar da shandado ana sa lema,bara,alkali da sarauniya,akan bi hanyoyin da lema,bara,alkali da sarauniya ke biyowa a nome ta tas ba haki idan damina tazo,duk saurayi ko budurwar da bata zo ba sai a tada lema da bara suje su taho da shi/ita,akwai kuma shuwagabannin fage da suke zaune bakin bishiya suna lura da kowa,idan an shiga gida to hadari ne ya taso,anan za'a kwana duka(samari da yanmata)cikin gonakai.

Bakin kalmomi gyara sashe

1.Fage na nufin fili

2.busashe na nufin dabbobi

3.lema na nufin dan aike

4.bara na nufin yar aike

5.alkali na nufin mai Yanke hukunci

6.haki na nufin ciyawa

Manazarta gyara sashe