SANA'AR NOMA Noma na duke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai ya tarar, wanna shine kirarin da akewa noma, sanar noma tasamo asaline tun shekaru aru-aru da suka wuce mutane ko kuma duk al'umma ta duniya amfani da noma akowane fanni domin sai da shine kadai za'a iya samun abinda aka sawa 'yan ciki domin samun natsu acikin dukkani ayukka, kuma dukkan kasar ba'ayin noma to tana dauke da cibaya ta ko wace hanya.   ABUBUWAN DA'AKE NOMA.  Akasar hausa ana amfani da abubuwa kamar haka wajen sana'a noma, kamar kalme, fatanya, dinga, adda, lauje da sauransu. Hausawa sun shahara matuka wajen sana'ar noma domin shine suka tashi sami iyaye da kakanni sunayi shine makasudin da ba zaka raba bahaushe da sana'ar noma ba.