MARNAF GLOBAL DIY
Ya yi rajista 28 ga Augusta, 2021
MARNAF GLOBAL DIY. Shafin kasuwanci ne,Wanda ya ke koyar da fasahar sarrafa tsofaffin kayan masarufi na gida zuwa sababbi,ko Kara gyara sababbi abubuwa zuwa yadda mutum ya ke so.
A takaice Muna koyar da Mata yadda za su maida abubuwan da su ke ma kallon shara zuwa kudi ,domin gyaran muhalli,da kiyaye ko rage yawan zaizayar kasa da gurbacewar muhalli saboda datti.
Muna koyar da abubuwan sana'o'i na hannu a fili da ta waya.
Sannan Muna bada gudummawa ga abubuwan da suka shafi muhalli ko lafiya.