Kabiru Yusuf
Falalar AZUMI RAMADAN DA HUKUNCE-HUKUNCENSA
Na
MUHAMMAD KABIR
ABUBUWAN DA SUKE CIKI 1. Ma’anar Azumi 1. Ganin Wata 2. Daukar Niyya 3. Dalilin Cika Azumi Talatin 4. Abubuwan Ki Ga Mai Azumi 5. Abubuwan Da Mai Azumi Zai Kiyaye Da su 4. Abubuwan Da ke Bata Azumi 6. Abubuwan Da Ke Sa A Yi Ramuwa 7. Abubuwan Da Ke Sa A Yi Kaffara 8. Yadda Ake Yin Kaffara 9. Abubuwan So Ga Mai Azumi 10. Falalar Watan Ramadan 11. Yadda Ake Ittikafi 12. Sallar Tarawihi 13. 14. Kardadan Daren Lailatul Kadari 14. Zakkar Fidda Kai 15. Sallar Tahjudi 16. Nafilolin Dare Da Falalolinsu
MA'ANAR AZUMI A LUGGA DA SHARA'A
A
zumi shi ne kamewa daga ci da sha, da jima'i da zancen banza tun daga Asubahi zuwa Magariba wato faduwar rana. Da niyyar yin/bayar da ibadar farilla.
1. Azumi yana wajaba ne ga Musulmi baligi ko baliga. Don haka ba farilla ba ne ga yaro ko yarinya wadanda ba su balaga ba. Amma suna azumtar shi domin su saba da yi a shara'ance, kuma ladan yana ga wanda ya tarbiyantar da su. Sannan wanda bai Musulunta ba, ba ya yin azumi.
2. Hankali:- Dole ne mutum mai hankali ya yi azumin watan Ramadana dukkansa ba tare da yanke wa ba, matukar babu wata lalura a tare da shi. Idan lalura ta hau mutum kamar wacce ta shafi hankalinsa to anan azumi bai wajaba a kansa ba. Haka kuma wanda hankalin shi ke gushewa lokaci-lokaci, kamar mai ciwon shigar aljanu, wanda idan aljanin zai tayar a kan shi yayin da yake azumin ya gusar masa da hankali, to babu ramuwa a kansa. Ko kuma mai ciwon farfadiya, sai dai idan sun farka a wurin da ake ciki kafin faduwar rana. Ko kuma tsoho, wanda ya shiga rudin hankali saboda yawan shekaru.
3. Daukewar jinin al'ada na biki, wato na haihuwa da jinin cuta da wani lokacin yake zarcewa mata. Idan jinin ya zarce da ita har bayan ketowar alfijir to shi kenan ba za ta yi azumi ba amma za ta rama shi. Duk yayin da farin ruwa ya gama zuwar wa mai al'ada ta kuma wanke ta sa auduga ta kalato babu ragowa to za ta yi wanka ne ta fara ibada kamar abubuwan da aka haramta mata, to yanzu sai su halatta a gareta. Idan da daddare ne kafin alfijir ya keto, shi kenan sai ta yi azumi. Haka ma mai jinin biki. Mai jinin cuta ita kuma za ta yi wanka ta yi salla amma ba za ta yi azumi ba har sai ta warke za ta rama. Mace mai ciki da mai shayarwa. Suma an dauke musu azumi bai wajaba a kansu ba har sai sun sami waraka. Sai dai wasu sun ce za su ciyar da muskini yayin da ake ramuwar.
GANIN WATA A llah (S.W.T) ya ce: "Duk wanda ya riski watan daga cikinku, to ya azumce shi." Bakara 185 Duk wanda aka ga jinjirin watan Ramadana yana cikin gari, ba wnada ya fita ba, kuma mai lafiya to sai ya azumci wannan yinin da za a tashi da azumin. Sabanin matafiyi da kuma mara lafiya, domin matafiyi idan zai yi tafiyar shi ne bayan ketowar alfijir to sai ya bari ba zai daura azumin ba, amma zai rama. Haka ma wanda bashi da lafiya ba zai yi azumi ba amma zai rama shi. Annabi (S.A.W.) ya ce: "Idan kun gan shi (watan) to ku azumce shi, idan ku ka gan shi ku ajiye azumi, idan an yi girgije a gareku to ku kadarta a gare shi" Ibn Umar. A wani hadisin kuma ya ce: "To ku cika adadin Sha'aban kwana talatin." Azumin Ramadan yana wajaba ne da ganin jinjirin watan Ramadan da ido, ganin mutane da yawa ko kadan, koda mutum guda adali cikakke. Saboda hadisin da ya zo daga wajen Abdullahi Ibn Umar cewa: "Mutane suna ta duba don ganin watan (jinjirin watan Ramalana) sai na fadawa Annabi (S.A.W.) cewar ni na ga jinjirin watan. Sai Manzon Allah (S.A.W.) ya dauki azumi ya kuma umarci mutane da su dauka. Saboda dalilin wannan hadisi malamai suka tabbatar da cewa ba lallai ba ne ka ce lallai sai ka ga jinjirin watan za ka dauki azumi ba, yana wajaba a kanka da ganin adali ko adalan mutane wadanda suke mutanen kirki ne ba sa karya. Domin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi an gaya masa cewa an ga wata kuma ya dauka. Haka nan bayan wannan hujja babu wata wacce manyan malamai suka yi riko da ita cewa lallai ne daukar azumi sai mutum ya gani da idanunsa wannan babu aya ko hadisi ko sahihiyar maganar malamai da aka yi riko da ita.
Haka nan idan kwanaki ashirin da tara na Sha'aban sun cika ba a ga watan jinjiri ba, to sai a cikin adadin kwanaki talatin na watan Sha'aban sai a dauki azumin. Wannan ita ce sahihiyar hanya kuma wasu malaman ba su yarda da harafin masu ilimin taurari ba wajen daukar azumi domin suna kafa hujja ta gani da ido aka ce a cikin hadisin. Wasu kuma sun amince da amfani da ilimin falaki wajen lissafin ganin wata saboda hujja da hadisin da Bukhari ya rawaito cewa Annabi S.A.W. ya ce: "Mun kasance al'umma wacce ba ta iya karatu da rubutu ba, da ilimin falaki, don haka ku yi azumi da ganin shi ku ajiye da ganin shi wata idan an yi girgije a gare ku, to sai ku cika adadin Sha'aban kwanaki 30.
DAUKAR NIYYA D aukar niyya dai shi ne kudurcewa a zuciya da kuma fili, cewa mutum ya yi niyyar azumtar watan azumin Ramadan gaba daya in ya kudurce haka gami da bayyanarwa bayan ganin jinjirin wata wasu manyan malaman suna ganin haka ya isar masa wato kudurtar azumtar farilla, azumin gaba daya. Yayin da wasu suke ganin sai ya rinka maimaita niyyar a kowane dare. Amma sahihiyar hanya ita ce idan mutum ya dauka sau daya a daren farko to ta wadatar masa, saboda a jere yake yi babu yankewa, inda kuma wani abu zai sa ya sha azumin to in ya zo daurawa sai ya maida niyya. Ita dai niyya farilla ce a rukunin azumi domin Annabi (S.A.W.) ya ce: "Kowane aiki sai da niyya. Kowanne mutum yana gare shi abin da ya yi niyyar."
Wani hadisin kuma ya ce: "Babu azumi ga wanda bai dauki niyya ba tun daga dare." Saboda wannan hadisi ne ma malamai suka ce idan ba ka kwana da niyya ba sai washegari ta bayyana a gare ka, cewar an ga wata, to babu azumi a gareka kuma za ka kame bakinka daga ci da sha da jima'i, kuma za ka rama wannan azumi. Ko kuma wanda ya yi niyyar idan an ga wata gobe, to ina azumi idan ba a gani ba ba na yi, to shima idan gari ya waye masa, kuma ya sami cewa an ga wata, to a shari'ance babu azumi a gare shi, zai rama ne kuma zai kame daga dukkan abin da mai azumi ya kame daga barinsa. Idan mutum ya dauki azumi ba tare da niyya ba to ko da ya yi shi, to ba shi da azumi sai ya rama shi. Saboda dogaro da wancan hadisin da ke sama.
DALILIN CIKA AZUMI TALATIN
Wannan yana samuwa ne yayin da aka yi azumi ashirin da tara watan Ramalana, amma watan Shawwal bai tsaya ba, ko kuma an yi hazo ba a ga wata ba wato an yi gumma. To sai a cike azumi talatin, kamar yadda mai littafin Risala ya tafi a kan cewa kwanaki ashirin da tara, ko talatin daga gummin watan da ke gaban shi.
ABUBUWAN DA KE BATA AZUMI DA ABUBUWAN DA BA SA BATA AZUMI Anan akwai wasu abubuwa wadanda idan mutum ya yi su, ko suka afku a agre shi, to Azumin shi ya baci sai ya yi ramuwa wasu kuma sai ya yi KAFFARA. Abubuwan sune kamar:- 1. Kin yin niyya:- Niyya farilla ce ga mai yin Azumi idan har babu niyya (ta jumla yake a kai, ko kuma ta maimaitawa wato ta kullum) to ba shi da azumi saboda hadisi da aka rawaito daga Annabi (S.A.W) wanda muka yi bayani a babin niyya.
2. Yin amai:- Malamai sun tafi bisa cewa idan har aman bai koma ba yayin da aka yi shi, cikin makwagoro ba to Azumi yana nan, amma matukar ya koma cikin makogwaro ta Azumi ya karye. Ko kuma yayin da mutum ya kakaro amai din da kan shi, da gangan.
3. Ci ko sha bayan fitowar alfijir:- Wannan idan ta faru to Azumi ya karye sai an rama shi kuma ana kame baki ne har rana ta fadi. Idan mutum ya ci ya sha bayan tabbacin fitowar alfijir, to bashi da Azumi. Idan yana shakkun fitowar alfijir, to shi kenan, ba zai ci ba. Idan kuma alfijir ya keto ne alhali yana ci to sai ya ci gaba, saboda hadisin da Abu Hurairah ya rawaito cewa, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: "Idan dayanku ya ji kiran sallah alhali (kwarya ko moda) na hannunsa kada ya ajiye har sai ya biya bukatarsa." Wannan ya nuna cewa idan kana cikin ci ko sha din to sai ka ci gaba, kar ka daina ba, da zarar ka gama shi kenan, to ballantana ma wanda yake kokwanto. Sai dai mutum ya kiyaye da lokaci sosai.
4. Ci ko sha bisa mantuwa ko isar wani abu makogwaro kamar ruwa, ko kura ko kuda, da sauransu: Amma akwai ramuwa idan aka ci ko sha bisa mantuwa. Idan mutum ya ci ko ya sha ba bisa mantuwa ba (yana sane) to Azumin sa ya karye, wato ya baci zai yi ramuwa da kaffara a jere. Amma sabanin mai mantawa ana samun rangwame cewar azuminsa na nan saboda hadisin da ya zo daga Abu Hurairah (A.S.) ya ce Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: "Idan mutum ya manta, kuma ya ci ya sha, to sai ya ci gaba da azuminsa, domin Allah ne ya ciyar da shi kuma ya shayar da shi." Ga mai mantuwa; wasu daga cikin malamai suna ganin akwai ramuwa. Yayin da wasu kuma suke ganin babu ramuwa kamar yadda ya zo a hadisin. Amma abin da ya fi shi ne a rama azumin da aka ci ko sha bisa mantuwar. Sannan ana kame baki da zarar an tuna.
5. Ci ko sha don zaton faduwar rana: Idan mutum ya ci ya sha, sai ta bayyana gare shi cewar rana ba ta fadi ba, to anan zai ci gaba da kame bakin shi ne har sai rana ta fadi. Zai yi ramuwa babu kaffara a gare shi matukar ba da gangan ya yi ba.
6. Karya da zur: Karya tana bata azumi, domin Annabi (S.A.W.) ya ce "Karya tana shiryarwa ne izuwa fajirci." Haka ma shaidar zur ka fadi abin da ba haka ba ne, ka bada shaida a bisa haka ne da rantsuwa da komai, don wani abin duniya. Annabi (SAW) ya ce "Wanda bai bar zancen zur ba da aiki da shi ba, to ba shi da wata bukata ga Allah don ya bar cinsa da shan sa." Ma'ana Allah ba ya son azumin shi da ya ke yi saboda haka shima bashi da azumi.
7. Fita daga Musulunci:- Idan mutum ya fita daga Musulunci (wato ridda wacce ake yinta da kalmomin da ake furta su da baki) alhali yana Azumi. To anan ma azumin shi ya baci ko da ya dawo Musuluncin Allah ya tsare mu, amin.
8. Yin jima'i da rana:- Idan mutum ya sadu da iyalinsa da rana to azumin shi ya karye wato ya bata azumin shi. Sai ya yi ramuwa da kaffara.
9. Fitar maniyyi:- Idan maniyyi ya fitowa mutum ta sumba ko rungume-rungume ko wasanni ko tuntuntuni, to auzmi ya karye sai an rama shi, kuma za a yi kaffara. Amma idan maziyyi ne to ramuwa ne babu kaffara.
10. Zuwan Jinin Haila ko Biki:- Idan haila ya zowa mace, ko jinin haihuwa, to azumi ya karye za ta rama shi kuma ba za ta yi ba har sai jinin ya dauke mata.
11. Ciwo ko rashin lafiya: Idan mutum ya ji ciwo na zubar da jini sosai, to azumin shi ya karye zai rama. Haka ma wanda bai da lafiya shima babu azumi a gare shi. Wato yana azumin rashin lafiyar ta same shi, to zai ajiye azumin saboda fadin Allah madaukakin sarki. Haka ma matafiyi, kamar mutum da bai san da tafiyar ba sai bayan da safe ko da rana shima zai ajiye azumi sai gaba ya rama.
WADANDA AKA YI RANGWAME A KANSU 1. Mace mai ciki:- Idan azumin yana ba ta wahala sosai to sai ta ajiye azumin ba za ta ci gaba ba, ta ciyar da miskini mudu duk kullum ko kuma kullum ta fada abincin ta zuba mai komai ta zuba cikin kwano ta bai wa miskini, wannan zai fi ta bayar da dawa ko masara danya mudunnabi biyu.
2. Dattijon mutum:- Shima wannan an yarda ya rika ciyarwa kullum in dai ba shi da damar iya yin azumin matukar tsawon rayuwar shi.
3. Mace mai shayarwa:- Ita ma za ta ajiye azumi, idan ta ji tsoron cutuwar yaron da ta ke shayarwa ko ita kanta, saboda hadisin da aka rawaito daga Anas Ibn Malik cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce "Hakika Allah ya dauke wa matafiya rabin sallah, kuma ya dauke azumi ga matafiyi da mai ciki da mai shayarwa saboda haka za ta ciyar ne yadda mai ciki za ta ciyar itama idan ta gagara da daukar azumin saboda ciwo ko cutuwa, wannan shi ne ra'ayin Abdullah Ibn Umar (R.A) da Abdullah Ibn Abbas (R.A.)
4. Wanda Ramadan ya riske shi alhali yana cikin ramuwar azumin Ramadan na baya:- Shima wannan zai ciyar in dai har ramuwar na wani watan yake yi. Wato kullum ya yi azumi, sannan kuma ya ciyar har ya kai adadin iya wanda ya ke ramuwar. Wannan yana ga mara lafiya ne da ya kasa ramawa har wani Ramadan din ya zo, sannan ya sami lafiya ko damar ramawa to shi ne zai yi hakan.
ABUBUWAN DA KE SA A YI KAFFARA
(1) CI KO SHA DA GANGANCI Wato wanda ya ciu ya sha daidai da yini guda alhali yana sane ba da uzuri ba to zai yi kaffara saboda Annabi (S.A.W.) ya ce "Wanda ya ci a yinin Ramadan ba tare da uzuri ba, ko azumin shekara bai isar mai ba ko da ya azumce shi." Wannan ya nuna cewar sai ya yi kaffara da niyyar kaffara sannan ya rika ci gaba da azumin, amma in har bai yi kaffara ba, to azumin shi yana nan Allah ba zai amsa ba.
(2) SADUWA DA MACE A nan ana nufin duk wanda ya sadu da mace da rana alhali yana cikin azumin Ramadan, to abin da ya kama shi, shi ne kaffara. Wala Allah matar shi ce mace ko kuwa zina ce duk kaffara ce ta hau su. Idan kuma da aure wato miji da mata, to idan har ita matar da izininta ya sadu da ita da rana, to ita ma sai ta yi kaffara, kamar yadda shima zai yi. Haka nan dai dai ne ya fitar da maniyyi ko bai fitar ba, sai dai ya yi kaffara da kuma yin makamancin wannan da ya shafi zuwar wa namiji ko mace ta je wa mace. Wannan duk kaffara ta hau su kuma zunuban su ababen ninkuwa ne matukar ba su tuba ba.
(3) MACEN DA JINI YA DAUKEWA TA KI YIN AZUMI Duk macen da jini ya dauke mata, gabanin fitowar alfijir, kuma tana da masaniya a game da hakan to wajibi ne a gareta ta yi azumi idan kuma ta sha ta ki ta yi to kaffara ce a kanta. Domin dalilinta na jini ne kuma ya dauke.
YADDA KAFFARA TAKE Kaffara dai ita ce tuba daga wani laifi da ka yi wa Ubangiji ta hanyar yin kyakkyawar ibada. Tare da niyya ta ramuwa da kaffara. (1) Ana yin azumi sittin: Wato na wata biyu, amma ana cika wa da talatin-talatin, kwanaki sittin kenan. Da kuma ramuwar wanda aka fara azumin a cikin yinin shi ne sittin da daya kenan.
(2) Sai kuma hanyar ta biyu ita ce ta ciyarwa: Wato za a ciyar da mutane miskinai guda sittin da mudu-mudu ko wanne daya ko kuma a basu abinci dafaffe wanda zai ishi kowane ya koshi, daidai gwargwado. Haka kuma za a iya tufatar da su da riga da wando ko wannen su ga wanda Allah ya wadata zai iya yin hakan.
(3) Hanya ta uku ita ce 'yanta bawa: Ana 'yanta bawa guda daya shi kenan an yi kaffara. Sai dai tunda yanzu ba lokacin taskance bayi ba ne, to dole dai sai dai a dauki hanya ta farko ko ta biyu. Allah ya sa mu dace, amin.
ABUBUWAN DA AKA YI RANGWAME Akwai wasu abubuwa da aka yi afuwar su ga mai yin azumi, wadanda in sun faru a gare shi, to ba su karya masa Azumi ba, ba kuma su sa shi kaffara ba. Kamar:- (1) SA MAGANI Mai azumi zai sa magani matukar ba zai zarce cikin shi ba ko makogoron sa ba. Idan zai zarce makogwaronsa to an hana shi ya sa maganin domin zai karya masa azumi.
(2) YIN ASUWAKI DA RANA Mai azumi zai yi asuwaki da rana amma ba zai yi da danyen itace ba, ko makilin da sauran abubuwan da za su je mishi har makogwaro.
(3) HADIYE KURA KO KUDA, KO KWARO Haka nan in hakan ta faru an hadiye kuda ko kuma kwaro, to babu laifi ga mai Azumi.
(4) FITAR DA MAZIYYI DA FITAR DA MANIYYI TA MAFARKI, KO WAYEWAR GARI DA JANABA. Duk idan wadannan sun faru an yi rangwamensu ga mai azumi matukar dai janabar ya sameta ne kafin alfijir ya keto, haka ma maniyyi ya fito masa ne yayin da yake barci ba a farke ba wato kuma bashi ne ya kawatawa kansa mafarkin abin da zai sa ya fitar da maniyyin ba. Haka ma idan maziyyi ya fita koda a mafarkin ne, to bai karya azumi ba. Saboda dogaro da Hadisan Annabi (S.A.W.)
(5) YIN HABO DA YIN AMAI DA MAGWAS Yin habo da amai duk ba sa karya azumi, matukar dai shi amai din ba kakaro shi a ka yi ba, ko kuma an bari ya koma makogwaro ba. Haka ma magwas duk ba sa karya azumi, an yi rangwamensu ga mai azumi.
(6) WANKA DA SA TURARE Haka ma mai azumi yakan iya yin wanka matukar bai sake ya bar ruwa ya shigar masa ta kunne ba, domin ruwa yana shiga ta kunne. Haka nan ba ya shiga kogi ya yi wanka domin cewa ruwan zai shiga ta kofofin da ke jikin shi. Haka nan halal ne mai Azumi ya sa turare sosai, sai dai haramun ne ya sa wanda idan ya shaki kamshinsa zai fitar masa da hankali. Wato ya dan sa shi juyawar kwakwalwa.
(7) YIN AMFANI DA KIRFA (ABIN SHAKA) GA MAI CIWON ASMA Shima an yi rangwame cewar zai iya shakawa yayin da cutar ta taso masa. Mafi kyautatuwa dai ya ajiye azumin saboda fadin Allah madaukakin sarki cewa mara lafiya da matafiyi su ajiye azumi sa rama a kwanakin gaba.
ABUBUWAN KI GA MAI AZUMI (1) YIN SAHUR DA WURI Ba a so mai Azumi ya yi sahur da wuri. Wato tun dare kashi na farko. An fi so mutum ya yi sahur a kashin dare na uku ko na hudu haka kuma an ki so mutum ya ki tashi ya yi sahur domin Annabin Allah (S.A.W.) yana fada: "Ku yi sahur domin cewa cikin sahur akwai albarka." Bukhari ne ya rawaito. Saboda haka an fi so mutum ya jinkirta sannan ya yi.
(2) YIN SUMBA DA WASA DA RUNGUMAR MACE DA RANA An ki ga mutumin da ba zai iya mallakar kan shi ba ya yi sumba yayin da ake azumi da rana, haka nan ko tuntuni ko kallon mace ko runguma duk ba a so, duk da dai ba su karya azumi in an yi su, in har matukar ba su fitar da maniyyi ba. Abu dai mafi kyautatuwa shi ne a hakura kamar yadda malaman Fikihu suka tafi cewa idan ba za a sami salama ba wato kubuta ya haramta.
(3) SANYA KWALLI DA DANDANA ABINCI DA RANA Saboda kwalli yana shiga cikin ido, wato zai iya shigewa shi ne dalilin da ya sa malamai suka ki hakan. Dandano ba ya karya azumi ga wacce take yin girkin ko wanda yake yin girkin, sai dai zai tofar ne yayin da ya dandana saboda maganar Abdullah Ibn Abbas (R.A.) cewa: "Babu laifi mutum ya dandana abin da yake dafawa." Sai dai an ki mutum ya hadiye bayan ya dandana.
(4) YIN KAHO DA BALLI-BALLI (SHAUSHAWA) Yin kaho da Azumi da rana, yana cikin abubuwan da aka karhanta, amma idan an yi bai karya azumi ba. Haka ma balli-balli wato shaushawa sha ma an karhanta, wato ba a so mutum ya yi da rana amma in an yi, to bai karya azumi ba. Amma mafi inganta shi ne mutum ya bari sai an sha ruwa. Wato da daddare za a iya yin kaho ko balli-balli wannan shi ne mafifici.
(5) GIBA DA GULMA Ita dai giba ita ce aibata mutum da wani abu da baya so, alhali baya wajen. To an ki mai azumi ya rika yinta, da gulma, wato ka dauki maganar wani ka kai wa wani, saboda a gibace shi. Saboda haka ba a so mai azumi ya zauna a rika yin irin hakan da shi domin Annabin Allah (S.A.W.) yana cewa: "Da yawa daga masu azumi ba su da azuminsu sai dai kishirwa haka da yawa daga masu ibada tsaiwar dare ba su da lada sai dai gajiya." Ibn Majah ya rawaito.
(6) FITINA Dama ita fitina ba ta da kyau koda ba da azumi ba. To ba a so mutum ya rika tayar da ita, da kuma yin fada da wannan ko ya zagi wancan, da sauransu, domin shugaba (S.A.W.) yana cewa: "Idan mutum ya wayi gari yana mai azumi, to kada ya yi rafasu (zancen banza) Idan mutum ya zage shi ko ya dake shi to ya ce ni mutum ne mai azumi." Ruwahu Bukhari.
ABUBUWAN SO GA MAI AZUMI (1) GAGGAUTA BUDA BAKI An so ga mai Azumi ya zama yana bude baki da wuri. Ana bude baki ne da zarar rana ta fadi an kiran sallah ko ba a kira ba, in dai rana ta fadi, to za a yi gaggawar bude baki. Domin Annabin Allah (S.A.W.) ya ce "Idan ku ka ga dare ya gabato daga nan (wato rana ta fadi) hakika mai azumi ya bude bakinsa." Bukhari ne ya rawaito. Sannan kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Mutane ba za su gushe tare da alheri ba matukar suna gaggauta buda baki." Saboda haka wadannan hadisan sun zama hujja da zata nuna mana gaggauta buda baki ga mai azumi.
(2) KARATUN ALKUR'ANI DA ZIKIRI Ana son wanda yake Azumi ya zamana kodayaushe yana cikin ambaton Allah madaukakin Sarki da yawaita karatun Alkur'ani da yawaita salatin Annabi (S.A.W.)
Bayani: Wato shi mutum mai azumi saboda barcin shi ibada ne, haka kuma ibadarsa abar ninkawa ce. Shi yasa ake so ya zamanto cikin dayan wadannan, wato ko dai ya zamana mai yawan ibada ta fuskar karatun Alkur'ani ko zikiri ko salatin Annabi. Ko kuma in bai sami dama ba, to yin barcinsa ya fiye masa da yawan surutu mara amfanarwa. Ko sabo ko zage-zage ko giba (cin naman dan uwansa). Saboda haka kame bakinsa daga hakan shi ne ya fi.
FALALAR WATAN RAMADAN 1- Falalar watan Azumi da yin azumin watan Ramadan, tana da yawan gaske. Kamar yadda ya zo cikin Risala cewa “Wanda ya tsaya (Ramadana) yana mai imani mai kyautata aiki an gafarta mai abinda ya gabata na daga zunuban shi." Haka kuma Allah madaukakin sarki ya ce cikin hadisi Kudusi “Dukkan aikin dan Adam nasa ne (wato Mala'iku ne suke rubuta ladan shi) amma azumi na Allah shi yake saka wa bawa dashi."
2- Haka kuma Annabi (S.A.W.) ya ce da Jabir Ibn Abdullah "Ya Jabir wannan wata na Ramadana ne duk wanda ya azumci yininsa, sannan ya mika da ibada da darensa, ya kiyaye aikinsa da farjinsa, sannan kuma ya kiyaye harshensa, to ya fita daga cikin zunubi kamar yadda yake fita daga watan.”
3- Annabi (S.A.W.) ya ce "Hakika watan azumi wata ne mai girma, Allah yakan rubanya kyawawan aiki a cikinsa, kana kuma ya shafe munana. Ya kuma daukaka darajoji. Duk wanda ya yi sadaka a cikin Ramadan Allah zai gafarta masa, haka nan kuma duk wanda ya kyautata, Allah zai gafarta masa, haka nan kuma duk wanda ya kyautata wa abinda hannun damarsa ya mallaka (bayi) a cikin watan, Allah zai gafarta masa, haka nan ma duk wanda ya kyautata ayyukansa a cikin watan, Allah zai gafarta masa, haka kuma wanda ya hadiye fushinsa a cikin watan Allah zai gafarta masa. Wanda ya sada zumunci Allah zai gafarta masa."
4- Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Hakika wannan wata na ku (na Ramadan) ba kamar sauran watanni yake ba don shi idan ya zo muku yana zuwa ne da albarkoki da kuma rahama idan kuma zai fita, yakan tafi ne da zunubanku da kuma yi muku gafara."
5- Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Mafi girman aiki kamewa daga abubuwan da Allah ya haramta." Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Idan Ramadana ya zo, ana bude kofofin aljanna, ana kulle kofofin wuta, haka nan ana daure shaidanu."
6- An tambayi Annabi (S.A.W.) cewa "Mene ne yake nisanta shaidan daga garemu? Sai (S.A.W.) ya ce "Azumi don Allah yakan bakanta fuskarsa, sadaka kuwa takan karya kashin bayansa. Haka nan kuma soyayya don Allah da kuma ayyukan kwarai sukan lalata asalinsa. Haka kuma neman gafara yakan yanke jijiyar jininsa."
7- Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Duk wanda ya azumci watan Ramadana, ya kiyaye farjinsa da harshensa, ya kuma kiyaye cutar da mutane to Allah zai gafarta masa zunubansa, wanda ya yi da wanda ya jinkirta ya kuma 'yantar dashi daga shiga wuta, ya kuma halatta masa gidan aljanna."
8- Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Watan Ramadan wata ne da Allah ya wajabta muku yin azuminsa, duk wanda ya azumce shi yana mai imani da burin samun lada, za a shafe masa zunubinsa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi."
9- Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Babu wani mumini da zai azumci watan Ramalana don neman lada face Allah madaukakin sarki ya wajabta masa abubuwa guda bakwai. Sune;- zai fitar da haramun din da ke jikin shi. Ba za a nisanta shi da rahamar Allah ba. Zai kasance ya yi kaffara ga zunuban shi. Allah zai saukaka masa zafin mutuwa. Allah zai kiyaye shi daga yunwa da kishirwa ranar alkiyama, Allah zai kare shi daga wuta. Allah zai ciyar da shi abincin aljanna."
10- Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Mai azumi yana cikin ibada ne ko da kuwa yana barci ne a kan gadonsa, matukar dai bai ci naman (giba) Musulmi ba."
11- Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "A aljanna akwai wata kofa da ake kira Rayyan, babu wanda zai shiga (aljanna) ta wannan kofar sai mai azumi."
12- Haka kuma an karbo daga Mu'ada Ibn Jabal (R.A.) ya ce: Hakika Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: "Shin ba na nuna maka kofofin alheri ba, sai ya ce "e" Ya Manzon Allah (S.A.W.) sai ya ce "Azumi garkuwa ne."
13- Abu Hurairah ya rawaito cewar Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Warin bakin mai azumi ya fi turaren miski kamshi a wurin Allah."
Abu Sa'ad Kudri ya rawaito cewa, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce "Lallai Allah madaukakin sarki yana da wadanda yake 'yantawa a cikin yini da dare (watan Ramadan) kuma ga kowane Musulmi a cikin kowane dare (akwai) addu'a wacce ake karba."
DAREN LAILATUL KADRI Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Hakika mu muka saukar da shi Kur’ani a cikin dare mai alkadari. "To me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Kadri." Lailatul kadri ya fi watanni dubu. Mala'iku da Ruhu (Mala'ika Jibril) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umarni. "Sallama (aminci) ne shi daren, har fitar alfijir (K97:1-5) A wannan dare na Lailatul kadri ne Allah madaukakin sarki ya saukar da dukkan Alkur'ani mai girma gaba dayansa daga Lauhil Mahfuz zuwa ga zuciyar Manzon Allah (S.A.W.) Allah (S.T.A.) yana fadi cewa: "Hakika mu muka saukar da shi a cikin dare mai albarka..." Wannan dare kuwa shi ne daren Lailatul Kadri. To sai dai kuma daga baya Mala'ika Jibril ya rika kawo wa Manzon Allah (S.A.W.) ayoyin Alkur'anin a hankali a hankali har cikin shekaru 23.
To amma kuma yana da kyau a fahimci cewa ba wai farkon saukar Alkur'ani daren Lailatul Kadri bane. Ko kuma wai an saukar da wasu ayoyin Alkur'anin daren Lailatu Kadri ba ne, don kuwa idan har haka ne, to wace falala wannan dare yake da shi kenan a kan sauran darare tunda suma an saukar da wasu ayoyin ma a cikinsu. Haka nan ba wai an saukar da surar "Inna Anzalnahu" ba ce a wannan dare, saboda fadin Allah madaukakin sarki cewa: "Hakika mu mun saukar da shi." Don lamarin "shi" din yana komawa ne ga Alkur'ani ba wai ga ita kanta surar ko wata aya ta cikinta ba ne. Don haka saukar da Alkur'ani gaba daya ne a ka yi a cikin ta daga Lauhul Mahfuz zuwa sama ta hudu kana daga baya kuma aka rika saukar da ayoyin kadan-kadan gwargwadon abin da ya faru a lokacin.
MA’ANAR LAILATUL KADRI An sanyawa wannan daren sunan Lailatul Kadri ne don shi ne daren da Allah madaukakin sarki yake kaddara abubuwa, yake kaddara abubuwan da za su faru cikin shekara na daga rayuwa da mutuwa, alheri da sharri, arziki, haihuwa da dai sauransu. Muna iya tabbatar da hakan kuwa ta fadin Allah madaukakin sarki cewa. "A cikinsa ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima. Al'amari ne daga wurinmu, hakika mu mun (kasance) masu aikowa ne. Wata rahama ce daga Ubangijinka, hakika shi ne mai ji masani." Don haka "Raba al'amari mai hikima" yana nufin kaddara al'amura da dukkan abubuwan da suka kunsa da kuma tabbatar da su a wannan dare mai albarka daga Allah madaukakin sarki zuwa ga bayinsa. Sannan kuma a kan ce al-kadr: da ma'ana matsayi a kan ce masa wato (daren) "Lailatul Kadri" saboda muhimmanci da kuma matsayinsa da kuma dacewar masu ibada a cikinsa, wato raya shi da ibadu da ayyukan alheri, shi ya sa zai fi sauran ayyukan mutum lada da ya yi su cikin darare dubu wadanda ba na daren Lailatul Kadari ba.
AYYANA DAREN LAILATUL KADARI Annabi (S.A.W) ya yi nuni da cewa mu nemi daren Lailatul Kadri a goman karshen na Ramadan. Kenan tun daga kwanakin (21) zuwa (29) ko zuwa (30) amma an fi sa rai a (27) Da yawa daga malamai sun tafi a kan hakan, domin an tambayi Iman Abu Abdullahi (A.S.) kan Lailatul Kadri sai ya ce: “Ku neme shi cikin daren 19, 21, da 23." wasu kuma suna ganin ana dacewa da wannan dare ne cikin daren 27. Abin da dai ake so shi ne dukkan dararen goma ko tara mutum ya yi ta ibada har Allah ya sa ya dace. Kuma duk wanda ya riski daren Allah yana gafarta masa, yana wajabta masa aljana ana amsar addu'ar shi a wannan lokacin kuma akwai mala'iku da Allah yake saukarwa a wannan dare su zo duniya suna nema duk wanda suka riska yana ibada gafara da amincin Allah. Kuma lallai shaidan yana buya cikin wannan dare ba ya fitowa. Albarka da ni’imomin Ubangiji sukan sauka a wannan dare, haka nan kuma yakan kare mutum daga dukkan sharrorin da wani ya nufe shi da su da sauransu.
ITTIKAFI Ittikafi shi ne zama a cikin masallaci da niyyar ibada, tsawon dogon lokaci, wato dare da yini a mafi karanci. Ittikafi shi ne kebantakar da kai da yawan ibada wajen da aka tanada domin ittikafin kuma sunna ne.
Ittikafi dai sunna ce ta Annabi kamar yadda sauran sunnoni suke. Wato ya kasance yana yin ta a rayuwar shi har yayin da Allah ya kawo wafatin sa, sai kuma iyalansa suke yi kamar yadda hadisi ya zo da hakan.
YADDA AKE ITTIKAFI LOKACIN SHIGA Ana shiga Ittikafi yayin da dare ya shigo wato bayan sallar Isha'i, sai a yi sallar Asubahi a ciki. Wannan ita ce fahimtar Iman Maliki da almajiran Malikiya. Yayin da wasu suke ganin ana shiga ne bayan fitowar alfijir in an yi sallar Asubahi. Wasu kuma suke ganin ana shiga ne kafin fitowar alfijir kamar yadda mafi yawan malamai kowa ya fahimci hadisin da aka rawaito daga Aisha, Allah ya kara yarda a gare ta, cewar:- "Annabi (SAW) idan ya yi nufin shiga Ittikafi sai ya sallaci Asubahi kana ya shiga." Mai Raisala ya tafi cewa a shiga kafin faduwar rana.
MAI SHIGA ITTIKAFI Shi ne mutum Musulmi mai hankali, wato wanda zai iya mayyazewa . Mai Ittikafi sai ya zama yana Azumi ko da na nafila ne, in ya zama ba lokacin watan Ramadan ba ne, ba za a shiga ba. Namiji babba ko yaro, mace duk za su iya shiga Ittikafi.
MASALLACIN DA AKE ITTIKAFI Ana yinsa ne a masallaci wanda yake jami'i wato wanda ake yin sallar Juma'a a cikin shi saboda shi mai Ittikafi ba a son ya fita ba tare da uzuri ba. In har akwai masallacin Juma'ar.
ABUBUWAN DA KE SA MAI ITTIKAFI FITA Mai Ittikafi ba zai fita ba, ba tare da uzuri ba, uzurin shi ne kamar in ya sami rashin lafiya zai fita idan ya sami sauki a lokuta kalilan to sai ya dawo ya ci gaba. Fita domin bukatar mutuntaka kamar bayan gida, bawali, wanka. Idan mace tana ciki haila ta zo mata, itama za ta fita sai ta yi tsarki sai ta dawo.
ABUBUWAN DA ITTIKAFI KE HANAWA Akwai abubuwan da mai Ittikafi ba zai yi su ba sune kamar:- (1) Jima'i da daddare ko sumba ko rungumar mace duk ba zai yi su ba ko da daddare ne. (2) Ba zai fita dubo mara lafiya ba, haka bai fita a kan sallar jana'iza ba. (3) Ba zai rika hira da 'yan uwanshi na Ittikafin ba. (4) Ba zai shagaltu da wani ilimi daban sabanin ibada ba.
ABUBUWAN DA AKA YI RANGWAME GA MAI ITTIKAFI (1) Zai iya zama limami a sallah a masallacin. (2) Zai iya yin aure alhali yana Ittikafi in ya kare ya tare da matar. (3) Zai iya daurawa wani aure in an bukaci hakan, amma da wasu sharadin idan a cikin masallacin za a daura auren.
ADADIN KWANAKIN ITTIKAFI Ana zama a masallaci mafi yawanci kwanaki sune kwanaki goma kamar yadda ya gabata cewa Manzon Allah (S.A.W.) yana shiga ne a goman karshe. Amma ana yin na kwanaki uku, hudu, shida, bakwai. Amma dai mafi karanci yini da kwana.
LOKACIN DA AKE FITA DAGA ITTIKAFI Mai Ittikafi in da watan Azumin Ramalana ne, to an so ya fita da Asubahin kwanakin karshe yayin da wata ya yi kwana talatin. Wasu malaman sun ce kada ya koma gida har sai ya isa ga masallacin Idi ya yi sallar Idi, idan watan Ramadan ne. Idan kuwa ba watan ba ne to an so ya shiga ranar Juma'a ya fito da asubahin karshen kwanakin da ya debar wa kanshi. Haka ma idand na bakance ne to shima sai ya cika adadin da ya yi bakancen sannan ya fito, kuma ba zai yi ittikafin ba sai matukar ya dauki azumi ko da na nafila ne a jere.
AYYUKAN DA AKE SO MAI ITTIKAFI YA HIMMANCI DA SU Yana a gare shi, ya himmanci da yawaita ibada ta fuskar yawaita nafila, ko salatin Annabi (S.A.W.) yawaita karatun Alkur'ani, zikirin Allah (S.T.A.) da sauran su. An kyamaci yawan surutu cikin abin da bai amfanarwa, yawan barci da sabon Allah ta kallon mata ko lura da mata duk an kyamata da cin naman mutane ko gulma, duk haramun ne ga mai Ittikafi.
ABUBUWAN DA KE BATA ITTIKAFI
Abubuwan da yake bata Ittikafi sune:-
(1) Mutum ya shiga bada Azumi ba wato ya ci ya sha da rana, to wannan ya bata Ittikafin.
(2) Karyarwar Azumi, idan Azumi ya karye to Ittikafi ya baci. Sai dai a daura in an dawo.
(3) Saduwa da mace: Saduwa da mace da daddare ya bata Ittikafi in da rana ne ma to ya bata azumi.
(4) Sumba da runguma: Sumbatar mace in da rana ne to ya bata Ittikafi amma bai bata Azumi ba, (amma in har ba a zubar da maniyyi ba).
Da daddare kuma nan ma ya bata Ittikafi.
(5) Fita ba tare da uzuri ba: Fita ba tare da uzuri ba ya bata Ittikafi.
Babu aminci ga me Ittikafi ya je da rediyo ya rika saurara, ko kuma ya je da waya (handset) ya rika kiran mutane suma suna kiran shi. Duk wannan haramun ne kuma babu wata madogara ta a yi hakan.
ZAKKAR FIDDA KAI (1) Zakkar fidda kai ita ce wacce ake yin ta yayin da aka kare azumin farilla na Ramadan kuma sunna ce wacce take mai karfi, Annabi (S.A.W.) ya fara illata a bisa Musulmai. Domin an karbi hadisi daga dan Umar ya ce: "Annabi (S.A.W.) ya farillanta zakkar fidda kai sai na dabino ko sa'i na sha'ir. A bisa bawa, da, namiji mace, karamin yaro, babban mutum Musulmai, ya yi umarni da ita cewa a bayar da ita kafin. Fitowar mutane zuwa wajen sallah Idi." Bukhari ne ya rawaito shi.
(2) Ana fitar da ita kwano-kwano ga kowa, uba shi ne yake fitar wa 'ya'ya da mataye da kadimin gida in yana da halin hakan. Idan kuma bai da halin hakan to sai da ya fitar wa da iyaye, in har shi yana da halin hakan amma dole ce a bisa kan kowa. Shugaban bawa, to shi ne zai fitar masa matukar dai Musulmi ne shi bawan, ko kadimin wato yaron gida.
(3) Ana bayar da mafi rinjayen abincin da mutane gari suke amfani da shi, idan mutanen gari sun fi amfani da shinkafa to sai a fitar da ita, in kuma masara ce, to in kuma dawa ce, to ita. Amma an fi bayar da abin da ka san shi ka ke ci. Kamar in kana cin shinkafa to sai ka bayar da ita, in kuma masara ko dawa ce ko wake ko alkama ko fulawa ce, to sai ka fitar da shi. Amma ba ka na cin masara ba ko shinkafa sannan kuma ka dauki dawa ka fitar da ita ba. In hakan ya faru, to ta isar masa amma bai kyautata ba.
Haka wanda ya sami damar ya kara bisa kwano guda, to ya yi hakan. Hikimarta: Don wanda bai da abinci, to shima ya samu ya yi ya ci kyakkyawan daga irin yadda karfin shi bai kai ba. Shima ya sa tufafi mai kyau ya ci abincin sallah.
SALLAH TARAWIH (ASHAM) DA TAHJUDDI Sallah Tarawihi wacce ake cewa sallar Asham, nafila ce ba farilla ba, kuma sunna ce wacce Annabin Allah (S.A.W.) ya fara yinta tun a zamaninsa, har ma ya nuna cewar sunna ce ba Farilla ba. Kuma sallah tana da matukar falala ta yinta, kuma ana so mai azumi ya rika yinta. Ana fara yinta daren farko da aka ga watan Azumin in hakan ya samu. In kuma bai samu ba, to dare na biyu wato daren da aka fara kai azumin farko. Ana yin raka'o'i takwas (8) ko goma (10) ko goma sha daya hade da Shafa'i da Wutri ko sha uku (13) ko kuma Asham (20) ko 21 har da Shafa'i da Wutri. Duk dai nafila ce gwargwadon iko mutum yake yinta. Wannan sallah ana iya yinta a gida mutum daya ko jam'i, haka ma masallaci in an gama sallar Isha'i ana iya yinta a jam'i. Amma tunda nafila ce ta fi lada a yi ta a gida. Ana yinta a jam'i ne domin tsoron kada mutum ya kasa yinta in ya je gidan. Kuma wannan sallah wanda ba sa yinta, su daure su rinka yinta domin Annabi Allah (S.A.W.) shi ya kwadaitar da a yi ta kuma tana da falala sosai.
SALLAR TAHJUDDI Sallar Tahjuddi itama sallah ce ta nafila wacce ake yinta da daddare wato karshen dararen goman karshe in an yi azumi ashiri (20). Kuma ana sauke Alkur'ani ne a cikinta, amma ga wanda bai haddace ba yakan iya daukar Kur'ani ya rika karantawa, har ya gama. Itama an fi so mutum ya yi ta a gida don gudun riya da jan ra'ayi da tsoron dare da fitinar mata. Amma in an yi ta a masallaci to ta inganta.
SALLOLIN WATAN AZUMI
(1) DARE NA FARKO
An karbo daga Anas Dan Malik, Allah ya yarda dashi cewa Manzon Allah (SAW) yana cewa duk wanda ya yi sallah a daren farko na Ramadan ya yi sallah raka'a (10) sallama (5) A cikin kowacce raka’a ya karanta:-
1- Fatiha kafa daya (1)
2- Inna Anzalnahu kafa (2)
3- Kul Ya Ayuhal Kafiruna kafa (2)
4- Kulhuwallahu kafa (2)
5- Idan ya gama sai ya karanta (YA HAYYU, sau 100)
FALALA: Allah zai haramta namansa daga wutar jahannama kuma Allah zai gafarta maza zunubansa, kuma duk abin da ya roki Allah a lokacin zai biya masa da bukatarsa.
(2) DARE NA BIYU Duk wanda ya yi sallah raka'a shida (6) sallama uku (3) kuma ya karanta:- 1. Fatiha kafa (1) 2. Inna a'adaina kafa (5) 3. Bayan ya gama sai ya karanta (YA KAYYUMU, sau 100) FALALA: Ba zai tashi daga wurin da yake a zaune ba face sai Allah ya gafarta masa zunubansa, kuma Allah ya rubuta masa irin ladan wanda ya yi Hajji da Umra.
(3) DARE NA UKU Duk wanda ya yi sallah raka'a shida (6) a dare na uku ya yi sallama uku (3) yana karanta:- 1- Fatiha da Inna Anzalnahu kafa (1) 2- Kul ya ayyuhal kafiruna (4). 3- Bayan ya gama sai ya karanta (YA RAHIMU, sau 100) FALALA: Zai samu lada kamar wanda ya 'yanta kuyanga dubu kuma kamar wanda ya ciyar da mai jin yunwa dubu.
(4) DARE NA HUDU Duk wanda ya yi sallah raka'a hudu (4) a cikin dare na hudu na azumi ya karanta:- 1- Fatiha da (Kul Ya Ayyuhal Kafiruna) kafa (3) 2- Sannan sai ya karanta (YA WAHHABU, sau 100) FALALA: To ba zai tashi daga inda ya ke ba sai Allah ya gafarta masa zunubansa sannan kuma Allah ya bashi ladan irin mutanen da suke tsananin tsoron Allah.
(5) DARE NA BIYAR Wanda ya yi sallah a dare na biyar, ya sallaci raka'a takwas (8) yana mai karanta:- 1- Fatiha kafa (1) 2- Alam Nashraha kafa (1) 3- KULHUWALLAHU kafa (3) 4- Sai ya karanta (YA SAMADU, sau 100) FALALA: To Allah zai rubuta shi a cikin kubutattu daga wuta, kuma kubutattu daga munafukai kuma Allah ya rubuta masa ladan wanda ya yi Hajji da Umara.
(6) DARE NA SHIDA Duk wanda ya yi sallah a dare na shida ya karanta:- 1- Fatiha 2- KULHUWALLAHU kafa 11 3- Sannan ya karanta (YA WASI'U sau 100) FALALA: To zai sami ladan wanda ya yi raka'a dubu a masallacin Harami.
(7) DARE NA BAKWAI Duk wanda ya yi sallah raka'a bakwai (7) ya karanta:- 1- Fatiha da Kul Ya Ayyuhal Kafirun ka (7) 2- Kulhuwallahu kafa (7) 3- Sannan sai ya karanta (YA MUTA'ALIN, kafa 100) FALALA: To zai sami kwatankwacin ladan wanda ya yi sadaka da dinari dubu.
(8) DARE NA TAKWAS Wanda ya sallaci raka'a biyu (2) a dare na takwas ya karanta:- 1- Fatiha da Kulhuwallahu (sau 12) 2- Sannan ya karanta (YA RAZZAKU, sau 100) FALALA: To zai sami ladan adadin haruffan da ya karanta a cikin sallar, kuma zai sami ladan wanda ya ciyar da al'ummar Manzon Allah.
(9) DARE NA TARA Wanda ya sallaci raka'a takwas (8) a dare na tara yana mai karanta:- 1- Fatiha da Tabbatyada kafa (3) 2- Kulhuwallahu (3) 3- Sannan sai ya karanta (YA MALIKU, sau 100). FALALA: Allah zai ba shi irin ladan masu hakuri, kuma za a ba shi ladan irin wanda ya sauke Alkur'ani kuma za a ba shi ladan ibadar shekara (70).
(10) DARE NA GOMA Wanda ya sallaci raka'a hudu (4) yana mai karanta:- 1- Fatiha da Ayatul Kursiyyu kafa (1) 2- Inna Anzalnahu kafa (1) 3- Kulhuwallahu kafa (13) 4- Sannan sai ya karanta (YA LADIFU, 100) FALALA: To ba zai tashi daga bijirensa ba face sai wani mai kira daga sama ya yi kira yana mai cewa “ya kai wannan bawa nawa na gafarta maka dukkan zunubanka.” kuma Allah zai rubuta masa ladan shahidai saba'in (70)
(11) DARE NA SHA DAYA Sai ka sallaci raka'a hudu (4) ka karanta:- 1- Fatiha da Inna Anzalnahu kafa (17) 2- Idan ka yi sallama sai ka ce (LAHAULA WALAKUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYUL AZIM, kafa (70) Sai ka yi salati ga Manzon Allah (SAW) 3- Kuma ka karanta (YA GAFURU 100) FALALA: To Allah zai gafarta maka zunubanka.
(12) DARE NA SHA BIYU A dare na sha biyu sai a sallaci raka'a goma (10) a karanta:- 1- Fatiha da Kulhuwallahu kafa (6) 2- Sannan sai ya karanta YA HALIMU (100) bayan ya gama sallar. FALALA: To Allah zai gina masa wani bene a cikin aljannah.
(13) A DARE NA SHA UKU A cikin wannan daren ana yin raka'a biyu (2) sai a karanta:- 1- Fatiha da Kulhuwallahu kafa (5). 2- Bayan an gama sallar sai a karanta (YA SAMADU, 100) FALALA: To Allah zai bashi ladan wanda ya yi sallah raka'a dubu (1000) kuma ya yi azumin shekara (20) kuma Allah zai bashi littafinsa da hannun dama.
(14) A DARE NA SHA HUDU A cikin daren sha hudu (14) ana yin sallah raka'a (10) a kara da:- 1- Fatiha da izaja'a kafa (7) 2- Bayan an idar sai a karanta (YA TAUWABU, sau 100) FALALA: Allah zai bashi irin ladan wanda ya yi sadaka da dinari dubu kuma ya 'yanta kuyanga dubu (1000).
(15) A DARE NA SHA BIYAR A cikin wannan daren ana yin raka'a shida (6) sannan a karanta:- 1- Fatiha da Izaja'a kafa (1) 2- Kulhuwallahu kafa (35) 3- Sannan idan ya yi sallama sai ya karanta YA'AZIZU, 100) FALALA: Allah zai musanya masa miyagun ayyukansa izuwa kyawawa, kuma Allah zai karbi azuminsa da sallar sa.
(16) A DARE NA SHA SHIDA A cikin wannan daren ana yin raka'a goma (10) ne sai a karanta:- 1- Fatiha da Izazulzilati kafa (10) 2- Bayan an gama sai a karanta YA HASIBU (100) FALALA: Allah zai gafartawa mutum zunubansa.
(17) A DARE NA SHA BAKWAI A cikin wannan daren ana yin sallah raka'a goma (10) sai a karanta:- 1- Fatiha da Inna Anzalnahu kafa (2) 2- Kulhuwallahu kafa (2) 3- Bayan ya gama sai ya karanta YA BADINU (100) FALALA: Allah zai bashi irin ladan mutanen da suka yi imani da Allah tun daga Annabi Adam har zuwa ranar alkiyama.
(18) A DARE NA SHA TAKWAS A cikin wannan daren ana yin sallah raka'a (12) sai a karanta:- 1- Fatiha da Suratul A'ala kafa (1) 2- Kulya kafa (1) 3- Bayan an gama sallar sai a karanta (YA NURU, sau 100) FALALA: Duk wanda ya aikata wannan sallar, Allah zai bashi babban birni a gidan aljanna.
(19) A DARE NA SHA TARA A cikin wannan daren ana yin sallah raka'a shida (6) sannan sai a karanta:- 1- Fatiha da Kulhuwallahu kafa (7) 2- Sai ya karanta YA HADI kafa (100), bayan ya gama sallar. FALALA: Allah zai 'yanta shi daga wuta, kuma Allah ya kare shi daga cutar hauka da kuturta.
(20) A DARE NA ASHIRIN A cikin wannan daren ana yin raka'a (10) sai a karanta:- 1- Fatiha da Inna Anzalnahu kafa (1) 2- Kulhuwallahu kafa (3) 3- Bayan ya gama sai ya karanta (YA SHAHIRU, sau 100) FALALA: Zai samu gafarar tsohon zunubinsa da kuma sabo.
(21) A DARE NA ASHIRIN DA DAYA Ana yin raka'a hudu (4) a cikin wannan daren sai a karanta:- 1- Fatiha da Kulhuwallahu kafa (11) 2- Bayan sallama sai ya karanta (YA HADI, sau 100) FALALA: Zai samu ladan kamar wanda ya ciyar da mutanen duniya, kuma zai bar duniya ba tare da zunubi ba.
(22) A DARE NA ASHIRIN DA BIYU Sai a sallaci raka'a biyu (2) a karanta:- 1- Fatiha da Suratul A'ala (Sabbih) kafa (1) 2- Inna Anzalnahu sau (3) 3- Kulhuwallahu (3) 4- Falaki da Nasi uku-uku (3-3) 5- Bayan ya gama sai ya karanta (YA SHAHIDU, sau 100) FALALA: Allah zai gina wa mutum gida a cikin aljanna, kuma zai zo ranar Alkiyama fuskarsa tana haske kamar wata.
(23) A DARE NA ASHIRIN DA UKU Ana yin raka'a hudu (4) a cikin wannan dare a karanta:- 1- Fatiha da Izaja'a kafa (5) 2- Kulhuwallahu kafa (5) 3- Bayan an gama sallar sai ya karanta (YA HADI, sau 100) FALALA: Allah zai gafarta masa zunubansa, kuma zai sami jin dadi a cikin kabarinsa, kuma zai tsallake siradi kamar walkiya.
(24) A DARE NA ASHIRIN DA HUDU Sallah Raka'a hudu (4) ake yi a cikin wannan daren, a karanta:- 1- Fatiha Kulhuwallahu kafa (6) 2- Falaki da Nasi shida-shida (6-6) 3- Bayan sallama sai ya karanta (YA SHAHIDU 100) FALALA: Allah zai karbi azumin ka da sallar ka, kuma za a samu aminci a ranar Alkiyama, kuma Allah zai ba ka littafinka a hannun dama.
(25) A DARE NA ASHIRIN DA BIYAR Ana yin raka'a takwas (8) tare da karanta:- 1- Fatiha da Kulhuwallahu kafa (4). 2- Bayan sallama sai ya karanta (YA WAHIDU 100) FALALA: To Allah zai gafarta masa zunubansa tun kafin ya tashi daga inda ya ke, kuma zai kubuta daga azabar Allah.
(26) A DARE NA ASHIRIN DA SHIDA Ana yin raka'a shida (6) ne a cikin wannan daren a karanta:- 1- Fatiha da Alkari'atu kafa (1) 2- Kulhuwallahu kafa (5) 3- Idan ya gama sallar sai ya yi Istigfari (25) 4- Sai kuma ya karanta (YA MUMINU, sau 100) FALALA: Zai samu lada a gurin Allah adadin taurarin sama kuma zai shiga aljanna tare da Annabawa da Shahidai da Saddikai.
(27) A DARE NA ASHIRIN DA BAKWAI Raka'a goma sha biyu (12) ake yi a cikin wannan daren, sai a karanta:- 1- Fatiha da Inna Anzalnahu kafa (10) 2- Bayan ya idar da sallar sai ya karanta (YA RA'UFU) FALALA: To Allah zai bashi irin ladan da ya bawa Annabi Musa, kuma zai sami lada adadin duk wata halitta da hasken rana ya kai gareta.
(28) A DARE NA ASHIRIN TAKWAS Ana yin sallah raka'a hudu (4) sai a karanta:- 1- Fatiha da Kul Ayyu, da Kulhuwallahu kafa sha dai-dai (11) 2- Idan ya yi sallama sai ya yi istigfari (100) salati (100) sannan ya karanta (YA ALIMU, kafa 100) FALALA: Wannan zai zama kaffararsa na zunuban da ya yi a cikin watan azumi.
(29) A DARE NA ASHIRIN DA TARA Raka'a shida (6) za a yi a cikin wannan daren a karanta:- 1- Fatiha da Kulhuwallahu kafa (20) 2- Bayan sallama sai ya karanta (YA RAHIMU) FALALA: Allah zai gina masa bene guda (70) a gidan aljanna.
(30) A DARE NA TALATIN Idan wata ya zama mai talatin to sai a yi sallah raka'a hudu (4) a karanta:- 1- Fatiha da Kul Ya Ayyu kafa (5) FALALA: Allah zai tserar dashi daga siradin kuma ya kubutar dashi daga barin shiga wuta.
KAMMALAWA
LADUBBAN AZUMI
Akwai ladubban da ya kamata mai azumi ya kiyaye domin cikar kamalar azumin, shi ne:
(1) KIYAYE HARSHE
Ya zo a cikin wani Hadisi Manzon Allah (SAW) yana cewa duk mai azumin da bai daina yin karya ba to Allah ba ya bukatar azuminsa don haka ya ci gaba da cin abincin sa da kuma shan ruwansa.
(2) Manzon Allah (SAW) yana cewa, idan dayanku zai buda baki to ya fara cin dabino domin shi dabino akwai alheri a cikinsa, idan kuma bai samu dabino ba to sai ya fara shan ruwa.
(3) An so idan mai azumi zai buda baki ya karanta wannan addu'ar. ذهب الظمأ وابتلت العروق وثبت الأجر إن شاءاللة Tarjama “Zahabazzama'u Wabtalla Til'uruku Wasabatil, Ajru In Sha Allah.”
(4) GAGGAUTA BUDA BAKI Manzon Allah (S.A.W.) ya ce alheri ba zai gushe a gurin mutane ba matukar suna gaggauta buda baki.
(5) SAHUR Sahur yana daga cikin ladubbamn da ake son mai azumi ya kula dashi, domin manzon Allah (SAW) yana cewa “Ku yi sahur domin a cikin sahur akwai albarka.”
(6) CIYAR DA MAI AZUMI Yana daga cikin ladubban azumi shi ne ciyar da mai azumi domin samun rahamar Allah, Manzon Allah (SAW) yana cewa. Dukkan wanda ya ciyar da mai azumi to za a bashi lada irin ladan da shi mai azumin ya samu ba tare da an rage wa shi mai azumin ladansa ba.
ABUBUWAN DA YA KAMATA MAI AZUMI YA KIYAYE DASU. Ya dan uwana Musulmi ka sani fa Allah madaukakin sarki shi ne ya wajabta mana yin azumi don haka sai mu kiyaye wasu abubuwa domin cikar kamalar azumin mu. (1) Abu na farko da ya kamata mai azumi ya kiyaye dashi shi ne sallah, domin ita ce babbar ginshikin addinin Musulunci, kuma kin yin sallah kafirci ne. (2) Yana da kyau mai azumi ya kasance mai kyawawan halaye, ya nisanci aikin kafirci da fasikanci da zagin dan uwansa Musulmi da mummunar magana ga sauran al'ummar Musulmi. (3) Kar ka zama mai furta yasassar magana ko da kuwa hira ta yi dadi, sai azumin ka ya tozarta, domin Manzon Allah yana cewa idan dayanku ya dauki azumi to kada ya fadi maganar banza kada ya aikata fasikanci kada ya yi husuma da dan uwansa, idan ma wani ya zageka to ka ce dashi kai azumi ka ke. (4) An so ga mai shan taba da ya bar shanta a cikin watan azumi. (5) Kada ka zama mai almubazzaranci da abinci domin almubazzaranci halin shaidan ne. (6) Ba a son tsawaita hida a cikin dare, domin ana son ka tashi ka yi sahur. (7) Ka yawaita sadaka a cikin watan azumi kuma ka ciyar da mabukata. (8) Ka yawaita ambaton Allah da karatun Alkur'ani, tare da fahimtar ma'anoninsa.