Abubakar Ishaq Hussain sabon edita kuma mai koyo a Hausa Wikipedia Fannin girke girke Ga yanda zamu hada yogot a gidajen mu cikin sauki kamar haka.


Da farko zaki samu roba meh murfi da zaki hada yoghurt dinki a ciki,sannan ki zuba madara seh ki kawo ruwa kofi 5 ki zuba a Kai ki juya sosai ya zama ba gudaji.Seh ki dora sauran ruwan kofi 5 a kan wuta ya tafasa.

Idan ruwan ya tafasa se ki zuba shi cikin Madarar da Kika dama ki juya ki barshi ya Dan huce dai dai yadda zaki iya saka dan yatsan ki a ciki ki iya rike shi Kamar second 8 ba tare da kinji yayi zafi baza ki iya barin yatsan a ciki ba.wato abin da ake so dai kada ya cika zafi Kuma kar yayi sanyi sosai da dumin shi.Seh ki kawo wannan kindirmo ko yoghurt ki zuba a ciki ki juya seh ki rufe da murfin,sannan Ki rufe da kitchen towel ki saka a oven ko waje meh dumi ya samu Kamar awa 5 zuwa 8.

Bayan Kamar awa 5 zuwa 8 seh ki duba ki gani ko yayi kauri,idan beh Yi ba seh ki barshi ya Kara wasu awannin,saboda wani lokacin ya danganta da yanayi idan akwai zafi zeh yi da wuri idan kuma akwai sanyi zeh dauki Dan lokaci kafin yayi kauri.seh ki saka sikari ki juya idan kina bukata seh ki saka a fridge don ya kara kauri.Amma kafin ki zuba sikari seh ki dibi Kamar Rabin kofi ki aje idan Zaki sake yi kin sami starter kenan shi Zaki zuba a ciki.

Yoghurtmatakin girki3 hoto

Yoghurtmatakin  girki3 hoto
Yoghurtmatakin  girki3 hoto