JARIMI DAGA JIGAWA.

Takaitaccen tarihin Nassir Isma'il, Jarimin Nollywood da Kanywood.

Yana da kyau duk inda mutum ya hango wani mutum daga Kasar sa ko Jihar sa ko Karamar Hukumar sa ko Garin Sa ko Unguwar sa yana wani abin a yaba masa to ya zama mai alfahari da wannan mutumin ko Domin ya kara masa karfin Gwuiwa.

A duniyar yanzu Kowa yana son yaga Jihar sa ta samu wani fitacce kuma sanannan Mutum a Nigeria Domin kamar yana kara daga Darajar Jihar ne shi yasa idan mutum ya zama Jarimi sai kaji kowacce Jiha tana cewa nata ne.

Musali Dauda Kahutu Rarara Kanawa suna cewa Nasu ne Katsinawa suna cewa nasu ne. Ali Nuhu Kanawa suna cewa nasu ne Gombawa suna cewa nasu ne.

Yau Daga Jihar Jigawa muna da Jarimi Wanda take aiki da daukacin Ma'aikatun Finafinan da suka fi suna a Nigeria baki daya Jigawa ma'ana Kanywood da kuma Nollywood.

Wannan mutum fitacce ne Wanda kowa ya sanshi saidai ba kowa ne yasan shi Dan Asalin Jihar Jigawa bane Dan Boko ne cikakke Domin kuwa yayi.

ND in Tourism a shekara ta 1993 sai kuma HND a Tourism a 1996 duk KADPOLY.

Sannan yayi PGD in International Relations and Diplomacy a shekara ta 2003 shima a KADPOLY.

Hakazalika yayi PGD in Journalism a shekara ta 2013 a International Institute of Journalism.

Yayi aikin Bautar Kasa ( NYSC ) a Jihar Kwara. 1996/1997. Wanda saboda jajircewar sa akan aikin sa saida ya samu Lambar Yabo da girmamawa ta ( State Certificate of Honour and Automatic Employment)

AIKIN SA.

Yana aiki da.

National center For Women's Development, Central Business District Abuja.

Ya rike mukamai Kalakala a wannan ma'aikatar sannan ya kawo musu cigaba sosai wannan Hukumar tana Alfahari da shi musamman da yake mutum ne mai tsayawa akan aikin sa kuma yana yin aikin komai tsananin sa komai wahalar sa yana da Naci da basira kwarai da gaske. Saboda kwarewar aikin sa saida ya kai matsayin Shugaban Yada labarai da tsarere tsakanin Alumma da Hukumar wato ( Director Press Protocol and Public Relations Unit )

NATIONAL ASSEMBLY.

Yayi aiki da Majalissar tarayyar Nigeria daga 2015 zuwa 2019 matsayin Legislative Aide na Dan Majalissar Tarayya mai wakliltar Kananun Hukumomin Ringim da Taura Hon. Muhammad Gausu Boyi. Yayi ayyukan sa yadda ya kamata mutane sun ji. Dadin Hulda da shi sosai.

Wani aikin na Musamman.

Yakan Gabatar da wasu Shirye-Shirye a Gidajen Talabilin na NTA da kuma Channel 5 duk a Abuja.

Ya shafe sama da Shekaru Goma yana harkar Films kama daga Arewacin Nigeria zuwa Kudancin Nigeria.

Sunan sa Ibrahim Nassir Isma'il. An haife shi 20 ga watan Nuwamba 1968 a Garin Ringim na Karamar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa abar Alfaharin mu.

Shine kuma yake amsa sunan Alh. Saminu Baba a Cikin Shirin Kwana Cassa'in na Gidan Talabijin Din Arewa24.

Ga kadan daga cikin Finafinan da daya taka rawa.

1-Muqabala TV series

2-Kala kala TV series

3-Imaan English TV series

4-Sons of the caliphate

5-Zero hour

6- 4 th republic

7- Boycott

8- If iam president

9- Alqibla

10- Kasata

11- Wata fansa

12- Hauwa kulu Fullo

13- Kwana casain

Dasauran su.

Mutum ne mai son Bincike akan lamuran da suka shafi rayuwar Dan Adam.

Mallam Ibrahim Nassir Ismail Jigawa Muna Alfahari da kai da Nasan kaima duk inda kake Jihar Jigawa tana zuciyar ka.

Danzomo. 12/sep/2020.