AIKIN HISBARSA  WANDA YA QUNSHI UMARNINSA GA AL’UMMARSA

Hadisi ya tabbata daga Abū Sa’īdul Khudrī  ya ce: na ji Manzon Allah  ya ce:

((مَنْ رَأَى مِنْكُمْ مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الإيمَانِ)). Ma’ana: Wanda ya ga wani mummunan aiki a cikin ku, to, ya kawar da shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to, ya kawar da shi da harshensa, idan ba zai iya ba, to, ya qi abin a zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani . Haka kuma wani hadisin ya tabbata daga Ubadatu Ibn as-Samit  ya ce:

((بَايَعْنَا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى السَّمْعِ وَالطَّاعَةِ، فِي عُسْرِنَا وَيُسْرِنَا، وَمَنْشَطِنَا وَمَكَارِهِنَا، وَعَلَى أَنْ لاَ نُنَازِعَ الأَمْرَ أَهْلَهُ، وَعَلَى أَنْ نَقُولَ بِالْعَدْلِ أَيْنَ كُنَّا، لاَ نَخَافُ فِي اللَّهِ لَوْمَةَ لاَئِمٍ)). Ma’ana: Mun yi mubaya’a ga Manzon Allah  a kan ji da bi cikin quncinmu da yalwarmu da abin da ya yi mana daxi da wanda bai yi mana ba, kuma kada mu ja da shugabanni a kan mulkinsu, kuma mu faxi gaskiya a duk inda muke, ba tare da jin tsoron zargin mai zargi ba . Haka kuma Manzon Allah  yana buga misali don faxakar da al’ummarsa game da haxarin qin yin umarni da kyakkyawa ko hani daga mummuna, kamar yadda ya buga misali a cikin hadisin da ya tabbata daga Nu’umān Ibn Bashīr رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا ya ce: Manzon Allah  ya ce:

((مَثَلُ الْقَائِمِ عَلَى حُدُودِ اللَّهِ وَالْوَاقِعِ فِيهَا، كَمَثَلِ قَوْمٍ اسْتَهَمُوا عَلَى سَفِينَةٍ، فَأَصَابَ بَعْضُهُمْ أَعْلاَهَا، وَبَعْضُهُمْ أَسْفَلَهَا، فَكَانَ الَّذِينَ فِي أَسْفَلِهَا إِذَا اسْتَقَوْا مِنَ الْمَاءِ مَرُّوا عَلَى مَنْ فَوْقَهُمْ، فَقَالُوا : لَوْ أَنَّا خَرَقْنَا فِي نَصِيبِنَا خَرْقًا، وَلَمْ نُؤْذِ مَنْ فَوْقَنَا، فَإِنْ يَتْرُكُوهُمْ وَمَا أَرَادُوا، هَلَكُوا جَمِيعًا، وَإِنْ أَخَذُوا عَلَى أَيْدِيهِمْ نَجَوْا وَنَجَوْا جَمِيعًا)). Ma’ana: Misalin wanda yake tsaye kan iyakokin Ubangiji da wanda yake qetare su, kamar misalin wasu mutane ne da suka yi quri’a wajen hawa jirgin ruwa, sai wasu suka sami sama, wasu kuma suka sami qasa. Sai ya zamana na qasan ba sa samun ruwa, har sai sun hau sama, sai suka ce: ina ma mu huda (jirgin) ta vangarenmu tun da mu a qasa muke, ba sai mun hau sama mun cutar da su ba. A nan sai Manzon Allah  ya ce: idan na saman nan suka bari na qasan nan suka huda jirgin, to, baki xayansu za su halaka, amma idan suka yi riqo da hannunsu (ma’ana suka hana su), to, sai su kuvuta kuma su kuvuta baki xaya . Haka kuma Manzon Allah  ya kan yi bayanin narkon azaba ga waxanda suke qin yin umarni da kyakkyawan aiki kamar yadda ya tabbata a cikin hadisin da Uwar muminai Zaīnab Bint Jahsh رضى الله عنها ta ruwaito cewa:

((أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَخَلَ عَلَيْهَا فَزِعًا، يَقُولُ : لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَيْلٌ لِلْعَرَبِ مِنْ شَرٍّ قَدِ اقْتَرَبَ، فُتِحَ الْيَوْمَ مِنْ رَدْمِ يَأْجُوجَ وَمأْجُوجَ مِثْلُ هَذَا، وَحَلَّقَ بِإِصْبَعِهِ وَبِالَّتِي تَلِيهَا، فَقَالَتْ زَيْنَبُ : فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ: أَنَهْلِكُ وَفِينَا الصَّالِحُونَ؟ قَالَ : نَعَمْ إِذَا كَثُرَ الْخَبَثُ)). Ma’ana: Haqiqa wata rana Manzon Allah  ya shigo mini hankalinsa a tashe yana cewa: Lā’ilaha Illallah! Azaba ta tabbata ga Larabawa dangane da wani sharri da ya kusanto! A yau an buxe toshewar/ginewar Yajuju da Majuju kamar haka, sai ya yi zobe da ‘yan yatsunsa (ya haxa babban yatsa da manuniya). Sai Nana Zaīnab رضى الله عنها ta ce: Ya Manzon Allah  yanzu a halakar da mu bayan a cikin mu akwai salihai? Sai Manzon Allah  ya ce: Na’am! Matuqar varna ta yawaita .