Hawan Sallah Sallah_Durba_2014

Wani biki ne da ake yi a kasar Hausa. Ana yin shi ne sau biyu a shekara; Bayan an kammala Azumin watan Ramadana watau 1 ga watan Shawwal, sai kuma bayan masu aikin Hajji sun yi Arafat watau 10 ga watan Zul hajji. Ana kiran Sallah bayan kammala Azumi da suna karamar Sallah, ita kuma dayar wadda ake bikinta bayan saukar mahajjata daga Arafat ita ake kira da Babbar Sallah.