Assalafytsafez
Idan kana so kaga munafukai a fili ba a boye ba toh ka kalli BBC Hausa, idan kana son ganin masharranta a zahiri ka kalli BBC Hausa, a yanzu sharrin su yana bayyana ne akan 'bangarori biyar:👇
1. 'Kasar Nijar 2. Kasar Saudi Arabia 3. Nigeria 4. Shugaban Nigeria Buhari da 5. Malaman Musulunci.
Mutanen kasar Nijar sun dade suna jin zafin abinda BBC Hausa suke musu, BBC suna kaskantar da kasar Nijar fiye da kowa a duniyar nan, BBC sune suka saka ma duniya kallon kasar Nijar a matsayin kaskantanciyar kasa.
.
Ba zaka taba ganin BBC sun kawo labari ko hoton cigaban kasar Nijar ba, idan kaga BBC sunyi magana akan kasar Nijar toh matsala ne kawai, BBC sukan je su dauko hoton kauyuka da wurare marasa kyau suna sakawa a matsayin kasar Nijar, hakan yasa mutane da yawa suke ganin kasar Nijar kauye ko wurin da babu komai na cigaban rayuwa.
Sharrin BBC ne kawai, shin Nijar babu wurare masu kyau masu ban sha'awa ne? akwai.
Toh me yasa BBC suke kaskantar da Nijar, akwai kasashen da sun fi Nijar talauci, amma BBC basa musu haka.
BBC sunce rahotannin su a kasashe uku ne da Hausawa suka fi yawa, Nigeria, Nijar da Ghana, amma BBC za tayi rahoto 10 da kyar ka samu biyu na Nijar, duk Nigeria ne, idan kaji na Nijar ma toh wani mummunan abu zaka ji sun dauko.
.
2. Kasar Saudi Arabia, idan kaga BBC tayi magana akan kasar Saudiyya toh zaka ga wani abu ne da zai jawo zagi ma Saudiyyar a wurin Musulmi.
Da wahala kaga BBC sun kawo wani report na cigaba ko walwalar mutanen kasar, ba zaka ga BBC ta kawo rahotan karfin arzikin Saudiyya ba, ko karfin Sojin ta.
Idan kaji report akan Saudiyya zaka ji maganar Ball ne, kwallo, ko maganar mata su tuka mota, ko an bude gidan rawa, ko maganar rage sautin Lasifikan kiran Sallah a fadin kasar.
.
Duk Musulmi kuma idan yaji ance Saudiyya tayi wadannan sai yaji ransa ya baci, sai yaji ya tsani kasar da shugabannin ta, BBC ba zasu taba kawo maka dalilin da yasa aka kai ga wannan matsayar ba.
Idan kaga BBC sun kawo wani report na cigaba a Saudiyya toh labari ne da babu yadda aka iya dole duniya sai taji, dan haka zasu kawo domin su rike matsayin su na a wurin su aka fara ji, ba dan suna son rubuta wannan report din ba.
.
3. Nigeria:
Da wahala kaga BBC sun kawo labarin dake nuna cewa Nigeria tana da future mai kyau nan gaba, ba zaka ga BBC sun kawo labarin cigaban da kasar ta samu a wasu wurare ba, kullum matsala kawai suke fadi game da Nigeriya.
Idan kaga sun fadi wani abu na cigaba toh abu ne da babu makawa duniya sai taji koda ba ta sanadin BBC ba, so zasu kawo domin su rike matsayin su na a wurin su aka fara ji.
BBC suna gaggawa su kawo report din kidnapping.
.
Suna 'barin jiki su kawo maganar talakan Nigeria yana cikin wahala, amma basu iya tattaunawa da masu mulkin domin jin kokarin da suke yi.
Idan kaga report din BBC guda goma akan Nigeria, toh ka duba zaka guda 8 ko 9 na matsala ne ko tashin hankali.
.
4. Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari:
Kiyayyar BBC ta bayyana karara ga shugaba Buhari, wannan a fili zaka gani, kuma wasu wawayen Hausawan dake aiki a wurin ne suke rura wutar kiyayyar, BBC har shiri suka kirkiro na habaici ma shugaba Buhari, wanda da yawa mutane basu Sani ba, shine rubutun da zaka ga suna yi a Facebook ko Twitter na karin magana, suna cewa karasa mana wannan karin maganar...... 'Karshen Alewa.......
Ko kuma "Bakin Rijiya ba wurin.......".
Duk saboda Buhari suke wadannan maganganu, abu ne a fili da yawa mutane sun san haka.
.
Kai hatta sunan sa basa iya rubutawa sosai da (shugaba Buhari) sai kaga sun rubuta Buhari yace ....... 'dan girmamawan nan na shugabanci ma babu.
Amma shugaban Amurka zaka ga sun rubuta shugaba Biden, ko shugaban Nijar, shugaba Bazoum.
Ko kaga sun kawo hoton Obasanjo, Yar Adua da Jonathan suce wane shugaba ne yafi tausayin talakawa?
Target din su Buhari ne, burin su suga ana ta comments ana zagin sa, ana fifita arna akan sa.
Wannan abu ne da kowa yake gani.
.
5. Hada fada tsakanin Malaman Musulunci:
Kullum suna son gwara kan Malamai, da hada fada da tayar da gaba acikin Musulmi, misali:
A lokacin Bikin Maulidi da 'yan Dariqa suke yi, sai BBC suje suyi hira da wani Malamin Salafiyyah ko na Izala, suce shin menene fahimtar ka akan Maulidi, ko kuma shin yana da asali?
Ba za suyi wannan ba sai daf da lokacin Maulidin, dan haka dai kaga ana ta zage zage tsakanin Musulmi.
.
Ko kuma wani abu ya faru a kasar Saudiyya, sai BBC suje su tambayi Malamin da bai taba zuwa karatu Saudiyyar ba, Kuma wanda Aqidar sa daban data Saudiyyar.
Misali, a 2020 akwai abinda ya faru a Saudiyya, sai BBC suka je suka tambayi Malam Ibrahim Makari akai, wanda bai taba karatu a kasar ba, bai san ta sosai ba, da ya bayar da amsa sai tasha bamban da abinda yake a asali.
.
Hakan sai ya tayar da rikici tsakanin Malaman Sunnah da Malam Ibrahim Makari..
Da gangan BBC suka tsallake Malamai irin su Dr. Sani Rijiyar Lemu, wanda a kasar Saudiyyar ma aka haife shi, acan yayi rayuwar karatun sa.
Da gangan suka tsallake Malamai irin su Dr. Abubakar Birnin Kudu, da Prof. Mansur Sokoto, Dr. Mansur Isah Yelwa Bauchi, da Dr. Bashir Umar Aliyu.
.
Abinda BBC suka yi a nan ba wai rashin sanin aikin jarida bane, No, makarkashiya ce domin tayar da kiyayya acikin Musulmi.
Kuma suna yin haka hatta a bangaren kasuwanci da siyasa da sauran su, domin tunzura jama'a.
Dan haka mutane su fada sosai da BBC, azzalumai ne, masharranta ne na karshe, Allah ya karya su gaba daya.
Za mu cigaba da bayyana sharrin su da gazawar su, kamar yadda suke bayyana gazawar wasu.