Toto Millionaire
Toto Millionaire fim ne na barkwanci da aka shirya shi a shekarar 2007 na Kenya wanda Simiyu Barasa ya rubuta kuma ya ba da umarni.[1] Fim ɗin ya fito da Mungai Mbaya ɗan shekara 10 a matsayin jagora wanda ke taka rawar Toto. Fim ɗin Toto Millionaire labari ne mai sauƙi na wani yaro yana fuskantar matsaloli a rayuwa tare da uwarsa mara lafiya. Amma yaron bai iya barin yanayi ya hana shi samun damar rayuwa ba.[2] An kaddamar da fim ɗin a ɗakin taro na Goethe Institute a Nairobi a ranar 13 ga watan Nuwamba 2007.[3]
Toto Millionaire | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2007 |
Asalin harshe | Turanci |
Ƙasar asali | Kenya |
Characteristics | |
'Yan wasa
gyara sashe- Mungai Mbaya a matsayin Toto
- Joseph Kinuthia a matsayin Barry G
- Ainea Ojiambo a matsayin Supa
Takaitaccen bayani
gyara sasheToto ya yi tuntuɓe a saman kwalbar da ke ɗauke da kyautar da ta kai miliyan a cikin cacar abin sha mai laushi. Idan ya je karɓar kyautarsa, yakan fuskanci cikas daga masu kokarin sace masa kyautar saboda shekarunsa. Amma yaron ya sami nasarar shawo kan kalubalen da yake fuskanta kuma ya karbi ladansa.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kenya: No Surprises As 'Toto Millionaire' Hits Screens". Allafrica.com. Retrieved 2021-11-28.
- ↑ "Africiné - No surprises as 'Toto Millionaire' hits screens". Africine.org (in Faransanci). Retrieved 2021-11-18.
- ↑ 3.0 3.1 "Toto Millionaire' now ready for release". Nation.co.ke (in Turanci). Retrieved 2019-11-29.[permanent dead link]