Littafin Things Fall Apart
Things Fall Apart shine littafin na farko da marubucin nan dan kasar Najeriya Chinua Achebe ya wallafa, wanda aka fara bugawa a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da takwas 1958. Ya kwatanta rayuwar kafin mulkin mallaka a yankin kudu maso gabashin Najeriya da kuma mamayar da Turawa suka yi a karshen karni na 19 . Ana kallonsa a matsayin babban littafin tarihin Afirka na zamani a cikin Ingilishi, kuma ɗaya daga cikin na farko da ya sami yabo mai mahimmanci a duniya. Littafi ne mai mahimmanci a makarantu a duk faɗin Afirka kuma ana karantu d a karantar dashi sosai a cikin ƙasashen Afrika dama nahiyar Turawa. William Heinemann Ltd ne ya fara buga littafin a Burtaniya a cikin shekara ta alif ɗari tara da sittin da biyu 1962, kuma ya zama aikin farko da aka buga a cikin jerin Marubuta na Afirka na Heinemann.[1] Things Fall apart yayi bayanin rayuwar wani dan kabilar Igbo mai suna OkonkwoJarumi kuma zakaran kokawa a Umoafia. Littafin ya kasu kashi uku, inda na farko ya bayyana iyalinsa, da tarihinsa, da al’adu da zamantakewar kabilar Ibo, sai kuma kashi na biyu da na uku ya gabatar da tasirin Turawan mulkin mallaka da da masu da'awar yada addinin Kiristanci. okonkwo, danginsa, da sauran al'umma. [2] Chinua Achebe ya nemi gyara barnar da nahiyar Afirka da al'ummarta suka yi a sakamakon mulkin mallaka na Turawa.yayi bayani a cikin littafin 'Things Fall Apart’ ɗaya daga cikin litattafan Afirka na farko da aka rubuta da Turanci don samun karɓuwa a ƙasa.