Thin Ice (fim na 2013)
Thin Ice fim ne na gaskiya na 2013, yana bin masanin ilimin ƙasa Simon Lamb akan bincike don fahimtar kimiyyar dake bayan canjin yanayi. Ana samun hakan ne ta hanyar zagaya duniya, da saduwa da masana kimiyya daban-daban,tun daga masana kimiyyar halittu zuwa masana kimiyyar lissafi, waɗanda ke binciken yanayin. Ƙarshen fim ɗin ya jaddada haɗin kan kimiyya game da sauyin yanayi da ɗan adam ya haifar.
Thin Ice (fim na 2013) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2013 |
Characteristics | |
Genre (en) | documentary film |
Launi | color (en) |
thiniceclimate.org |
Fim ɗin wani shirine na haɗin gwiwa tsakanin Jami'ar Oxford da Jami'ar Victoria ta Wellington, kuma an fara shi a duniya a Ranar Duniya 2012, da kuma a New Zealand a 2015.
Manazarta
gyara sasheHanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Gidan yanar gizon hukuma na Thin Ice, daga inda za a iya kallon fim din da kuma sayen DVD.
- Tirela na hukuma