Theresa Obumneme Okoli ita ce ta 4 a matsayin shugabar kwalejin Ilimi ta Tarayya (Fasaha), Umunze. A ranar 17 ga watan Mayu a shekara ta, 2018, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada ta don maye gurbin mai rikon mukamin shugaban kwalejin, Dr. Cicilia Nonye Ibekwe.

Tessy Okoli
Rayuwa
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
Sana'a
Sana'a Malami

Rayuwa da ilimi gyara sashe

Tessy an haife ta ne daga gidan Aniagboso a kauyen Okpuifite, Agulu, karamar hukumar Anaocha, jihar Anambra. Ta fara karatun ta ne a makarantar firamare ta St. Augustine, da ke jihar Ogun sannan ta ci gaba a makarantar sakandare ta mata, da ke Awgbu, ta jihar Anambara, daga shekarar, 1971zuwa1984, inda ta samu takardar shedar kammala makarantar sakandaren Afirka ta Yamma (WASSCE). Ta riga ta wuce Kwalejin Ilimi ta Jihar Anambra (a yanzu, Kwalejin Ilimi ta Nwafor Orizu, Nsugbe, Jihar Anambra), inda ta kasance mafi kyawun ɗalibin da ya kammala karatu daga Sashen Noma. Ilimi a shekarar, 1988. Ta samu digirin ta na B.sc a fannin aikin gona. Ilimi a shekarar, 1990 daga Jami'ar Nijeriya, Nsukka da kuma digiri na biyu a shekarar, 1995 daga wannan jami'ar. A shekarar, 2011, ta samu digirin digirgir a jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Enugu

Manazarta gyara sashe

https://www.fcetumunze.edu.ng/news/fg-appoints-colleges-first-internal-provost Archived 2019-10-19 at the Wayback Machine

https://www.sunnewsonline.com/day-umunze-college-celebrated-first-internal-provost