Terrence Mashego
Terrence Mashego (an haife shi a ranar 23 ga watan Yuni 1998) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Afirka ta Kudu wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kulob ɗin Cape Town City na Afirka ta Kudu da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu.
Terrence Mashego | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Mamelodi (en) , 23 ga Yuni, 1998 (26 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa | Afirka ta kudu | ||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||
Makaranta | Jami'ar Fasaha ta Tshwane | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Aikin kulob/Ƙungiya
gyara sasheAn haifi Mashego a Mamelodi, Gauteng.[1] Ya shiga ƙungiyar matasa ta Arcadia Shepherds a cikin 2006.[2] [3] Mashego ya halarci makarantar sakandare ta Bona Lesedi, inda ya kammala karatunsa a shekarar 2014.[4] [3] Ya halarci Jami'ar Fasaha ta Tshwane ta hanyar karatun wasanni daga 2016, yana hada karatu tare da yin wasa da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta su amma ya barta bayan watanni 8 kuma ya sanya hannu a ƙungiyar National First Division Mthatha Bucks. [3] Ya yi bayyana sau ɗaya a Bucks a cikin lokacin 2016–17 da bayyana 10 a cikin lokacin 2017–18.
Mashego ya shiga sabuwar kungiya ta National First Division TS Galaxy a shekarar 2018. Ya lashe Kofin Nedbank na 2018–19 tare da Galaxy bayan kulob din ya doke Kaizer Chiefs a watan Mayu 2019.[5]
A watan Oktoban 2020, Mashego ya rattaba hannu a kulob din Cape Town City na Afirka ta Kudu.[6]
Ayyukan kasa
gyara sasheMashego ya samu kiransa na farko zuwa tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu domin buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da kasar Habasha a watan Oktoban 2021.[7] Ya buga wasansa na farko a Afirka ta Kudu a wasan da suka doke Habasha da ci 3-1 a ranar 9 ga watan Oktoba.
Girmamawa
gyara sasheTS Galaxy
- Kofin Nedbank : 2018-19[8]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Sibanyoni, Buleyeni (16 October 2021). "Terrence Mashego inspirational rise to the top". New Frame. Retrieved 9 April 2022.
- ↑ "Terrence Mashego: Summary". Soccerway. Perform Group. Retrieved 9 April 2022.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namednew frame
- ↑ Sibanyoni, Buleyeni (16 October 2021). "Terrence Mashego inspirational rise to the top". New Frame. Retrieved 9 April 2022.
- ↑ Mothowagae, Daniel (19 May 2019). "Galaxybshock Amakhosi in Nedbank Cup final". City Press. Retrieved 12 October 2021.
- ↑ Ditlhobolo, Austin (9 October 2020). Terrence Mashego: Cape Town City confirm signing of TS Galaxy defender". Goal. Retrieved 9 April 2022.
- ↑ "Eric Tinkler hails 'dedicated' Terrence Mashego after first Bafana Bafana call-up". sport24. 28 September 2021. Retrieved 9 April 2022.
- ↑ Ratsie, Ofentse (12 October 2021). Terrence Mashego living his dream in the Bafana camp: 'This is a big moment for me' The Sowetan. Retrieved 9 April 2022.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Terrence Mashego at WorldFootball.net